← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 143

Sashe 82

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Aliyu ya ja ya katse kiran yana rika sitarin motar, sannan ya lalubo number wani abokinsa wanda ya san yana fannin makaranta ya kira shi ya fada masa cewar yana son a sama masa wanda zai rika koyar da wata karatu a gida, domin ganin yake Nasir be dauki abun serious ba, and idan ba karatun ya sakawa gaba ba yana ganin kamar Momy zata iya daukarta ta bawa Muhseen amman idan ta fara karatu dole zata kyaleta.

ATAA POV.

lokacin da na bar falon da kuka na fito zuciyarta cike da jin haushi Aliyu da nasan cewar hana tafiyar zai yi da tun farko ban fada masa ba. Gurin Nana na dawo lokacin tana balcony zaune ni kuma na wuce dakin na hau kan katifa na kwanta ina ta kukana a hankali dan bana son Nana ta ji. Ina jin lokacin da Momy da kanta ta kawo mana abun karya har ta zauna kusa da Nana tana tambayar ina na ne.

“Ya sega ciki dazun ya shiga ta kwanta”

“Ko ta yi fushi ne saboda na ce ba a a Abuja da ita ba?”

“Abuja?”

“Murna za muje yi to tace zata bi mu amman yanzu Yayansu ya zo ya ce ba za a je da ita ba, wai ba zata je ta barki haka ba”

“Ataa haka yake ai wani lokacin da haurin hutsi amman nan da nan ka sauka”

Ban san abunda ya bawa Momy dariya ba har sai da tai magana bayan gama dariya.

“Ke har yanzu hausarki bata gama fitowa ba”Sai na ji Nana ma ta yi dariya ta ce.

“Da san kai baka iya hausa ba, baka ji hausa ba sai faranse sai buzanci, kadan kadan ka fara jin hausa har ka ji ka sosei sosei”

“Amman kin ga Ataa ita ta iya hausa sosai sam ba zaka ce ma tana jin buzancin ba in ba dan kammani ba.”

“Ataa ya tashi cikin hausawa, tun kuna kamba kai da babanka har ka zauna argungun har ka dawo sekoto, Ataa da Lukman mai mutuws duk ka ji hausa sosei”

“Ku yan wani gari ne Nana? Na ji kin ce kun zauna kamba?”

“Daga Agadez ka gudu doso daga doso ka zo kamba sai ka yi argugun ka yi bodinga ka yi sokoto, kana ta yawa yawa yawa kai da mai gida na mu”

Momy ta dade tana fira da Nana a nan na ji cewar a ni a kamba aka haife ni Lukman kuma a sokoto, wanda da duk ban san da hakan ba, domin ni na yi wayo ya bude ido na ganni a sokoto ne kawai kuma ban taba tambayar dalilin zuwanmu ba balle inda aka haife ni.

“To amman miya kawo ku garin nan na? Miyasa kuka baro garinku Agadaz?”

Daga wannan tambayar da Momy ta yi ma Nana ban sake jin Nana ta ce koma ba har na tsawon lokaci, can kuma na ji Nana ta ce.

“Labarinka ba se da dadi ka ji ma kunnenka, baka son kana tuna baya ba se da dadi ka ji, amman kai babban mutum ne mai kima da gima amman yanzu ba shi da amfani, ka koma kai kadai mijinka ya tafi ya barka dan ka ya tafi ya barka yanzu ka koma kai kadan sai Ataa”

“Muna tare da ke Nana, sanin wacece ke ba shi da amfani ma yanzu kuma na jidadin da aka samu Ataa ta hanyar aure, shine babban farin cikina”

Shine abunda na ji Momy ta fada kamin Nana ta dora da nata tana ɗaɗa hannunta.

“Ahhh Ataa yana da ubanta mai kyau kyau kyau kyau sosei, kai ne Ataa ta biyo ai, uban Ataa kana da kyau kana da fari kama da gasi kamat balaraba”

“Allah sarki Allah ya jikanshi, ashe Ataa shi ta biyo domin na lura yata ta fiki kyau sosai, bari na leka bangaren Daddynsu na bar shi shi kadai”

Daga haka na ji ficewar Momy faga bq din ni kuma na taso na share ragowar hawaye na fito na zauna kusa da Nana na rumgumeta, cewar Ni kadai na rage sai ita ya taba min zuciya, ban taba tambayar dalilin zuwan mu nan ba, da kuma rashin kowa a nan ba, domin ban tana kawowa rai komai ba, kuma na lura kamar Nana bata damu da hakan ba, sai yanzu ina da bukatar ji domin na lura yan'uwa suna da rana ko da kuwa talakawa ne na tabbatar da ace wani nata yana kusa da ita da bayan ni da Doc Asim be isa ya mata haka ba. Da yare buzanci ma kalleta ina murmushi na ce.

“Nana idan kin kara jin sauki sosai za mu tafi gida can Agadez gurin danginki ko?”

Sai ta girgiza min kai.

“Aa ba zan taba zuwa ba har abada, Babana ya yi fushi da ni, na bashi kunya ba zan iya komawa garin nan ba har abada, sai dai ke kije idan na mutu”

Ban sake cewa komai ba ganin hawaye a idonta, tabbas ba dadi ne ya saka ta baro garin ba, wata kila wanin abun ta aikata ko kuwa korarta yai oho.Da rana Amina ta kawo mana abincin rana jalof din taliya da kifi an saka mata koren wake da wasu abubuwan da na zan iya tantance su ba, sai kamshi take mai ya kwanta gwanin sha'awa. Bayan mun gama ci na shiga bandakin nai wanka daman Nana tun da ta gama karyawa safe tai nata, ina fitowa na dauki rigar dazun na saka n zauna kaina babu dankwali daman na fi sakewa a haka. Can da la'asar sai ga Amina ta sake dawowa, wai na fito ana kirana ban saka komai ba na fito daga ni sai doguwar rigar jikina na biyo bayanta na yi zaton Momy ce take kirana sai na ga wani mutum cikin shiga ta kamala zaune a amman wata kujera hannunsa rike da wata katuwar waya.

“Zauna nan”

Na zauna a empty chair da Amina ta nuna min sai ta wuce ciki, ni kuma na gaishe da mutumun ya amsa min da fuskar far'a, ya soma tambaya inda na tsaya a karatuna na boko daga nan na gane cewar malamin boko ne.

“Aji hudu na tsaya a yakubu mu'azu, ban sake yi ba”

“Kin iya karanta hausa?”

“Eh na iya karanta hausa ko wace iri, da numbobi”

“Ban iya ba”

Sai ya miko min wayar hannunsa ya ce na karanta hausa. Gata ne a rubuce a take na soma karanta ta sai dai ina yi ina gargada wani gurin kuma sai ya gyara min idan na fadi wani abun ba daidai ba sai yayi ta min dariya, bayan na gama ya bani turanci ya ce na karanta sai na kafaranta da hausa ba tare da san ma'anarsa ko fassararsa ba, nan ma ya sha dariyata ni kaina na yi dariyar kaina domin duk turancin da ya nuna min da hausa na ke karanta shi. Muna cikin haka Aliyu ya fito tare da Momy ashe wai yana cikin gidan ni ban ma sani ba. Mutumen ya shiga masa bayani

“Ba laifi tana da kai kuma ta yi kokari sosai, yanzu hausar ce za a dora ta akai sai kuma turancin da zamu fara daga farko domin shi tace bata iya komai a ciki ba”

“To yayi kyau”

Ya fada fuskarsa ba yabo ba fallasa, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin da ban san ko nawa ba ne ya mikawa mutumen.

“Ga wannan ka hau mota za mu neme ka?”

Karba yai yana godiya ya karbi wayarsa da ke hanuna yai min sallama ni da Momy fuskarsa da murmushi ya nufi gate.

“Be yi ba ba ne?”

Bayan ya wuce Momy ta tambaya.

“No na cika sakewa bana son namiji mai sakewa da mace sosai”

Ya fada yana kallona.

“Ba na ce ki daina fitowa haka ba?”

“To ai hijab din ya yi datti duka kayan sun yi datti”

“Je ki sako Hijab dinki”

“To ba ya wuce ba?”

Na fada ina turo baki. Harara ta yai sai Momy ta ce.

“Ataa yata idan Aliyu ya ce ki yi abu ki rika yi ki daina masa garda kin ji? Je ki saka wata kila rakiyarsa za ki yi”

“Tau”

Tashi nai naje na saka hijab din na dawo, ko da na dawo yana cikin mota ya bude front seat da alama ni yake jira, shiga nai na zauna da gangan na ki rufe motar sai ta ya mika hannunsa ya janyo ganbun ya rufe sannan ya soka taka motar daman tuni aka bude masa gate.Ba mu yi wata lafiya mai nisa ba, muka iso gaban wata katuwar makarantar islamiya, wani irin dadi ne ya lullube na kalleshi da sauri.

“Saka ni za ka yi?”

Sai yai min banza kamar be san da zama a cikin motar ba, ya bude motar ya nufi wani bangare na makarantar ya bar a ciki, be dade ba ya dawo ya bude min murmushi motar da kansa na fito na tsaya a kusa da shi ya wani hade rai irin kar na ga damarsa din nan, wani malamin ne ya zo ta takardu ya ya tambayi sunana da sunan Baba lafiya ta da sauransu sai ya rubuta a form din hannunsa dabya bukaci number waya sai Aliyu ya bada tasa.

“Shikenan yanzu sai uniform za a siya mata da kuma hotonta da za a laka a jiki”

“Ana siyar da uniform din a nan”

“Akwai muma siyarwa dinkaken ma ne”

Be tambayi nawa ba yake ba kawai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin masu dan dama ya mikawa mutumen.

“A bata uniform din ka rike canjin ka cire kudin form din hoto kuma za muje ayi yanzu, dan Allah ka saka ido akanta bata iya komai ba, tun daga farkon fari za a fara koya mata komai”

“In-Sha-Allah ba ka da matsala, ba ri a dauko mata uniform din”

Komawa yai cikin makarantar ya dauko uniform din cikin wata farar leda ya miko min na karba ina wani irin murna kamar na zuba ruwa a kasa na sha. Sannan na koma cikin motar shi ma Aliyu ya zagayo ya shigo yayi mata key.

“Na gode na gode sosai Allah ya saka maka da alheri”
Chapter 82 · 0% Book details