Sashe 108
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rukaiya ta yi shiru ba dan maganar Mama Fulani ta kwantar mata da hankali ba sai dan babu wani abun da zata iya yi idan ma sun zo ba lallai ne su ce suna son su ba domin wacan zuwan ma ai ba su ce ba. Ita da Maryam wannan rashin manemi ya ishesu sosai suna damuwa da wannan matsalar domin ta nan kawai Allah ya rage su, suna ta iyaye a rayu masu hali ga family ta ko'ina ga ilmi kyau nan ma gwargwado suna da shi amman sun rasa manemi daga ita har yar'uwarta Maryam, ko an fara zuwa sai mutum ba zai dawo ba idan kuma haduwar online ce ma ba za a zo ba.
RAHMA POV.
Tana zaune falon mahaifinta kanta a kasa sai rabon ido take tana sauraren irin amsar da za su bata. Ba Mommy kadai da take mace ba har Daddynta yau haushinta yake ji na abunda ta fada taya suna fafutukar nema mata lafiya suna fushi da Aliyu akan abunda yai mata yanzu zata zo musu da wani zancen wai Aliyu ya kirata ya ce ta dawo dakinta?
“Idan ma da gaske ne, ai shi zai zo ya tafi da ke mana ba wai ya bugo miki waya ba, ke kike wahalar da kanki akansa shi yana can ya yi aure ya manta da ke ma”
Mommy ta fada a hasale.
“Ba kiji irin magiyar da yake min ba Mommy wannan yarinyar ya fada min hada shi Momy tai da ita saboda huce ta kaini yace min yanzu haka baya ma shiga dakinta, har da kukansa yana ta rikona na dawo”
Haka ta tsara karyar ta murje ido kamar gaske.
“Yana son ki dawo shine ba zai zo ya tafi da ke ba sai dai ki kai kanki? Wannan ai zubar da kimarki ne idan ma baki sani ba”
“Wai ba zai zo ba saboda abunda kikai wa mahaifiyarsa tace idan ya zo nan sai ta tsaba masa, auren ma duk itace tai ita da Mama Fulani saboda huce takaici har wani cewa suke wai na shanye shi”
“Ina kika ji?”
“Shi ya fada min jiya da dare a waya mantawa ma nai ban yi recording ba, da kunya har da kukan shi Wallahi”
Mommy ta nuna ta gatsanta.
“Ke tun kamin a haife ni na san wayo, ba zaki koma ba Matukar ba shi ya zo bikinko ki kuma sai mana alkawarin wacan ba zata takura miki ba, dan ba za mu zuba miki ido ki mutu ba, idan ke ba ki son kanki mu da muka haife ki muna son ki”
“Ai Wallahi wacan yarinyar har aiki ce aka kawo min shi ma ai ya fada, yace duk wani aiki na gidan ita zata rika yi, ni hutawa kawai yake son nai”
“To mun ji tashi ki tafi”
Haka ta taso cikin bakinciki rashin amincewa ta koma da iyayenta suka yi, yanzu kam bata san karyar da zata musu ba, sai dai ta kira Aliyu ta rokeshi akan ya yarda ya zo ya dauke ta idan ya ki zata ba shi hakuri ma, ita dai burinta kawai ta ganta a gida daya da Ataa yadda zata jidadij ci amata mutunci kuma kallon da kawayenta suke mata na mijinta yayi aure ya barta su daina shi kowa ya san cewa yar wanke wanke aka auro mata, ta san Aliyu ba zai hana ta ba, domin shi kanshi baya son talaka kuma ta san babu ta yadda zai iya zaman auren da Ataa balle har wata alaka ta hada su, tunanin sharing ma da gai na cewar abunda yake mata zai iya yi ma Ataa yanzu take jin cewar ta yi kuskure saboda Aliyu ba sa'an Ataa ne ba ko da wasa ba zai yarda ta zauna kusa da shi ba ma, a iya tunaninta a yanzu Ataa na can daki dabam shi kuma yana daki dabam, ko cewar da yai wacce zata kula da mijin kawai aka auro tana tunanin ya fada mata haka ne saboda ta ji haushi tunda ta tafi ta barshi. Ai da ta zumudin amarya yake da ba zai kirata ba, sai yanzu take jin bakinciki rashin daukar kiran da ba tai ba, wata kila ma hakuri zai bata kuma ya roki ta dawo dakinta ko kuma ya bukaci ta bashi dama ya zo ya tafi da ita, ta san irin rayuwar da suke da kuma yadda Aliyu yake da kyama da kin kula mata ba zai iya raba zuciyarsa da jikinsa wa mace biyu ba, mace ma kazama yar bara kuma yar aikin gidansa kamar Ataa.
“Hahaha yarinyar za ki ci ubanki ba dai mijina kika aura ba? Kina yar talakanki kika jawa kanki wahala Wallahi sai kin yi kuka da idonki kuma kin gwammace ba a taba halittarki duniya ba”
Ta fada yana shiga dakinta na da wanda ya kasance mallakin Muneera a yanzu, ita da Muneera suke sharing a yanzu.
Gaban madubi ta zauna tana kallon kanta a madubi ta mika hannu ta dauki wayarta ta kira Aliyu, ringing biyu a na uku ya daga sai yai shiru yana jiran tai magana kamar yadda ya saba idan dai kai ka kirashi ba shi ya kiraka ba ko da ma shi ya kiraka idan uzurin naka ne kyalewa zai yi sai ka yi magana da kanka.
“Aliyu”
Ta fada a shagwabe tana tana wani cream dake gaban madubi.
“Ka kira ni jiya”
“Lafiyarki zan tambaya”
“Ka damu da ni kenan? Amman ka auro wata”
“Wata aba kanki take ba, ke ma kuma ba akanta kike ba, idan kina da wata maganar ki fada”
Kasa cewa tai ya zo ya je da ita ko kuma yai hakuri tana son har sai shi da kansa ya bata hakuri ko kuma ya roketa ta dawo da kanta idan ma ba zai iya zuwa din ba.
“Dear kina bukatar wani abun ne?”
“Aliyu ba zaka ba ni hakuri ba? Na zaka ce komai a auren da kai ba?”
“Ina nufin kina bukatar wani abun kamar na ci ko na sha ko wani abun daya shafi lafiyarki?”
Ta ji haushi a take ta kashe wayarta tana buga kafa kasa, ta san halin mijinta da jin kai ai, ba zai bata hakuri ba tun da yana ganin shi ne da gaskiya, amman zata jira har nan da sati daya ko biyu idan ya be ce ta zo ba ko be biyota ba zata share shi, balle ma tasan yana yin hakan ne kawai dan ya bata haushi kamar yadda yake mata idan yana fushi da ita a gida, ta san Aliyu can't live without her shiyasa ya turo mahaifiyarsa ta bata hakuri ta koma wacan karon duk kuwa da ya san yana da gaskiya, yanzu ma saboda abunda Mommynta tai ne da yanzu ya sake aikowa ko kuma ya zo da kansa.
ALIYU POV.
ya sauke wayar, ya amsa wayar a gaban Ataa ne saboda Rahma ta kira shi kamar yadda zai iya amsawa wayar Ataa a gaban Rahma saboda dukansu matansa ne kuma wani uzurin zai iya sakawa wata ta kira, da dai ba daga daga cikinsu ba ne, sai kuma Momy ko Mama Fulani Daddy Abbah, bayansu sai ya ga dama yake daukar waya idan an kira ko da yana waje balle kuma yana tare da iyalansa. Aje wayar yai gefena yana kallon Ataa wacce ke ta motsi kamar bata jin dadin zaman, ta turo baki sai hawaye take a hankali.
“Ba kya jinddin zaman ne?”
“Zafi ni dai har yanzu”
Ya san abunda take nufi sai kawai yai yar dariya, ya mike tsaye ya dauke ta ya nufi dakinsa da ita.
“So kike a kara kenan?”
“Wallahi baka da tausayi kai mugu ne”
Ta fashe da kuka.
“Ni ne mugun?”
Ya tambaya yana cige baki yayinda yake sauke ta saman gadon. Sai ta kara fashewa da kuka shi kuma ya saka mata dariya.
“Kin cika raki, ba da gaske na ke ba, ruwa zan hada miki”
Bandakin ya shiga ya hada mata ruwan zafi, ya fito yana fada mata
“Kullum ki rika yin tsarki da ruwan zafi”
“Wallahi ko wuta na saka ba zai daina ba, ni kaina na san zafin da na ke ji, har ya fi na jiya ma, kuma har yanzu bana iya tafiya daidai”
Ta fada tana wani irin shan iska saboda kukan ya mata yawa.
“Na lura ai ba zan sake ba”
“Har abada?”
Yayi wata mahaukaciyar dariya sannan yaja kunnenta.
“Yes har a bada”
Sannan ya fice daga dakin, falo ya koma ya zauna for a while sannan ya taso ya dawo dakin ya shirya cikin wasu tufafin, sai ga Ataa ta fito daga bandakin tana ta sauri.
“Ka ce zaka kai ni gurin Nana ko yau?”
“Ke fa baki da wyo ya za ayi Amarya da fita yau? Kuma da rana? Da ma da rana ne zan iya kai ki ki ganta sai dai kuma ba a yadda kike ba wannan abun kunya kawai zai sa na ji”
“Zan yi tafiya daidai”
“Ba kya iyawa ai, dole sai kin warke idan kin warke zan kai ki gida ki ga Mama da Momy”
Ya fada yana fesawa jikinsa turare sannan ya juyo ya sumbace ya saka bakinsa cikin nata bayan ya cire ya shafa kumatunta.
“I love you”
ATAA POV.
Da kallo na bi shi har ya fice sannan na zauna bakin gadon ina dan sake jikina ina hawaye, gaba daya satin haka nai shi cikin takura domin daga kafan da yai min na kwana hudu ne kawai, ranar da na cika sati daya ya kai ni da dare na ha Nana ranar ji nai kamar karna dawo gida, daker na shiga motar ina ta kuka yana jin ba dadi.
Muna kama hanyar gida ya mika hannu ya rika hannuna yana ta murzawa a hankali, kamin ya kwanta da ni jikinsa.
“Ashe ba za ki iya zuwa wata kasar ki barta ba? Gashe na shirya nan da kwana uku za mu dawo mu musu bankwana mu wuce”
Ni dai ban ce masa komai ba sai kukan na ke a hankali, da gangan na feshe masa majigina a jikin shaddarsa na yi tunanin ko zai yi magana ne, sai dariyarsa na ji ya shafa kaina.