Sashe 74
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Magana yake da kansa yana kallon madubin dakinsa, yana jin wayarsa na ringing amman ya ki ya duba mai kiran ma balle ya daga. Bathroom ya shiga yai wanka yana fitowa ya shirya cikin kananan kaya sannan ya dauki wayar yana duba miss calls din da Momy ta jera masa, kiranta yai da dayan layinsa da be cika kiran mutane da shi ba.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya Kalau Muhseen, miya nai ta kiranka ka ki ka daga? Kuma ya wuce na tare da ka min sallama ba?”
“Kawai raina ne ya bace, amman ki yi hakuri dan Allah”“Ranka ya bace saboda na fada maka gaskiya Muhseen? Har ga Allah yarinyar nan yanzu ba soyayya ce a gabanta ba, bana jin ta san wani ma wai so, ta mahaifiyarta take shiyasa ban goya maka baya ba, komai ai dan a hankali ne”
“Ba abunda kike ce min ne kawai ba Momy, har da yanayin da na ga Ataa din wata kila wani abun Aliyu yace mata a kaina domin na ga tana daridari da ni ba kamar da ba”
“Idan ma wani abun ya fada mata ba damuwana ba ne, kai na ke son ka kwantar da hankalinka idan komai ya daidai kai kanka ka sani ni mai nema maka auren yarinyar nan ce tun da har ka furta kana son ta”
“Na gode Momy, amman Mama ma bata so ta min fada sosai yau saboda Ataa tana ganin kamar be dace na aureta ba, jarabawa ce kawai Momy kuma na hakura da ita”
“Haba dai, wane irin ka hakura da ita kuma? Fulani uwa ce kawai ba uba ba, ba ita zata maka aure ba, kuma zan tattauna da ita amman sai hankali ya kwanta komai ya daidai ta na maka alkawari”
“Na gode sosai Momy”
Daga haka ya sauke wayar a kunnensa ya saka aljihunsa ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin.
ALIYU POV.
Da yamman ya koma gida ba dade wurno road din ba saboda ya san ran matarsa yana can a bace. Kamar wanda aka koro haka yai fakin a cikin gidan ya fito da sauri ya shiga cikin falon. Kai tsaye dakin Rahma ya wuce ganin bata falo sai ya samu a dakin ma bata nan, be kawo cewa tana dakinsa ba domin ba ta cika shiga dakinsa idan baya ciki ba, sai ya sauko ya leka kitchen be same ta a nan ba, tunani daya ne ya zo masa arai wata kila ga hi fushi ta tafi gidansu.Remote ya dauka ya kashe tv falon sannan ya nufi dakinsa yana bude batulan rigarsa. To his surprise yana shiga dakin ya same ta zaune kasa kusa da bed dinsa tana hawaye. Cikin sanyin jiki ya karasa kusa da ita ya zauna yana kallon fuskarta.
“Minene Rahma?”
Dagowa tai ta kalleshi tana hadi yawun bakinta idonta yayi ja sosai alamar ta dade tana kukan kenan.
“A daina kula da ni a yanzu, da a da nd da kanka zaka dawo ka ba ni magani ko ka kira waya ka tambaya idan na sha amman yanzu baka damu ba, ka canja Aliyu ka tashi daga sanin da nai maka zuwa wani dabam, babu ruwanka da matsala a yanzu, da a da ne ba zaka iya zuwa ka kwana wani gurin da ba kusa da ni ba, idan ko har ba kusa da ni ba to a gida zaka kwana ba wani gurin ba, ka kwana a gida ka bar matarka ta sunna saboda wata matar da baka san inda ta fito ba, kana tunanin ka min adalci kenan?”
Hannunta ya kama ya rike yana matse shi cikin hannunta.
“Na sani wata zan zama babu ni, ina kawo abubuwa da yawa a rai, kamar samun lafiyata a can baya, yanzu kuma mutuwa ta, samun haihuwa wata rana da kuma dawwama a haka, amman ban taba kawowa cewa zaka so wata macen bayan Rahma ba, amman na ga ni ba ma ji nai ba, ba zan iya dawainiyar kishi a yanzu ba Aliyu idan har ka fara son wata ka sallame ni ka ji da ita ni kuma na ji da ciwo na, na sani ka yi kokarin zama da ni, amman idan ka yi hakuri wata kila ba zan dade ba zan tafi na barka sai ka auri wacce kake so, na kasa fadawa iyayena matsalar nan tun bayan wacan matsalar da muka samu na san idan har na fada musu za su nemi raba aurena da kai, saboda gudun bacin raina, amman bana son aikata hakan ya zama kamar butulci a gareka na san zaka kalli cewa iyayena ba su kyauta maka ba...”
Matsawa yai kusa da ita ya jata jikinsa ya rumgume.“Babu kowa a cikin zuciyar Aliyu sai Rahma, ke kadai na ke so Rahma ban daina son ki ba kuma ba zan daina ba har abada, ba wai na gaji da dawaniya da ke ba ne, wannan dawainiyar da ke da yarinyar nan ma saboda ke ne, duk wani hali da yarinyar nan ta shiga saboda ke ne, bayan tausayinta da tsoron ta shiga wani hali babu komai a zuciyata, ba son ta na ke ba Rahma”
Dago kanta tai ta kalleshi.
“Amman Aliyu saboda ita ka zo nan ai, kuma tana gidan Momy kana kula da ita”
“Momy ta sauke ta gidanta ne saboda ba su da wani gurin zama a yanzu, idan aka barta ita kadai zata iya shiga wata rayuwar dabam, ba saboda ita kawai na zo nan ba har saboda ke kin sani Rahma ina kauna sosai mi zai saka ki tashi hankalinki?”
“Aliyu kana da kyau da siffa mai kyau ba ko wace mace ce zata daga maka kafa ba, balle kuma ace kai na nuna mata so da kanka, ina kishin ka so wata Aliyu ina jin zuciyata kamar zata fashe ina jin duk ranar da ka auri wata mutuwa zan yi”
Ta fada tana kamkameshi kamar zata shige cikin jikinsa. Wani kalar tausayin matarsa ne ya lullube shi shi kansa ya san be kyauta mata ba, ya kwana wani gurin bayan ita tana gida tana sammanin dawowarsa. Saman kanta yai kissing yana shafa bayanta.
“I'm sorry”
“Yanzu yarinyar tana ina? Gidan Momy ita da mahaifiyarta ko? Ta tare a can so that ka rika ganinta tana jindadi ko? Na sani ai tana son ka, dole ai zata so ka”
“Yarinyar nan ba son kowa ne a gabanta ba, mahaifiyarta na asibiti tana jinya? Hankalinta yana gurin mahaifiyarta ne”
“Wace asibiti?”
Be amsa ta ba, ya cigaba da shafa bayanta, ita kuma bata sake tambayar ba, bata bar jikinsa ba sai da aka kira sallah magariba. Sannan ya daga ta daga jikinsa ya shiga bathroom yai alwala, tana ganin ya shige ta yi saurin mikewa tsaye ta nufi dakinta wardrobe ta bude tana duba kayan cikin ba dan zata saka ba sai dan ko shigowa yai ya tararda ita tana wani abun. Be shigo dakinta ba sai dai ta ji lokacin daya sauka kasa ya bude kofar falon ya fita. Gurin windows ta koma tana lekensa, hangoshi ya fita ba tare da mota ta san ba zai je nesa ba wata kila da yayi sallah zai dawo gida.
Dawowa tai ta dauki wayarta ta turawa Muneera sako sannan ta goge ta shiga bathroom din dan yin alwala.ATAA POV.
Mun wuni da Nana tana ka ce bakinta, muna ta fira kamar ba rashin lafiya take ba, a yadda na ke ganin ta samu sauki a yau kawai na gode Allah ba adadi, domin idan abun ya daure a haka Nana ta dauko hanyar samun sauki fiye da wacan aikin da aka mata a asibitin Asim. Sai dai hakan be hana na wuni da rashin jindadi kalaman Muhseen na bankwana a gareni ba. Da dare Husna da Siyama suka kawo min mana abincin dare sosai suka so na bi su zuwa gida amman na ki, ko ba komai na san Nana zata fi sakewa idan ta gan ni zata fi sakewa ni ma kuma hankalina zai fi kwanciya idan ina ganinta duk kuwa da na san ba wani maganin zan iya mata ba.
Ni da Laraba muka ci abinci dare a ranar, sannan muka kwanta a Bedsheet daya Nana kuma tana saman gado, bachinta take da ninshari har garin Allah ya waye. Asubar fari aka tashe mu ni da Labara masu wankin daki muka fito waje sai da aka gyara duka ward din sannan muka dawo. Na yi zaton Aliyu ne zai kawo mana abun kari sai naga Husna da Siyama kamar dai jiya, bayan sun yi ma Nana ya jiki suka dauki kulolin jiya suka koma da su, haka nai ta rabon ido da rana ko Aliyu zai dawo amman be dawo ba, sai direban gidansu aka aiko da abincin rana ya kawo mana. Bayan wucewar direban tare da Labara dan tace zata fara zuwa gida ta gyara idan ta dawo sai ni na tafi na shirya. Nana na fara zubawa shimkafar da miyar ina ta bata tana ci a hankali har ta koshi na bata ruwa ta sha sannan na zubawa kaina na ci sai da na koshi sannan na zuba lemu na sha. Ina aje kofin wani mutum mai kamar masinja ya leko dakin mu.“Wai ance ana kiran Ataa”
“Wa ke kirana?”
Na tamabaya ina tashi tsaye na bi bayan mutumen da ya riga da ya fice. Hango inda ya bi yasa na bishi har muka isa wani dakin da nake zaton dakin likita ne muna shiga ciki zaton da nake ya zama gaskiya, domin kuwa dakin likitan ne sai dai macece tana hakimce saman kujerarta tana kallon laptop din gabanta tana murmushi.
“Hajiya ga nan”
Mutumen ya fada sai tai masa alama da ya tafi ni kuma ta nuna min kujera, bayan na zauna ya dauko wani katon wali ta miko min, sannan ta juyo da laptop din gabanta izuwa inda nake, Muhseen na gani a ciki yana zaune saman wata kujera mai juyawa da alama shi ma yana office din ne. Matar ta tashi ta fice daga dakin ta barni da laptop din da kwali a hannu, ban dauka da gaske na ke ganinsa a ciki ba har sai da yai min magana.
“Pretty ya jikin Mamana?”
Ya dan wara ido kamin na amsa masa.