← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 143

Sashe 17

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Momy muna neman mai aiki wacce zata rika gyara mana gida”

Ya fada yana aunar jalof din taliya da Momy ta zuba masa.

“Yar talakawa za'a nemo maka kenan, kaga ko dan za a ci amfaninta”

“Za tai ci amfaninmu ai biyanta za a yi”

Momy ta yi murmushi.

“Dan wajen Fulani har yanzu ka ki yarda da cewar za ka ci ribar talaka ko?”

“Momy kece ai kin ji ki gane, idan ba wani abu zaka saka talaka ba ka biya shi me zai hada ka da shi, Mama Fulani tana yawan yi min bitar kar na yarda ko rigata talaka ya rika balle kuma har ta kai ga alaka, kin san talaka dan hassada ne”

“Lallai kuwa, ina jiye maka tsoron ranar da zaka fara kaunar talaka, wata kila abun ba zai zo maka da sauki ba”

“Kamar ya?”

“Ba a son fariya, Allah zai iya jarrabarka ya koma talakan cikin talakawa, ko kuma Allah ya jarrabe ka da son yar talakawa wacce zaka duka har kasa kana rokon ta so ka?”

Ya tofar da ragowar abincin da ke bakinsa.

“Allah ya tsare ni Momy, ni ai bana da ra'ayin mace fiye da daya, Rahma ce kawai bayan ita babu wata”

“Wallahi yayan talakawan nan akwai tarbiya, da ace Rahma yar talakawa ce da zata fi ganin girma da girmanka fiye da yanzun”

“Ko a yanzu tana ganin girman ki Momy, kawai dai ita ta tashi a rayuwar turai ne, kuma kin san irin Rahma bata tashi gidan wahala ba shiyasa....”

“Hmmm To Allah ya kyauta”

Shine abunda Momy ta fada daga karshe sannan ta tashi daga dinning din ta nufi kitchen. Sai bayan sallah magariba ya biya gidan family house dinsu Rahma ya dauko matarsa suka dawo gida. Kamar wata marar lafiya haka ta shigo cikin falon tana takawa kamar mai jin wahalar tafiyar.

“Wani abun ne Dear?”

“Aa Daddy be dawo ba, kuma ance yai hasara kudi da yawa a shopping mall dinsa daya kone”

“Shine kuma za ki dauki damuwar ki saka a ranki? Bayan kin san lalurarki?”

Tai murmushi tana kai hannayenta ta zagaye wuyansa.

“Ina kokarin kawarda damuwar fa ko dan saboda na rayu da kai”

Kissing din lips dinta yai sai kuma ya rumgume ta a kirjinsa.

“Ka yi Momy maganar mai aikin? Ni wallahi har kyamar shigowa dakin nan na ke, duk datti”

Yai shiru be ce da ita komai ba.

“Bathrooms din mu duka suna son gyara fa, ga tarin wanke-wanke, ga kitchen din mu and bedrooms duka datti, ko mopping an dade ba ayi ba, kuma kasan ba zan iya ba”

“Shiiiiiiiii”

Ya fada yana shafa bayanta, yasanta da  yawan magana wani lokacin kamar radio, ga shi kuma baya son yawan magana sai idan da Mama Fulani ne ko Momy.

“Doc Asim zai rika zuwa yana duba ki kullum”

Ya fada bayan ya saketa, sannan na nufi upstairs.

ATAA POV.

Mun taki sa'a domin kuwa mun isa cikin asibitin a lokacin da yake tsaka da aiki, ina gaba polisawan ba bayana kowa sai kallon mu yake har muka isa ofishinsa, da muka shiga sai muka tarar baya ciki wai yana dakin tiyata, a ofishin mukai tsaye cirkocirko muna jiransa har ya fito daga dakin tiyatar ya shigo ofishin, da fari tsayawa yai yana kallon polisawan kamin ya maida dubansa a zuwa gareni, da alama an labarta masa zuwan mu tun kan ya shigo ofishin.

“Kai ne Doc Asim?”

Daya daga cikin yan sanda ya fada sai ya gyada masa kai.

“Yes wani abun ne?”

“You're Under arrest”

“Akan me?”

Ya tambaya kamar da gadara, ni kuma nai karfin halin bude bakina na ce.

“Kai ka cirewa Mahaifiyata koda dan haka dole a kama ka kuma a kwato mata hakkinta”

“Kodar da kika siyar? Blackmailing dina za ki yi? Are you out of your sense?”

Mamakin furucinsa ya hanani ko da motsin kirki balle har na sake cewa wani abu, waina siyar da koda, yaushe na siyar? Wa na siyarwa ya ma za ayi na siyar da kodar mahaifiyata.

“Oficer kar yarinyar tai wasa da hankalinku ta raina muku aiki, kar kuma ku isko ni har cikin ofishin ku ce za ku ci min mutumci akan aikin, muje station din ku hada da dan sanda ku daya zan saka shi motata sai mu tafi station din amman ni ba zan shiga motar ku ba”

Yadda ya bukata haka akai, ni da sauran polisawan muka koma a motar da muka zo, shi kuma ya shiga motarsa da dayan dan sanda bayan ya dauki wasu takardu.
A motar yan sanda sukai ta tambaya wai da gaskiya na siyar da kodar nai ta musu rantsuwar ban siyar ba, ban ma ya cire ba, idan har na siyar mi zai sa na kawo kararsa gurinsu, a nan suka min tausayawa kuma suka ce za su kwatar min hakkina, dan sanda yana ya matse ni sosai jikinsa na ta gogar nawa.

“Yarinya kyakkyawa da ita za a ci amanarta, ki sha kuruminki sai mun kwato miki hakki”

Shine abunda ya fada yana kallona da jajayen kamar dan shaye-shaye. A lokacin da muka isa Station din sai muka shiga ciki, a nan ya fiddo da wasu takardu ciki har da takardar da na sakawa hannu lokacin da za ayi ma Nana tiyata.

“Kin san kin saka hannu a wannan takardar ko ba ki sani ba?”

“Na saka”

Na amsa masa ina kallon takardar.

“Magani kawai na dubu nawa kika siya mata? Abincin da kike ci safe da rana da dare daga Hotel ake kawo miki duk ina kika samu kudin?”

Kasa magana nai sai hawaye na ke gaba daya ya gama dauren kafafu kai har ma da jikin gaba daya. Sai kuma ya juya gurin polisawan ya ce.

“Yi ma Babban likita irina sheri abu ne mai sauki domin ta samu kudi, yarinyar nan ina zaman ta dauko mahaifiyarta ta kawo wai maciji ya tsareta, kuma babu yadda zata yi ita bata da gabas bata da yamma, na ce ni ba zan taba ba, sai an kawo kudi, sai kawai ta ji ina magana da wani mai neman koda a nan tace zata siyar kuma babu yadda ban yi da ita ba akan ta nemo manyanta sai tace daga ita sai mahaifiyarta suke wai basu da kowa a nan, kuma idan ban taimaka na siye kodar mahaifiyarta ba, babu inda zata samo kudin da za ayi mata allurar dafin macijin, a haka tai convince dina na yarda na bata takarda ta saka hannu, na bata kudinta ta ce aa na aje gurina na siya mata magani ragowar canjin na bata wannan ne kawai abunda na sani”

Cikin kuka na nuna shi da yatsa na ce .

“Allah ya isa, karshenka ba zai yi kyau ba, kuma za ka ga abunda zai same ka?”

“Kaji ko? Oficer nima bude min file sai na ji akan me take kokarin bata min suna”

Ya fada yana nuna ni. A maimakon polisawan suyi wani abu sai na ga kamar suna tsoronsa, ashe ya siye dayan sandan daya shiga motarsa, sai kawai na ga sun fita waje har da shi Doc Asim din sun kebe suna ta magana da juna, suna kawowa sai suka fara tuhumata wai waya biyani na bata masa suna.

“Babu wanda ya saka ni, amman wallahi karya ya fada”

“Kina da wata shaida ne? ”

“Ba ni da ita, amman Allah shine shaidata”

“Aikin banza, haka kawai za ki nemi batawa mutum aiki da suna?”

“Wallahi ba bata masa nai ba, gaskiya na fada”

“Wannan duk shairin makiya ne, so kawai take ta bata min suna, dan haka su saka ta a cell sai ta fada muku wanda ya saka ta yin wannan sherin”

Cewar Doc Asim cike da gadara. Ni ko ina jin haka sai tsoro ya kamani take na saka kuka, ni ce da gaskiyata amman na risina har kasa ina rokon Doc Asim yafiya, sai ya fisge kafarsa ya daka min hannu har sai da dan yatsana ya fashe saboda zafin takalmin kafarsa. Haka suka rika ni saboda tsabar zalince suka saka ni a cell din mata ina ta kuka kamar raina zai fita.
  Daga cikin matan da ke cell din ta daka min tsawa wai na yi musu shiru na cika musu kunne da hayaniya, a haka nai shiru na samu guri na rabe a cikin dakin mai cike da sauro da duhu sai wari yake.
   Ba a bari ka fito ko da sallah za kai, fitsari ma sai dai kai a cikin cell din gaban kowa da kowa. Dukan tunani sai ya karkarta gurin Nana ban san halin da take ciki ba, ban san iya tsawon lokacin da zan dauka a nan ba.
Da dare yai sai naga ana fita da mata masu kyau, can da asuba kuma aka kawo su, ni dai ina zaune jigum har safe ban saka komai a bakina ba, sai can da azahar wani dan sanda ya bude min yace na fito a nan na samu damar yin alwala na raba gafen masallacin mazan nai rama sallah da akd bina sannan na gabatar da azahar, a lokacin ne dan sanda ya kawo min abincin shimkafa da miya har da kabeji da nama, kadan na ci saboda cikina ya daure sosai bayan na gama ya bani ruwa mai sanyi na sha.

“Idan an jima da dare zan zo na dauke ki, sai mu fita mu sha iska, idan mun dawo zan yi belinki da safe kin ji”
Chapter 17 · 0% Book details