← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 143

Sashe 118

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka tai ta maimaitawa sai da ya rufe mata baki, sai kuma ta fashe da kuka kuka irin sosai din nan kamar wacce akai wani abu rasa tai me zata yi, ita a rayuwarta bata taba rika waya ba ko karama balle babba irin wannan mai screen kato.
Rikota yai suka baro kitchen din suka dawo falo suka zauna, sai ya karbi wayar ya bude mata ya hada mata.

“Idan na fita ko kuma zan saka Nasir ya siyo miki layi mai kyau na ki na kanki, kuma yanzu sai an saka wayar carji idan ta yi full sai a fara tabawa”

Ta yi saurin tashi daga kan kujerar tare da carjar wayar ta nufi socket ta saka ta zauna s gurin ta tsare wayar. Shi kuka ya tashi ya koma kitchen din ya dauko musu abincin daya siyo musu ya zo kusa da ita ya zauna ya bude abincin.

“Aliyu ka dauko Nana na nuna mata wayata”

“Ba yau ba dai, gobe ai zamu je mu gaisheta sai ki nuna mata”

“Har sai gobe”

Ya gyda mata kai yana deban abincin ya bata a baki, jin tai bata gamsu ba har sai da ta dawo saman jikinsa ta zauna ta rumgume.

“Na gode sosai Allah ya kara arziki ya tsareka daga dukan sheri Allah ya biya maka bukatunka na alheri”

“Nima na gode da ki kai ciki”

Rankwashinta ya ji a kanta ya ji kamin ya ji sautin dariyarta yai murmushi ya kara rumgume ta. Ba wani abun kirki ta ci ba abincin tsabar zumudin waya ya saka ta manta da wani zancen cin abinci duk kuwa da tana jin yunwar. Ranar a gaban wayar ta kwana duk yadda ya so ta dawo ciki daki su kwanta kin tai tana ta jiran har sai wayar ta yi full sannan ta fara tabawa, a dole ya dauko matashin kai ya aje a gurin yai mata matashin kai da hannunsa ya lulluba musu mayafi suka kwana a gurin har safe.

MAMA FULANI POV.

Tun da Abbah ya dawo ya fada mata abunda ya faru kuma ya ce mata Mahaifiyarta Ataa zata zo kuma a nan zata sauka sai ta fasa inda zata saka kanta sabar kunya, dole ne tai mata tarba ta musamman kasancewar yar sarkin Agadaz sai dai taya? Baya ta wulakanta yarta? Ta sani har abada ita da Ataa ba za su taba ganin kimarta ba, yadda za tai ido biyu da ita ma take tunani. Gabanta be kara faduwa ba sai da ta ji tsayawar motar Aliyu da sauri ta tashi ta shige dakinta har da hadawa da gudu.
Saman gado ta haye ya lulluba da blanket tana jin sallamar Aliyu ta fara rawar sanye abunda bata taba ba a rayuwarta.

“Mama ba ki da lafiya ne?”

Ganin shi kadai ya shigo yasa ta tashi zaune cikin yanayin damuwa tana kallonsa ta ce.

“Aliyu ina jin kunyar hada ido da Ataa da mahaifiyarta, ba ni da wannan idon na kallonsu ko na ce zan musu wata magana, waya taba tsammanin haka Aliyu? Ko daman can ka sani?”

Zaunawa yai kusa da ita cike da damuwa da damuwarta domin ita din ma uwarsa ce kuma mai damuwa da abunda ya dame shi.

“Ban sani ba Mama ban ma taba kawo wa a rana cewar wata wana haka zai faru ba, iyakar abunda na rike wata rana dole yan'uwanta za su bayyana, amman ban taba kawowa kaina cewar masu kudi ba”

“Ka huta, Momy ma bata mata komai ba sai ni oh ni Fulani yau na jin kunya na shiga uku, Wallahi ko a mafarki aka fada min cewar wata rana yarinyar zata zama haka ba zan yarda ba, amman ji abunda ya faru? Ina ta zagin yarinyar nan ina ta ci mata mutunci ashe ma har ta fi mu komai”

“Mahaifiyarta tana can falo, Ayusher kuma tace zata tsaya bangaren Ammy”

“Eh ta tsaya can ai tana gaskiya, ni ai muguwa ce na san haka take kallona, ka ji fa rashin rabo jiya na hana yarinyar ruwan sha a gidan nan ashe ashe.... ”

Wannan karon har da kwalla gaba daya duniyar ta rikice mata, domin yadda take son zuri'ar masu hannu da shuni da ace ba tai wa Ataa haka ba da yanzu sai ta kulla abota da Nana, kuma ta sake jikinta da ita amman ina ta bata komai. Tashi Aliyu yai ya fice daga dakin, ya barta ita kadai tana da tufka da warwara, har da dan lekowa ta leki fuskar Nana ta koma cikin dakin, gaba daya kunya take ji kamar wacce tai sata ko. Maryam ce ta shigo cikin dakin sai Mama Fulani ta juyo da sauri ta kalleta.

“Ke kin gaishe ta?”

“Eh na gaishe ta ni da Rukaiyah”

“Ta karba miki?”

“Ta karba mana amman tana ta kallonmu”

“Kunyar sauka na ke ji”

Ta fada gumi na karyo mata.

“Wallahi Mama da kunya wa ya saka ran haka zai faru? Kara ma Ammy bata taba mata komai ba, ita da Ya Muhseen da balle Ya Aliyu da yake mijinta gaba daya”

Mama Fulani ta dora hannu saman kai.

“Kai ni dai kan na shiga uku naga ta kaina, ni yanzu ya zan yi na fita na ganta?”

“Ai ita bata san ki ba, kuma kin san Ataa kila ma bata taba fadar abunda kika mata ba, kuma ai dole ki fita tunda Abbah yasa an kawo ta nan”

Babu yadda Mama Fulani ta iya da abunda ya fi karfin wuta, dole ta kulle kunyarta a baren zane ta fito tana saukowa a hankali.

“Lale lale mara da Hajiya ashe har kin iso da yake ina wanka ban san shigowarki ba”

Ta fada tana dariya da far'a kamar ba ita ba, Nana kan kallonta kawai take har ta zauna saman kujera tana gaisheta kamar zata risina.

“Hajiya Ina wuni? Ya gida ya hanya?”

“Lafiya kalau Alhamdulillah”

Nana ta amsa a hankali ba tare da ta saki fuskarta ba.

“Aa ya ba a kawo mata komai ba? Ke Rukaiyah me kike yi baki kawo mata komai ba”

“An kawo mata ruwa da lemu ta ce a dauke wai ta koshi”

“To ko kin fi son na gida irin wanda ake hadawa wannan?”

“Bana jin kishin ruwa ko yunwa a yanzu, ki ce Fulani?”

Mama Fulani ta ji kamar ta nitse cikin kasa.

“Eh ni ce, ai ni ce na rika Aliyu a hannuna na girma tun yana dan yaye, ai shi mai gidan nan mijina shi da mahaifin Aliyu uwa daya uba daya suke, mijina shine yaya sai mahaifin Aliyu ne kane, da yake a wacan lokacin ni da Momy a makaranta kawayen juna ne sosai tare mukai karatu a ABU zariya, mahaifin Aliyu dan'uwanta ne sun hada kakanni daya kuma......”

Ganin Nana ta zuba mata ido sai ya saka ta ji kunya har da yin kasa da kai.

“Ataa na yawan ba ni labarinki ai”

“Ehhh Wallahi ni ce fa Mama Fulanin dai, Allah sarki Ataa baiwar Allah, Wallahi Ashe abun haka ne, Wallahi ehh huh”

Mama Fulani sai kame kame take cike da kunya. Sai ta mike tsaye ta nufi kitchen.

“Ban ma dora girkin rana ba da yake bana dan jindadi, Rukaiya ki kaita gurin Ammynku su gaisa kamin na gama abincin, sai dai ban sani ba ko kina da ra'ayin wani abun da za a dafa miki?”

“Aa”

Nana ta amsa tana mikewa tsaye ta bi bayan Rukaiyah wacce tuni ta nufi kofa, sai da ta fice Mama Fulani ta fadi zaune a kofar kitchen ta dafe kanta.

“Wai ni Allah wannan abun be min dadi ba, ai dai kam ba zata ci komai nawa ba, tun da yarta zata fada mata cewar na hanata ita, ai idan da kunya ni ma ba zan ce zan bata ko?”

Magana take kamar mai yi da wani gaba daya abun ya dameta a yanzu, wacce suke wulakantawa suna gani ba komai ba, yau ta koma sama da su, a cikin arzikin kakanta suke tsoma ludayinsu su ci.

Kamar kallon yadda Ammy take da far'a haka ta amsa mata sallamarta tai mata lallen marhabun, sai a lokacin Nana ta dan saki jiki har tai murmushi Rukaiya sai kallonta take ganin ta sakewa Ammy, kamin ta juya da fita.

“Aiko yanzu yanzu nan Aliyu ya fita tare da Ataa”

“Allah sarki ke ce Ammy ko?”

“Eh ni ce Allah dai ya sa lafiya?”

Ammy ta fada tana dariya sai Nana ita ma tai dariyar.

“Lafiya kalau labarinki na ji a gurin Ataa, har da kowa da wa yaranki”

“Allah sarki ina ruwan Ataa, yaran duka basa nan sai Humaira ita ma yanzu ta fita ko bangaren Hajiya Fulani tai ban sani ba, ya gida ya hanya?”

“Alhamdulillah”

Ammy ta shiga ciki ta kawo mata ruwa da da dan abun tawa, a nan kam Nana ta sha ruwa har da cin abinci ma domin ita ta gama nata abincin rana tuni, Mama Fulani ma abunda ya faru ne yasa jikinta yai sanyi har taji kamar bata da kuzarin girkin.

Mama Fulani na zaune bakin kofar kitchen din tana jimami sai ga Rukaiya ta dawo tana labarta mata cewar Nana ta sake a gurin Ammy har da dariya. Mama Fulani dai abun duniya ya isheta ta bata ce komai ba sai domin ta san duk abunda akai mata bata da bakin magana a yanzu kuma ta cancanci fiye da hakan ma. Maryam ce ta fito rike da wayarta ta sauko kasa ta kawo mata. Ganin number Nasir yasa tai saurin picking.

“Mama ina wuni?”

“Lafiya Nasir ya gida”

Ta amsa da muryarta kamar ba ita ba.

“Lafiya Kalau Mama kira nai na miki albishir kamin kowa ya riga ni”

Gabanta ya fadi domin a halin da take yanzu tsoron jin komai take.

“Albishir kuma?”

“Eh Ataa ce bata jindadi Aliyu ya kaita Asibiti shine suka ce ciki ne”

Dif Mama Fulani tai daukewar wuta, ta zaro ido ta mike tsaye da sauri sai kuma ta cire wayar daga kunnenta ta duba mai kiran ta ga Nasir din dai ne ta sake mayarwa a kunnenta sai idonta ya cika da kwalla.

“Allahu Akbar, Allah mai iko Allah sarki”

Ta kashe wayar sai ta koma saman sofa ta zauna sai hawaye suka fara mata sallama.
Chapter 118 · 0% Book details