← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 143

Sashe 83

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Be amsa ni ba ko inda na ke be kalla ba, ni kuma ban damu ba farincika ya gama cika zuciyata gaba daya, daga ilslamiyar ya wuce da ni gurin daukar hoto aka dauki hotona aka ba shi, fiye da kudin hoton ya bawa mutumen, abunda na lura da shi idan zai maka alheri ko ya baka hakkinka sai ya ninka maka ko kuma ya baka abunda ya fi yawan nawa, na yi zaton daga nan gidan za mu koma sai ya nufi AGG da ni, ban taba shiga shagon ba tun da nake ganinsa sai dai kawai na bi an wuce amman har bara na yi a gurin shagon lokacin da nake tsananin bukatar kudin nan.
Yana gaba ina binsa a baya sai rabon ido nake ina kallon kayan shagon ina ta kalle kalle da kansa yake zabon kayan ciki, yawanci gowns ne na abaya da riga da skirt na kanti, sai takalmi masu kyau ta ki hudu, sai da ya biya kudin sannan suka saka masa a mota muka fito muka shiga motar ya dauki hanyar wata plaza da ni, wannan karon a motar ya barni ya shiga ciki domin be bude min dan na fito kamar yadda yai min dazun ba, ni kuma na zauna a cikin motar har yayi abunda zai yi ya fito wani na riko masa manyan ledodi.A bayan mota aka saka masa musu sannan ya shigo motar yana cin wani abu mai kamar chocolate kuma ba chocolate ba, ya ci kusan rabi sannan ya miko min sauran sai na karba na saka gefen hijab dina na goge kufan bakinsa sannan na ci, ido ya saka min yana ta min kallon rainin wayo sannan ya tashi motar muka kama hanyar gida ana kiran sallah magariba.
A harabar gidan ya faka motarsa ya bude boot din ni kuma na bude na fito rike da uniform dina zan tafi bq sai na ji ya ce.

“Wa za ki bar wa wadannan kayan?”

Dawowa nai na dauki ledodin na yi zaton cikin falonsu za a shigar masa da su sai na ji ya ce.

“Leda ukun ne na ki biyu Mamanki ne”

Na zaro ido ina bude baki.

“Da gaske da gaske”

“Da karya”

Na fada ba tare da ya kalleni ba ya rufe boot din ya nufi sashen Momy, wani tsalle nai na dire rai na fes, a gaskiya yau Aliyu ya burge ni domin na kura shi ma yana da mutunci kamar Kamal sai dai Kamal ya fishi son mutane da far'a. Nana ma ta yawa sosai da ganin kayan da kuma halin Aliyu daman tun muna asibiti take ta yabonsa tana ganin kirkisa sosai, wannan karon har da cewat tana mamakin yadda hake ga hidima da ni haka. Bayan sallah isha'i Nana ta ce na je na masa godiya kuma na ce ita ma tana masa godiya. Rigar jikin na cire na saka daya daga cikin Egypt abaya da ya siya min na saka na yafa mayafinta sannan na nufi part din rigar sai kyalkyali take ko'ina na jikinta.

Da sallam na tura kofar falon na shiga, sai Momy ta amsa min da far'arta Aliyu yana zaune saman cushion ya hade rai sosai kamar an masa wani abu, ina juyowa sai na Muhseen tsaye yana sakar min murmushi.

“Laaa Ya Muhseen”

“Pretty na”

Ya fada yana kallon yadda rigar ta karbe abun ka da farin mutum ya saka babaken kaya.“Yaushe ka zo?”

“Yanzu nan, jiya na ban ji a waya ba kuma ina da bukatar ganinki shiyasa na zo, ya kike?”

“Lafiya kalau”

Na amsa ina dariya kamar an min wani abu, ni dai har ga Allah ina son mutum mai far'a da dariya kamar Kamal da Muhseen, sai dai Kamal ya fi kwanta min sama da Muhseen din kuwa da kasancewar shi ma yana min far'a sosai, kusan sai na ce duka suna burgeni kuma ina son su.

“Kin yi kyau pretty na rigar ya karbd ki”

Ya fada yana rika rigar nawa ya buda ta tai fadi.

“Eh dazun Aliyu ya siya min ita Nana tace na zo na masa godiya”

Yanayin fuskar Muhseen na ga ta canja sai ya dan wara ido yana zolayata.

“Hop kin daina sake jikinki dai domin na lura ana sake miki da yawa”

“Sake jiki kuma?”

Momy ta tambaya sai ya kalleta

“Yes, lokacin da take Abuja a garden take wanka, a gareji take canja tufafi sai da na mata magana”

Juyowa Aliyu yai ya kalli Muhseen yana lilo da kafarsa wacce dayar ki saman daya.

“Ka ganta kenan? Shiyasa ka ce kana son ta?”

“Idan ma haka din ne ai ban yi illa ba”

Tasowa Aliyu yai daga saman kujerar da yake zaune yana fadin.

“Ataa ba ki da hankali kuma kurciya na damunki, Momy kina ganin abunda na ke fada miki ko? Ya ganta tana wanka ta na canja tufafi kuma shi ne yanzu a tsaye a gabanki har kina amsa dariya? Wallahi baki san ciwon kanki sam”

Muhseen yayi murmushi har zai yi magana sai muka hi Aliyu ya kyalkyale da dariya mai karfi wacce ban taba zaton bakinsa na iya irin wannan dariyar ba.

“Magana ta fito Muhseen kana son Ataa saboda ka ganta a sirara, Wallahi wannan nuna mata rashin daraja ne da raina mata hankali, what a shame lallai kai yaro ne kuma wawan duniya tun da har tsiraicin yake maka sha'awar kallo what a sad”

Yana fadar hakan ya fice yana dariya dariya irin sosai din nan kamar ba ta hankali ba.ALIYU POV.

Duk wata dariya da yake na fuska ne kawai amman ransa cike ya ke da bacin rai da bakin cikin jin cewar Muhseen ya taba ganin Ataa tsirara wani abun yaji marar misaltuwa har yana jin kamar kirjinsa zai rabe biyu, sai kuma ya ji kamar ya danne Muhseen ya cire masa idanuwa. Be san abunda ya kawo shi yau ba ma, gashi yana cewa ba za a tafi da Ataa abuja ba saboda shi da Kamal shi kuma yazo yanzu.
Yana faka motarsa harabar gidan sako na shigowa wayarsa, ganin sunan Rahma yasa shi budewa domin baya cikin mood din saurare kowa a yanzu.

_I'm sorry akan abunda ya faru, Mommy ta yi fushi ne sosai shiyasa amman dan Allah ka yi hakuri, kuma ina neman izininka zan tafi Dubai jibi_

“Really?”

Ya furta bayan ya gama karanta sakon.

“You will regret this Rahma ke da iyayenki”

Ya fada sannan ya bude motar ya fita zuwa cikin gidansa, haka ya kwana a gidan cikin wani irin yanayi na bacin rai tsakanin wanda Rahma tai masa da abunda Muhseen ya fada sai ya rasa wanne ya fi masa zafi. Ko da ya tashi da safe kansa kamar zai tsage sabar bacin ran daya kwana da shi jiya, he feel unsafe sai da yai wanka ya shirya cikin wasu tufafin ya dauki hanyar arkilla tun da farar safiya haske ma be gama bayyana ba. Ko da ya shiga falon babu kowa sai ac da wutar da aka kunna, but he got lucky yau Momy a part din ta tai sallah asuba after Daddy ya tafi masallaci ita kuma ta dawo part dinta tai sallah, daman ta kan yi haka wani lokaci wani lokacin kuma acan take yin sallah ta. Tura kofar dakinta yai ya shiga ba dan ya tabbatar tana ciki ba, idan ma bata ciki shi zai kwanta a nan ne for a while hankali zai fi kwanciya ace yana gidan fiye da yana can dabam. Zaune ya same ta saman carpet karbin a hannunta tana ja. Ita kanta ta yi mamakin ganinsa da safen nan.

“Lafiya dai?”

“Lafiya kalau Momy ina kwana”

“Lafiya Kalau, amman ba lafiya na ka zo da safen nan”

Ya yi shiru na wani lokaci sannan ya ce.

“Momy wai Rahma ta turo min sako zata je Dubai”

Da mugun mamaki Momy ta kalleshi.

“Dubai? Da izinin wa?”

“Wai izini take nema”

“Uhmm Wallahi Rahma nan ta maida wani sholobiyo, daman tun farko kai ka nuna mata fita ba da zininka ba ai, yanzu kuma ganshi ba nan, maganinta kamin ta dawo ka auri wata Wallahi”

“Yes nima abunda na kwana da shi a raina kenan”

“Haka ma za a mata, kuma idan zaka bi nawa Ataa na ke son ka aura wacce ta raina take ganin ba komai ba ce”

Kamar saukar Aradu haka Aliyu ya ji maganar Momy, Ataaa Ataaa Ataaa Ataaa sunanta na ta maimaita kansa a kunnensa, da sauri ya kalli Momy.

“Momy Ataa?”

“Yes”

“Amman..... ”

Sai kuma ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu ya daga kansa sama yana shakar iska kamin ya sauke ya juyo ya kalli Momy.

“Momy seriously?”

“Yes don't you like her?”

“I do, but.....”

Sai murmushi ya subuce masa ya shafa kansa.

“Momy ke kike fada min wannan da kanki? I can't believe this”

Murmushi Momy ta yi.

“Do you love her?”

Shiru yai na wani lokaci yana sauraren yadda zuciyarsa ke mugun bugawa with full farincikin da be daga ina yake sauko masa ba.

“Momy wasa dai kike min?”

“Indai tana son ka da gaske na ke yi”

“Zata so ni mana Momy ai ita bata san so ba, zan koya mata komai Momy trust me”

Ya fada yana dukawa ya kama hannayenta duka biyu ya rike, shi kanshi sai yanzu yake jin cewar son Ataa yake yi, duk wani abun da ya dade yana jinsa akanta sai yanzu kullin ya watse a jikinsa da zuciyarsa, domin tun da ta zo duniyarsa sai yake jin kullum kamar a takure yake.
ZAKI

By Khadeeja Candy

39...

Kamar an diga man kuli a cikin ruwa mai mugun sanyi haka Aliyu yaji jinin zuciyarsa ya taso yayi tsama saboda kalaman Muhseen.

“Kai Pretty wai kin duba madubi yau ko? Gaskiya Allah ya iya hallita”

Cewar Muhseen yana kara kallon yadda uniform din yai mata mugun kyau kasancewarsa Maroon color, ga gashin kanta data sakawa ribbon ya sauko har bayanta gwanin sha'awa. Ko wace kalma ta Muhseen Aliyu hade ta yake da yawun bakinsa, ba kuma iya yawun ne kawai yake hadewa ba har da abunda yake ji yana taso masa yake dannewa, shi kanshi ya san yayi abunda ba zai iya ba, yana tsaye wani na yaba kyau matarsa.
Chapter 83 · 0% Book details