← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 143

Sashe 36

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

He keep himself busy these days saboda shirye shiryen da suke na zuwa Abuja ya san akwai aikin kamfaninsa yana jiransa, kamar yadda ya saba and Rahma ta masa complain cewar tana on ganin likita idan sun koma Abuja saboda matsalar haihuwarta. Da kanshi ya dauke ta suka je sukai Momynsa da Daddynsa sallama sannan naje gidansu Rahma suma sukai musu bankwana, domin tafiyarsu gobe ne. Farinciki gurin Rahma ba a magana tana ganin da zarar sun koma Abuja komai na damuwarta ya wuce, sun bar garin da Ataa take hakan zai saka hankalinta ya kwanta gashi kuma ta jin cewar idan ta je ga babban Likita kamar Doc Perry matsalar haihuwarta zata gushe, duk da acan din ma tana fargabar Mama Fulani saboda zancen haihuwa da take mata gashi kamar bata san Allah ne yake komai ba.

ATAA POV.

Ina ta gudu yana biye da ni a baya har na nufi garejin na boya sai kuma na wuce falon Mama Fulani a tunani ba zai iya biyo ni ya shigo ba, amman ga mamaki na sai ya biyoni har cikin Falon, mamaki ya hana ni cewa komai sai bin sada nai da iso, shi kuma yana ta murmushi kamar daman can mun saba irin wannan wasan da shi, zaunawa yai saman sofa yana maida bindigarsa aljihu.

“Ba ruwana idan suka zo suka maka fada”

“Ba za su min ba, sai dai ke su yi miki ke da kika kawo ni”

Ban sake wata maganar ba, gabana sai faduwa yake gudun kar Mama Fulani ta fito ta ganshi, gashi ban san mi zan ce mata ba, ban gama tunanin abunda zan yi ba sai ga Mama Fulani ta fito daga dakinta sanye da doguwar riga da alama wanka tai ta canja tufafi. A take hantar cikina ta kada tsoro duk ya bi ya cika min ciki, tana sauko ya mike tsaye a mamakina sai ganin nai ta sakar masa fuska tana masa murmushi.

“Kamal ne?”

“Ni ne Mama ya gida?”

“To ba dai Aliyu ya zo ba balle na ce, na san sai idan yana nan kake shigowa gidan nan”

Murmushi yai ya shafa kansa.

“Kawai dai yau na ce bari na zo na gaishe ki”

“Ato ka kyauta gaskiya, ka yi abun kai, ina Hajiya Uwani?”

“Tana nan lafiya kalau”

“Ke shiga kitchen ki dauko masa cup ki bude freezer ki dauko masa lemu”

Mama Fulani ta fada min, sai na juya da sauri na nufi kitchen din, ina shiga na duba inda kofuna suke na dauko tare da lemun na dawo falon na kawo a gabansa na dire.

“Mama ina kuka samu wannan mai aikin?”

“Wallahi wata wacce ta saba kawo mana mai aiki ta kawo ta mana ita”

“Okay ni kan na ce ban san da zamanta a gidan nan ba”

“Bata dade da zuwa ba”

“Okay”

Ya fada yana mikewa tsaye ba tare daya sha lemun ba yai mata sallama ya fice yana ta kallona kamar zai yi magana sai kuma be ce komai ba har ya fice.

“Zo ki dauki kayan nan ki maida su kitchen”

Mama Fulani ta fada tana daure fuska. Kamar daman umarni na ke jira sai na nufi lemun na dauka na kai kitchen na aje sannan na fito na dawo falon na zauna inda na sabawa kaina da zama na kurawa tv ido. Misalin sha biyu na rana da yan mintuna Mama fulani ta fito ta shiga kitchen ta dora abincin rana, guraren karfe biyu ta kammala abincin sannan ta fada min na dauko plate dina ta zuba min abinci a ciki, sai na tashi da sauri na nufi garejin na dauko abincin safe da ban ci ba na nufi garden na siyayarda tea Wainar kuma na cinye, daman ni ba soyayiyar dankali bane dan haka na shanya shi a inda na sanya ragowar kazar nan ta dazun. Sannan na kunna fanfo na wanke plate din na dawo part dinta na kawo mata.

“Aje kasa”

Sai na risina na aje da alama kyamata take da har ba zata iya rika plate din ba, debo abincin tai ta zuba min a plate sannan ta zuba min miyar bata saka min naman da ke miyar ba ta ce na dauka, ni kuma na dauka da sauri na fito balcony na zauna ina cin abincin a hankali. Ina daf da cinyewa Ya Muhseen ya shigo gidan da motarsa, inda manyan motoci suke yai parking sannan ya bude motar ya fito yana matsa remote din motar tana kara.

“Pretty nan kike cin abinci?”

“Eh sannu da zuwa”

“Yauwa”

Ya fada sannan ya shiga part din Mama Fulani be dade ba ya fito ya nufi wani bangare na gidan inda nake saka ran a can dakinsa yake, sai da na gama cin abincin na je na wanke plate din na maida shi gareji na aje sai na kwanta a gurin, ina ta tunanin yadda zan iya da zaman gidan, anya zan iya juye wulakanci irin na Mama Fulani? Amman ya zan yi tun da na riga na zo, Sai da la'asar na fito daga garejin nai alwala na koma nai sallah sai na nufi part din Ammy, tambayar ta nake son yi domin ita ce mai far'a da son mutane ba kamar Mama Fulani ba. Da sallama na shiga sai ta amsa min tana zaune kasa tana cin abincin.

“Tun dazu na ke nemanki ba ki shigo ba”

“Je kitchen ki dauko tuwon ki ga shi can kina cin tuwo da rana dai ko?”

“Eh ina ci”

Na gyada mata kai sannan na nufi kitchen din, sai na samu tuwon shimkafa da miyar yauki a rufe cikin wani plate an saka min har da man shanu, ga wasu manyan tsokoki a sama. Daukowa nai na fito sai na koma can kusa da kofar shigowa falon na zauna na soma ci, ba wani da yawa zan bi ba ni kaina na san cikina ya cika da shimkafar da Mama Fulani ta bani amman ina son tuwo sosai ga kuma manshanun da aka saka a sama da namomi ba zan iya barinsu ba. Ina cikin cin abincin wayar Ammy tai kara alamar kiranta akai, picking tai ta kara a kunne ban san mi aka ce mata ba na ji dai ta yi amsa da okay, sannan ta kalleni.

“Mamana kin iya zuba tuwo?”

“Eh na iya”

“To shiga kitchen ki samu plate ki bude fula gata can dinning ki zubawa Muhseen ki rufe sai kije ki kai masa kin ji”

Sude hannun na yi na tashi na nufi kitchen da kuzarina na dauko plate din sannan na dawo dinning na zuba nasa miya a wani plate din sannan na saka tuwon a dayan plate din na rufe na dauka na nufi part din Mama Fulani, Ya Muhseen kadai na samu a falon yana shan kankana da fork, ganina yasa shi murmushi ya mika hannu biyu ya karbi abincin.

“Yauwa thank you, ke kin ci abincin ki?”

“Shi na ke ci ka karani”

“To dauko ki zo nan ki karasa”

“Zan fi jindadi ci a can”

“Saboda Mama tana miki fada a nan ko?”

Ya fada yana bude tuwon.

“Kin ga kin fini cin abinci yanzu na ganki kina cin shimkafa yanzu kuma kina cin tuwo”

Murmushi nai har na soma jin kunya na baibayeni.

“Dauko min ruwa”

Na nufi kitchen din an bude freezer na dauko gorar ruwa da cup na kawo masa. Kamar daga sama na ji muryar Mama Fulani tana masa fada.

“Wai Muhseen baka kyamar yarinyar nan ne? Ka cika shige mata fa bana sin haka”

“Miye a jikinta?”

Banza tai masa tana jin haushin tambayar da yai mata, sai gyara tsayuwar jikar da ke hannunta take da alama fita za tai. Ni dai ban ce komai ba ina tsaye ina jin umarninsa ko zai sake bukatar wani abun ne, ban ji ya ce komai ba hakan yasa na fice na barsu ita da danta na koma part din Ammy. Da sallama na shiga kamar dazun, wannan karon kishingide na sameta tana kallo tv.

“Mamana amman ku fulani ne ko?”

Ta fada tana kallona.

“Aa ni buzuwa ce”

“Wane gari kike?”

“Sokoto”

“Tare da iyayenki kike zaune?”

“Babana ya rasu mama ce kawai”

“Allah sarki, ita ta turo ki aiki a nan kenan? Ina kika san Maman Salma ko yar'uwarku ce?”

“Aa ba mu da alaka da ita zaman unguwa ne kawai”

“Allah sarki, amman kina da kanen ko? Ke ce ta nawa gidanku?”

“Ni ce ta farko ina da kane amman ya rasu”

“Ayyah Allah ya jikanshi”

“Amin”

Daga nan bata sake magana ba har na gama cin abincin na tashi na maida plate din na wanke hannuna na dawo na zauna. Gefen kujerar muka cigaba da kallon a tare, sai ga Ya Muhseen ya shigo rike da plates bakinsa kunshe da nama ya miko min plates din.

“Kai kitchen”

Na karba da hannu biyu na nufi kitchen din na aje. Ban san abunda ya fadawa Ammy ba kallona kawai take tana dariya. Kamar yadda shi ma yake dariyar har na soma tsaguwa, ma tashi na bar musu falon na dawo gareji na zauna ina turo baki kamar an min wani abu. Tun da na dawo ban koma fita ba sai da magariba, shi ma sai da na sauke farilla sannan na fito harabar gidan na zauna ina ta kallon fitilun da suka haska gidan gwanin sha'awa. Ban tashi daga gurin ba sai da aka kira isha'i sannan na nufi garden da tsoro nai alwala na dawo garejin nai sallah ta sai na kwanta a gurin ina ta jin tsoron da ban san ta ina yake fito min ba, kamar jiya ba ni kadai na kwana ba, yau kan tsoro ya kamani sosai ko iska ya kada sai na ji kamar wani aljanine zai kama ni, da naji na kasa natsuwa da gurin ne na taso na koma Part din Ammy na zauna, ina ta kallon Anty Zee Inteesar da ke cin abinci a plate daya.

“Shiga kitchen ki dauko na ki”
Chapter 36 · 0% Book details