← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 143

Sashe 113

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta hannu yai min alama da na wuce sai ya bi bayana, har muka shiga dakin saman gado na haye abuna sai ya dauko filo ya dora min a gurin kafafuwana sukai sama.

“Sannu”

Ya fada yana taba kaina.

“Na gode”

Na fada ina kallonsa da fafaren idanuwana.

“Amman Babyna da gaske mahaifin Mama ne? Hakan na nufin kakanki ne kenan?”

Na gyada kai. Mamaki ne karara a fuskarsa kamar zai sake tambayata sai kuma yai shiru ya zauna gefen gadon kusa da ni.

“Akwai abubuwan mamaki a wannan maganar ta ki, amman lafiyarki ta fi muhimmancin a gareni, runtse idonki ki ja numfashi da karfi ki sauke a hankali ki saki tunaninki za ki samu bachi yanzu nan”

Yadda ya fada min haka nai a take kuwa bachi yai gaba da ni daman bachin ne a ido na.

ALIYU POV.

yana ganin ta yi bachi ya taso ta baro mata dakin tare da jan kofar a hankali ya kulle, part din Mama Fulani ya dawo a inda ya same ta cikin falon ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana ganinsa sai tai saurin zaunawa tana kallo kofa ko zata ga Ataa ta shigo, da ta bata shigo ba sai tai kasa da murya kar wani ya ji kamar ba daga ita sai shi ne a falon ba.

“Aliyu na ce wai ita wannan Ataa daga ina take? Na ga ta rike kafafuwan sarkin Agadaz tana kuka suna buranci, na ce ko ta masa aiki ne a can kamin su dawo nan da zama?”

“Aa ta fada min cewar kakanta ne shine ya haifi mahaifiyarta”

Mama Fulani ta daki kirji tana zaro ido.

“Kakanta? Kaka kaka kaka fa? Kakanta fa? Ai idan mai fada ba shi da hankali mai ji yana da shi”

“Amman Mama Ayusher ba zata min karya ba”

“To ni kuma sai na yarda tunda gani fulanin mahaukata ko? Yarinya yar titi yar bara rana daya zata ce ita jikar wannan mutumen ce sai kuma sai na yarda ko? Jikarsa zata zo ta mana aiki? Har tai bara? Na yarda dai ta masa aiki a can Masautarsu, oh na ma tuna ina jin babarta baiwa ce su bayin Masautar ne”

“Wata kila kuma da gaske take yi Mama, tun da har kika ga ya kyaleta kuma ya aiko a kira ai kin san yana da alaka da ita, kuma bana zaton Ayusher zata karya, wata kila wata kaddararce ta saka suka tsinci kansu a cikin wannan halin rayuwar”

“Uhm Aliyu baka da wayo wallahi taya za 'ayi tana jikar sarki ta zauna a nan ko tai bara? Ai da kowa sai ya jiya, kuma ko dukansu yake kullum sai sun zauna a inda yake, yanzu ma ina ga aiki suka masa ko kuma bayin masarautar ne shiyasa lokacin da ta ji sunansa hankalinta ya tashi ita dai ta ganshi”

“Ko ma minene dai za a warware shi very”

Mama Fulani taja wani dogon numfashi ta sauke tana girgiza kai.

“Kai ba haka ba ne, sam ina... Ba za zai yiyu ba”

Ta kasa yarda da abunda Aliyu ya fada mata taya ma zata yarda wai wata Ataa jinin wannan sarkin ce. Sai dai wani abun amman bata yarda ba, Aliyu ya mike tsaye ya nufi kitchen kenan sai ga Abbah ya shigo yana gyara babbar rigarsa.

“Hajiya Fulani za mu je sokoto yanzu nan”

“Sokoto kuma? Gurin me?”

“Mai Martaba ya ce aje a dauko masa mahaifiyar Ataa, da jirginsa da ya zo da shi za a aje kin ga ko tunda gida ne ai da ni za a aje”

“Mahaifiyar Ataaa?”

Ta fada tana dukan kirjinta har da wani kashe ido take.

“Mahaifiyar Ataa fa kace Alhaji?”

“Eh ita fa kin san tana gidan Momy”

“To ina jin wata babbar sata suka masa lokacin da sukai zama gidansa, ina lokacin da suke bayinsa sun masa wata katuwar sata ko kuma hasara, shiyasa Ataa take kuka tana rike kafafuwansa so take ya yafe musu”

Mama Fulani ta fada tana gyada kai.

“Amman abunda shi jikan nasa da suka zo tare yake fada mana wai Mahaifiyar Ataa ita ce yar Mai martaba”

“Aehhhh ya fa ka ce?”

Ta tambaya da karfi tana zaro ido.

“Eh Wallahi ni kan na ce ai sun warke”

“Aa ba wani zancen warkewa ina jin dai yana nufin yarsa ta gari tun da shi sarki ai baban kowa ne, balle mutane masu nijar kasan yadda suke da junansu”

“Ko ma minene dai ai shi Mai Martaba zai fada da kansa, yanzu haka har ya wuce gidansa da ke nan yana jiranta, da ko be yi niyar zuwa gidan ba hotel ma zai sauka ni ne dai na dage ya sauka a nan ashe kin ga abo ne,sai muj dawo”

Abbah na fadar hakan ya juya ya fice da sauri. Mama Fulani ta rumfume hannayenta a kirji sai girgiza kai take.

“Aa ina ai ba zai yayu ba sam”

Duk abunda suke Aliyu na jikin kofar kitchen din rike da ruwa yana sha, shi kanshi mamakin abun yake ya san Ataa ba zata masa karya ba, kuma yadda ya ga Sarki ya nuna mata kukarwarsa ya san dole akwai alaka mai karfi a tsakaninsu, gashi kuma yanzu har ya ce aje a taho masa da ita, sai dai be san taya ta bar gidansu ba mi ya faru har suka tsinci kansu a cikin wannan rayuwar.

Gaba daya Mama Fulani kasa sukuni tai zuciyara na son yarda kuma tana jin yarda idan ta duba wasu abubuwan da suka faru, abun na ta cinta kamin su Abbah su kai har ta kira Momy ta labarta mata abunda ya faru, ita ma kanta Momy ba karamin mamaki tai ba jin abun kai tsaye kamar daga sama a take mamaki ya cika ta. Bayan ta gama da Momy kuma ta koma tana tatauna maganar da su Maryam da Rukaiya Maryam ce tai saurin yarda yayinda Rukaiyah kuma ta tsaya kwankwato.

“Idan kuma da gaske ne fa Mama? Kina ganin da ba jikarsa ba ce zai kyaleta ta rike masa kafa kuma tai ta masa kuka haka har kuma ya ce a aje a dauko masa mamanta? Gaskiya ina ganin gaskiya ne”

“Ai sarakuna suna da wannan karancin, kin san ai wasu suka rika kafafuwan manyan mutane saboda neman gafara ko kuma tubarraki, amman ba gaskiya ba ne”

“Gaskiya ni ma ban yarda ba, ai ko da mai unguwa kake da alaka sai an ji balle kuma mutum irin wannan, ai ko kama ma ba su yi ba”

“Eh ba su da kama fa, yauwa Rukaiya ashe kin gane, ina jin dai ba yin sa ne ada can da”

Haka sukai ta tattauna maganar a tsakaninsu daga Mama Fulani har Maryam da Rukaiya da kuma Baby wacce bata ce komai ba mamaki suke suna Ala ala abun ya zama ba gaskiya ba. Aliyu kan yana ta an ya tare a bangaren Ammy yana cin abinci shi da matarsa wacce bata dade da farkawa ba.
Ya jidadin yadda ta farka zazzabi ya sauka duk kuwa da kasancewar bata sha magani ba a lokacin da zata kwanta.

ATAA POV.

Na farka da tunanin Nana a can cikin mafarkina kuma abunda ya faru dazun nai mafarki, babu komai a raina sai son ganin irin yadda Nana za tai idan ta ji cewar na hadu da Babanta ko kuma Mahaifiya ce aje a taho da ita. Ina ma ace ina can na na ga irin kukan farinciki da za tai da kuma irin rudewar da za tai. Ina cikin wannan tunanin Batula ta shigo sai nai saurarin share hawayena.

“Ya jikin”

“Na ji sauki”

Na amsa har lokacin hawaye na sauko min.

“Ya Aliyu ya ce na tashe ki ki yi sallah magariba ki ci abinci idan zazzabi be sauka ba za ku je asibiti”

Sai da tai maganar na tuna da cewar da yamma na kwanta, ashe har magariba ta yi ban sani ba, lallai na dan yi kwanan da nauyi.

“Ki fada masa na ji sauki”

Na amsa ta ina gashi na nufi bandaki da yin alwala so na ke nai sallah sannan na saka Aliyu ya kira min Momy ta bawa Nana mu yi waya, na fara yi mata wannan albishir din kamin kowa ya mata domin an san ba za a je daukarta a yau ba idan ma anje yau sai gobe za su iya ko kuma cikin dare, waya sani ma ko za su tsaya tsaya jiran jirgi kuma ace babu jirgin sannan na da wasu hours. A gagauce nai alwalar ina fitowa sai an samu Aliyu zaune a kasa Inteesar na jera mana abinci shi kuma idonsa na kaina kamar zai cinye ni.

“Ya jikinki”

“Na ji sauki, Aliyu idan mun yi sallah za ka kira nin Nana?”

“Yes amman sai mun fara cin abinci tukuna”

hijab din Zee na saka nai sallah har yai na gama na yi addu'a idon Aliyu na kaina, kamin na juyo har ya bude fular tuwon ya soma zubawa a a plate, ina juyowa ya saka spoon ya fara diban abincin ya bani, kadan kadan na ke ci saboda warin miyar nake ji daker ma na ke iya hadewa a take warin manjan ya daki hancina sai na ji kamar zan yi ama da sauri na rufe bakina na nufi bandaki, shi kuma ya taso ya biyoni ina sheka aman yana shafa bayana yana min sannu cike da tausayawa.

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Chapter 113 · 0% Book details