← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 143

Sashe 112

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Wani irin kuka na ke bai ban tausayi da taba zuciya ni kaina ina jin wani yanayi da ban taba jin irinsa a sai yau, taya zan iya bayyana ganin farinciki? Farincikin mahaifiyata? Kakana? Kai tsaye kuma a saukake ban taba kawowa raina haduwa da shi a nan kusa ba. Ban taba tsammani abun zai zo da sauki kamar haka ba. Ji nai an shafa kaina sai na dago da saurin domin tantace mai taba nin shi din ne ko wani? Shi ma kwalla ce a idonsa irin da tsufaffin da basa son bayyana kukansu. Daga cikin wanda yake tare da su ne suka zo za su rikani su raba ni da kafafuwansa da na rike sai an kara rike su da sauri na fashe da kuka, a take ya daga musu hannu Alamar su kyale ni. Wani irin kuka nake kamar dacan an halitto kukana dan zuwan wannan ranar ne kawai, tun ina a hankali har muryata ta fara shakewa, sai Aliyu ya matsa kusa da ni ya dafa yana kokarin raba ni da jikinsa.

“Ayusher ya isa haka”

Kai na girgiza masa na sake rike kafarsa, dadi na ke ji yau na ga wani daga dangina, yau na ga mutumen da Nana take ba ni labarinsa, ban tana gani wani dan'uwa daga jinin Nana ko jinin Mahaifina ba, sai yau taya ba zan yi kukan dadi da farinciki da tausayi da takaici a lokaci daya ba? Hannu ya daga wa Aliyu kamar yadda yai ma sauran, a dole Aliyu ya kyale ni yana ta damuwa da kukan da na ke, ni kuwa na samu damar yin kukana iya son raina har sai da na ji an samu natsuwa sannan nai shiru dan kaina amman ban sake kafar ta shi ba. Sai a lokacin na lura da hankalin kowa yana kaina, cikin har da Mama Fulani da Maryam da Rukaiya da Ammy da yayanta da ban san lokacin da suka shigo ba.

“Waya fada miki cewar Mai Martaba shine kakanki? Taya za mu yarda da ke?”

Dayan ya tambaya da yaren buzanci.

“Ita ta fada min, kuma na ga kamaninta a fuskarsa, idan kuma kana musu ne zan iya kai ku har inda Nana take”

“Asma'u.....ta....na...ra.... ye?”

Wannan karon Mai Martaba ne da kansa ya tambaya maganar tana fitowa da dai daya daga bakinsa cike da kasaita da izza irin ta manyan sarakuna.

“Tana raye amman bakincikin rashinka da duka danginta ya dade da kasheta, kullum mafarkina ni da ita a ina zamu ganka, ta wace hanya zan sadu da kai? Mai Martaba ba ni da kowa sai Nana aka Nana kuma vata da kowa sai kai, ban sanka ba ban taba ganinka a ido ba amman ta kwadaita min kaunarka da son ka da kuma son rayuwa da kai, kullum kukana a kanka mafarkina ni da Nana na ka ne”

Lumshe ido yai ya hade ya sauke ajiyar zuciya a hankali.

“Ki daina magana haka Mai Martaba baya son yawan magana, kuma ya kai matsayin da ba komai ake fada masa kai tsaye ba”

Daya daga cikin samarin ya fada. Sai ya bude ido ya daga masa hannu.

“Barta ta fadi iya abunda zai mata dadi, ita ma jika ce kamar kai, ita din jinin Asma'u ce Asma'u kuma jini na ce, jinina kuma na duka iyalaina ne”

Duka da yaren buzanci mukai wannan maganar daga Mai Martaba har ni har jikansa na sa. Wani irin dadi ne ya lullube ni jin yadda ya kira ni jikarsa jininsa kai tsaye ba tare da tantama ba, ba kuma tare da kyama ba. Murmushi nai na sake rumgume kafafuwana ina jin wani irin sanyi da Rahama irin ta kaka da jikasa. A take na ji amai na cika min baki da sauri nai baya ina kokarin mikewa kar ma sa shi jikin nai kofa da sauri sai dai kamin na kai tuni aman ya cika min baki ni kuma na bashi hanyar fitowa.

“Subhanallahi”

Ammy ta fada tana nufo inda nake kamin ta kawo tuni Aliyu ya zo ya rika ni, shi ya fito rike da ni harabar wajen na fara sheka amai kamar zan amayarda duka hanjina domin har ta hanci zubo min yake ban taba amai mai wahala irin wannan ba. Ina gamawa Aliyu ya zaunar da ni Batula ta dauko ruwan gora ta miko masa ya wanke min fuskata ya zuba min a hannunsa ya dura min a baki na kuskure ya zubar.

“Sannu”

Ya fada cike da tausayawa, sai na gyada masa kai ina jin wani irin jiri na dibana kaina kuma yana ciwo sosai har bana son daga idona.

“Bari na janyo mota sai muje asibiti”

“Aa bana so dan Allah”

Na fada da saurin domin har ga Allah bana son zuwa asibitin, daman can ni asbiti ba burgeni take ba, kuma ina ganin idan na bar gidan Sarkin Agadaz zai iya tafiyarsa ban sake magana da shi ba.

“Amman jikinki ya yi zafi sosai kuma.... ”

“Aliyu idan bata son asibitin ka barta tasha magani sai ta kwanta idan idan ta farka abun be sauka ba, sai a tafi asibitin”

Ammy ta fada ganin zan saka kuka saboda kawai ance aje asibitin.

“Aa ni bana jin bachin ma”

Na fada idona na cika da kwalla.

“Aliyu mu koma ciki ina son magana da shi”

“Ki barshi ya huta idan ya huta zai ce a kira ki ai”

Aliyu be gama rufe ba ki ba, sai ga daya daga cikin jikansa ya fito yana fada min Mai Martaba na son ganina. Da sauri na mike tsaye sai Aliyu ya rikani domin bana iya tafiya da sauri jikina kuma ba karfi ga jiri na dibata, daf da zamu shige bangaren Abbah muka ji tsayarwar mota, sai na waigo na hango Muhseen ya fito daga motar da waya a kunnensa, ni kuma na juyar da kaina muka shiga cikin falon, wannan karon babu kowa a ciki sai shi kadai da jikokin nasa. Daga bakin kofar Aliyu ya tsaya ya bar ni ni na wuce can ciki. Kasa na zube kusa da shi na zauna yana ta kallona a hankali ni kuma nai fuskar tausayi ya langwabar da kaina ina kallon kasa.

“Ina Asma'u take?”

“Tana sakkwato”

Na amsa mishi da sauri cike da kaguwar jin abunda zai sake fada.

“Ta fada miki dalilin rashin danginta a kusa da ita?”

“Ta fada min kuskuren da ta aikata, kuma ta yi nadama sai dai ta ce ba zata koma gareka ba har abada saboda abunda ta aikata maka, ta ce ta saka masarautarsu a kunya, da maka butulci ba zata sake dawowa gareka ba saboda ba zaka taba gafarta mata ba, ta yi kukan rashinka ta shiga matsalolin rayuwa ta rasa muhallin zama da abun sakawa a baki saboda butulcin da tai maka, a cikin abubuwan da ta rasa mai martaba har da lafiyarta, kuma ta alakanta hakan da butulce ma iyayenta da tai, a kullum tana fada min rayuwarta ba mai tsawo ba ce ta min umarnin na nemi danginta bayan rayuwarta kuma na roka mata gafararka da na su, ta haife mu ni da kanena shi ma har ya rasu gurin bara be san ka ba, tana bakincikin gina wata rayuwar ba tare da kai ba, da ni da ita duka rayuwarmu a titi ne sai mun yi bara muke ci, gidan kuma za mu kwanta sai dai mu raba a gidan wasu mu kwana”

Tun da na soma maganar yake ta jinke hannusa da sandar da ke hannun nasa, da alama maganganun da na ke masa sun taba masa zuciya ko kuma basa masa dadi.

“Ina Umar?”

“Ya rasu, Nana ce kawai ta rage sai ni”

Na fada cikin kuka, sai ya mika hannunsa da sauri jikan nasa ya risino yana sauraren maganar da ke fitowa daga bakinsa kadan-kadan.

“Ta fada muku inda Asma'u take ku je ku taho da ita”

A take ya karaso inda na ke yana tambayata da yarenmu.

“Ina Asma'u take?”

A take na fada masa, sai ya fice daga falon.

“Tashi kije ciki zan je masaukina”

Mai Martaba ya fada min, sai na mike tsaye ina jin kamar kar na tafi na fito daga dakin, sai na samu Aliyu a tsaye yana jirana.

“Kin yi magana da shi?”

Ba gyada masa kai.

“Eh yace zai je masaukinsa”

“To muje ciki ki huta”

“Mama Fulani ba zata bar ni na shiga dakinta ba, na kai ni gurin Ammy”

Na fada ba dan ina da tabbacin Mama Fulani zata hana ni shigar ba, sai dan na fi son Ammy da ita kuma zan fi sakewa a can. Be min musu ba ya gyada min kai sannan muka sauko tare muka nufi bangaren Ammy. Muna shiga falon Zee da Humaira suka fara min sannu na amsa musu har da Inteesar da ke ta daukin ganina.

“Ataa mun yi missing dinki sosai”

Ban ce mata komai ba bayan murmushin karfin hali da nai mata, sai Aliyu ya kalli Zee ya ce.

“Zainab kwantawa za tai a dakinki kar motsi ko wani hayani ya tashe ta dan Allah”

“Okay ya Aliyu”
Chapter 112 · 0% Book details