← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 143

Sashe 123

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

After fitar Aliyu Mama Fulani ta dauki wayarta ta kira Momy ta labarta mata abunda ya faru tana rokon ta yi ma Nana magana saboda ta fi ganin kimarta sama da ita, kuma tana ganin kamar ran Aliyu ya bace saboda ta ce ba zatai maganar ba.

“Wannan aikin ai na ki ne Fulani, ke da danki akwai wanda ya isa ya shiga tsakaninku?”

“Da dai ace duka sannan be faru ba da zan iya yin komai amman yanzu bana da wannan yancin”

“Ki manta da abunda ya faru, dukan abunda ya faru kin aikata ne a cikin rashin sani da kuma rashin tunani, daga d'an ki har ke kun yi wa talaka da talauci wata gurguwar fahimta ne, ba ku ganin kimar wanda ba shi da shi matukar mutum talaka ne ba shi kima ba shi da yanci a gurinku, shiyasa bana son munana kiyayyah ko tsananta soyayyah wata rana wanda kake ki ne zai dawo masoyinka wanda kake so kuma ya zama makiyinka, tun daga lokacin da Nasir ya labarta min zancen samun cikin na ga ba ki kirani ba na san ba ki cikin jindadi, ba kuma na samun cikin ba sai na kunyar abunda kika aikata, a yau duk wata naira da izzar dukiya da kike takama da ita Fulani Ataa ta damata ta shanye tun da kuwa Kakanta ne mai wannan arzikin, kuma na jidadin hakan wata kila da ba ta haka abun ya zo ba da har yanzu ba ki gane cewa akan kuskure kike ba, wata kila da har gobe ba zaki yi nadama ba balle a ranki kiji ko cewar kin aikata wani abu da ba daidai ba, na tabbatar da Ataa ta yi arziki ne ta hanyar d'anki da har jibi sai kin mata gori kuma kina ta kallinta kallonta da wannan tambarin na talauci wanda ba ita tai ma kanta shi ba, amman da Allah ya so nuna miki isarka da ikonta sai ya kawo wanda daga ke har Rahma za ku zauna a karkashin inuwarsa kuma ku wayi gari jininsa kuke wulakantawa”

Tun da Momy take maganar Mama Fulani take hawaye ko wani harafi da za a hade da dan'uwansa ya bada ma'ana sai da ya taba zuciyar Mama Fulani.

“Abunda ya faru ya riga ya faru, ki manta da komai ki maida komai ba komai ba, ki murje ido ki nunawa Ataa kulawa da kauna, domin su ne kadai abunda take bukata a yanzu, har yanzu akwai abubuwan da Ataa ta rasa, ilmi, iya mu'alama da mutane, zamantakewar rayuwa, girki da kuma zaman aure, Ataa yarinya ce da har yanzu bata wayancin wasu abubuwan ba, za ki iya maye mata gurbinsu a yanzu cikin hikima za ki nuna mata soyayya da nadamar abunda kikai, ko ba yanzu na sani dole wata rana za ki so Ataa ko ki zauna da ita dan dole tun da danki take aure, Fulani wannan ya iashe ki izna talaka ba abun wulakantawa ba ne, ko da ko ba ta irin sigar da Ataa ta zo miki ba, ba ki san inda wani talakan zai taima ke ki ba, ita rayuwar duniya makaranta ce dukiya da talauci kuma dukansu jarabawa ne ya kamata ki gane wannan”

Mama Fulani ta gyada kai kamar Momy na gabanta. Sannan ta saka hannunta ta share hawayenta .

“Na gane, amman har yanzu ina jin tsoro kuma ina kunya sosai”

“Wallahi ki gode Allah daya nuna miki haka tuna a yanzu ba sai da kika fada wata mummunar rayuwar ba, kuma ya saka miki saduda a take, daman can ban ga wani abun dagawa a dukiyar da zaka mutu ka barta ba, da arzikin da ba zai iya hana ka ciwo ko tsofa ba balle kuma mutuwa, yanzu dai abunda ya fi ki tashi da kan ki kije ki yi magana da mahaifiyarta ki yi kamar komai ba faru ba, ni kaina bana ra'ayin zuwanta gidan a yanzu, domin na san halin dan ki ba komai zai gani ya kyale ba sai yai ta nuna rashin kunya a gidan sarauta kuma ba a haka, kara dai sai cikin ya yi kwari”

“Allah Momy ba zan iya ba, abun da kunya sosai”

Daga dayan bangaren Momy ta yi dariya jin abunda Mama Fulani take fada wai da kunya, yau Mama Fulani ce take cewa tana jin kunyar yin wani ba wacce ke bugun gaba tana ganin ita tana da kudi kowa zata iya tinkara ta fada masa magana kai tsaye, kuma jin kunyar ma ta Ataa yarinyar da ta gama wulakantawa tana nuna mata ita din ba kowa ba ce.

“Na fada miki idan kika ce za ki dauki zancen kunya ki saka a ranki za ki yi ta cutar da kanki da d'anki ne kawai, ki kasa sama masa abunda yake so ke ma kuma ki kasawa bawa kanki, ni dai ina farinciki da yadda na ji halin nan ya sauko Wallahi, na dade ina jiran zuwa wannan ranar amman ban samu ba sai yau na dade ina nuna mu ku abunda kuke kuskure ne amman kuka kasa fahimta, sai da Ataa ta zo, lallai Ataa ta zama alheri a familyn mu”

Ajiyar zuciya Mama Fulani ta sauke a hankali sannan ta sake share hawayen da suka zo mata.

“Ina murna da samun cikin nan abunda muka dade muna nema, ashe Allah ya rubuto sai ta bangarenta za a samu, Allah ya inganta ya bata lafiya kula da shi”

“Ameen, yanzu kulawarta a hannunki take tunda kin san a nan za su zauna kusa da ke”

Mama Fulani ta yi shiru tana kallon Muhseen wanda ya shigo hannunsa rike da wasu magani har kala hudu.

“Na gode Sai kin sake ji na”

Mama Fulani ta fada sannan ta katse wayar tana cigaba da kallon Muhseen wanda fuskarsa ke cike da walwala.

“Mama ki sha wannan maganin yanzu”

“Na dazun ma ban sha na fa”

“Miyasa da kin sha ai sai ki sha wannan yanzu kawai, amman ki bar wacan ki sha wannan”

“Duka? Na ji zazzabin ya sauka ma da nai wanka fa”

Kusa da ita ya zauna yana murmushi.

“Mama ki sha kawai likita kika haifa fa, sai dai anjima zai iya dawo miki tunda tunanin yana nan cikin ranki”

“Tunanin me?”

Ta tambaya tana nuna kamar babu abunda ya dame ta.

“Na abunda ya faru mana Mama, kina ta jin kunyar Ataa ko?”

Ta yi shiru bata ce komai ba.

“Wallahi tun daga lokacin da kika fada min labarin nan, sai Ataa da mahaifiyarta suka kara burge ni, yanzu irin yarinyar da ake wulakantawa kamar haka ace ta san tana da family irin wannan amman ta yarda ta zauna a haka ta jure wulakanci da cin mutunci, kin san da wata ce tun daga lokacin da suka fara shiga gararin rayuwa za su fara neman yan'uwnasu ko da yankasu za ayi a ci namam su? Wani abun farinciki faruwar wannan abun ya saka a take jiki ya yi sanyi, kin zubar da makaman yakinki ga shi har kina jin ba dadi a abunda kika aikata, dubi Aliyu dazun davya shigo tare da ita part din Ammy abun har mamaki yake ba ni mai tsanar talaka ya koma son ta ko kunya be ji ba, ke ma kuma kina jin kunyar talaka kamar ba ku ba gaba daya, tun yaushe na ke son rayuwar ku ta canja Mama? Tun yaushe na ke nuna muku cewar talaka ba abun wulakatawa ba ne, amman kuka kasa ganewa ke da d'an lelen danki har kuna ganin kamar ni da Momy ba mu waye ba ne, lallai Ataa yar baiwa ce ita ta canja muku komai cikin kannen lokaci, ni kaina ina cikin farinciki a yanzu domin na samu wace ta fita, kuma raina yake so fiye da ita but the most funniest part Aliyu kishina yake har yanzu, ni kaina dunno why na ji kamar na tsani Ataa, but seriously tana burgeni akan wannan abun daya faru”

Mama Fulani ta mike tsaye ta nufi bandakinta ta dauka fanfon ciki ta kunna ta sha maganin sannan ya fito tana fadin.

“Yana ta damuna wai na je na yi magana da mahaifiyar Ataa akan tafiyar da za su yi kar su je da ita, ko kuwa ba ni da wannan damar a yanzu”

“Saboda me? Ataa fa dole ta girmamaki indai har tana ganin kimar mijinta, ke fa uwa ce a gurin Aliyu”

“Na sani amman ba yanzu ba”

“Yeah komai da sannu zai wuce kamar ba ayi ba Mama In-Sha-Allah”

Ya fada yana mikewa tsaye.

“Ya maganar kayanka? Idan ka shirya komai sai na yi ma Abbah ku magana”

“Ba yanzu ba Mama sai hankalinki ya kwanta, na fi son ayi komai kina cikin farinciki”

Ta gyada masa kai shi kuma yai murmushi ya fice.

ATAA POV.

Da tunanin abunda Mama Fulani zata fada min na shiga bangarenta, Aliyu ya fada min cewar tana son magana da ni amman akan me? A hankali na tura kofar falon na shiga babu kowa a ciki sai sanyin ac, ni kuma na zauna a saman sofa ban yi kaudi ko tunanin hawa sama inda take ba na zauna zaman jiranta har ta zuwa lokacin da za ta sauko.
Na kusan awa daya a zaune bata fito ba kuma wani be shigo ba, har na mike tsaye da zimmar fita sai na ji motsin saukowata hakan yasa na koma na zauna na daga kaina ina kallon yadda take takowa har ta sauko kasa, wani gefe gafe take da ido kamar ba ta ganni ba ko kuma bata son kallona.

“Mama Fulani Aliyu ya ce kina son magana da ni”

Shiru tai na wani lokaci kamin ta amsa min ba tare da ta kalleni ba.

“A a, wata kila dai be gane ba ne”

“Tau”
Chapter 123 · 0% Book details