← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 143

Sashe 21

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin murya kuka ta fadi haka da sauki kasa-kasa. Hannu nasa na share hawaye na daga inda na hango kudin da na bata dazun na dauka na fito jiki ba kwari na je bakin titi gurin wata pharmacy, na fada masa yadda ciwon yake sai ya ba ni magani kusan dubu uku da dari bakwai na dawo jiki na rawa na balla na bata na shafawan kuma na shafa mata, sai na koma ta bayanta na rumgumeta na fashe da kuka marar sauti, ji na ke kamar ace ina wata dama zan iya nema mata lafiya ta warke ita kadai ta rage min idan ta tafi ta barni ban san halin da zan shiga ba.
Na dade rumgume da mahaifiyata sannan na saketa ta kwanta, ni kuma na goge fuskata na fito tsakar gidan ko za a samu sassaucin abinda na ke ji a zuciyata. Da na fito sai Farida ta dasa min wata sabuwar fira dama akwai da yawan magana, a nan take labarta min cewar mahaifinta ne ya ce Nana ta dawo nan ta raba ta zauna tun da mai wacan kangon gidan ya koreta gashi bata da wani gurin zama. Ni kaina nasan indai Farida ba to ko sai mahaifinta, domin mahaifiyarta ba zata taba yarda tace ta zauna a gidan ba.

Bayan sallah magariba na dauki kudi da kwano na siyawa nana tuwon masara da miyar yauki domin shine mai yar nasiha ba kamar shimkafa ba mai tsada, ko da na shigo na tarar ta samu sauki sosai tana zaune saman dankwalinta da tai sallah. Gaba na saka ta na cilasta mata cin tuwon ita kuma ta ki ta ci ala dole sai ni na fara ci, a dole sai na ci sannan ita ma ta ci na kawa mata ruwa ta sha, sannan muka gabatarda Allah isha'i muka kwanta a gurin da mutum ba zai iya mike kafafuwansa ba straight ba.

***      ***      ***
Da wuri na farka gudun kar nai lattin zuwa gurin aiki, bayan na ayi alwala ita kuma na samo mata kasa tai taimama ta yi sallah asuba, cikin kudin na dauka naje na siyo mana koko da kosai da suga na kawo muka karya sannan na shiga bandaki nai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyin safiya da be gama sauka ba.
  Bayan na fito na saka wasu tufafi, daman can shafa mai be dame ni ba bayan cikin tsarina wankan ma gudun kar suce ina wari da ba zan yi ba. Haka na shirya cikin wata kodaddiyar atamfata na sake kwaba gawayi kamar ranar na shafa a fuskata, tun da sun ce na daina saka nikab sai na saka bakin gawayin da na saba sakawa duk kuwa da irin kazantar da suke ganina da shi.
   Yau ma sai da na dauki naira dari a cikin kudin sannan na saka Hijab dina na yi ma Nana sallama na fito na shiga dakin Maman su Farida na gaishe ta ita da mijinta shi ya amsa da far'a sabanin ita da ko kallon kirki bata min ba, wata kila tana ganin kamar mun takura tane mun zauna mata a gida mun hana ta wali a yadda a gidanta.
Yau ma achaba na hau na fada masa inda zai kai ni, ba aje ni ko'ina ba sai bakin gate din gidan na mika masa kudinsa na sauka, ina kokarin yin knocked gate din sai na ga an bude shi gaba daya, ashe mai gidan ne zai fita sa na raba gefe sai da ya fice sannan na shiga ina mikawa mai gadin gaisuwa bayan ya amsa min na nufi kofar gidan wato kofar babban falon da zai sada ka da cikin gidan gaba daya. Da nai knocked din kofar sai na zauna kusa da kofar dan nasan ba yanzu zata bude min ba, haka nai ta zama a gurin har mai gidan ya dawo ya faka motarsa inda sauran motocin suke ya fito fuskarsa da Annuri da haifa ya nufo kofar ya saka keys din hannunsa ya bude.

“Ina kwana?”

Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake ta yi wata kila yana mamakin yadda yau ban saka nikab dinba na sake shafa bakin gawayi, ni dai ban kalleshi ba domin matarsa ta fada min mijinta baya son kallo. Shi ya fara shiga sannan na bi bayansa na shiga kai tsaye na nufi gurin jiya na dauko tsintsiyar da mopper na fara gyara falon sannan na shiga kitchen na gyara, ban san a wane dakin ta ke kwance bana son na shiga ta ce na mata ba dai-dai. Sai kawai na nemi gefen kujera na zauna, ina ta jiran fitowarta shiru har bachi ya dauke ni a gurin ban sani ba. Can cikin bachin nawa na ji an watso min ruwa mai dumi hakan yasa ni farkawa a firgice, ashe ruwan tea da ke hannunta ta watsa min.

“Ina kwana”

Na mika mata gaisuwa kamar a rikice.

“Ba ki yi bachi a can gidanku ba ne da za ki zo nan kina mana bachi? Ba aiki aka dauke ki ba?”

“Na gyara nan na gyara kitchen ina jiran ki fito sai na gyada dakunan”

“Miye a fuskarki kuma?”

Na yi shiru ban ce mata komai ba sai kawai ta tabe baki ta zauna a kan kujerar.

“Shiga ki gyara min bedrooms dina”

“To”

Na amsa a ladafce sannan na dauki tsitsiyar na nufi dakunan na gyara na na dawo na dauki mopping na goge ko'ina na wanke bandakunan sannan na sauko.

“Na kare”

Na fada mata bayan na maida kayan inda na daukosu. A gurin ta bar ni tsaye bata ce na tafi ba, ba ta ce na tsaya ba, har jikinta sauko hannunsa rike da agogon hannu yana kokarin sakawa.

“Kin tabbatar za ki iya driving da kanki? Idan ba za ki iya ba don't stress yourself zan turo direba ya kai ki”

Shine abunda ya fada mata, ita kuma ta girgiza masa kai.

“Aa zan iya, wannan yarinyar za ta rika min kayan”

A gabana ya kai bakinsa a goshinta ya sumbace ta babu ko kunya, shi da kiss ni da jin kunya har na ji kamar kasa ta nutse da ni da kunya. Be yi minti talatin da fita ba ta hau sama ta bar a gurin a tsaye ina ta jiran saukowarta, sai da tai wanka ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsada sannan ta sauko idonta sanye da katon bakin gilashi nan na mata.

“Shiga dakina ki dauko min ledodi ki saka mota”

Abun ka da mai jiran umarni sai nai hanzari cira kafa na taka har dakin na dauko na kai gurin motar da ta bude na zuba su a baya, sai kuma nai tsaye ina jiran abunda za ta ce min. Bayan boot din taje ta dauko wani tawul ta miko min.

“Shimfida wannan a baya sannan ki zauna karki shafa min dattin jikinki a mota”

Na saka hannu na karba cike da jin zafin furucinta, na shimfida kamar yadda ta fada sannan na zauna ita kuma ta shiga mazaunin direba tai ma motar keys, muka fita ba tare ni na san inda za mu je ba, nawa ido ne kawai ina ta kallon titi har muka isa wata kyakkyawar unguwa mai manyan gidaje, gida hudu muka wuce sannan ta danna horn mai gadin ya bude mata gate, a inda sauran motocin suke ta faka motarta ta fito sannan tace da ni na fito ya dauko mata ledodin, tana gaba ina bayanta har muka shiga cikin gidan. Alhajin nan mai kangon gidan da ya kore mu na hango zaune kan kujera yana dariya an zagaye shi suna ta hayaniya da alama wata wainar ake toyawa.

“Daddy... Happy birthday”

Hajiyar ta fada tana nufar inda yake, ban yi mamakin wulakancinta ba indai har wacan mutumen marar ganin tausayi ne mahaifinta
*Z A K I*

By Khadeeja Candy

1️⃣3️⃣

A gidan ta wuni ita da mahaifinta da sauran yan'uwanta suna ta tayashi murnar birthday kowa na kalla fuskarsa dauke da farinciki,kamar wadanda aka yayewa damuwa har abada. Sai da yamma mahaifinta ya fita ya barsu a cikin gidan suna ta shagalinsu. Duk iya shagalin da akai da ciye ciye da akai Ataa na waje zaune ita kada kamar yadda Rahma ta umarce da zama waje, sai misalin sha daya na dare ta fito cikin gidan baya ta yi waya da Aliyu ta fada masa ba zata iya driving ba ya zo ya dauke ta.
  Ko da ta fito Rahma na kwance a balcony, matsawa tai ya saka fada ta dan musgune ta kadan ita kuma ta farka a girgice sannan sai ta jefa mata dari biyu

“Tashi ki je gidanku”

“To”

Ta fada tare da saka hannun ta dauki kudin ta gyara Hijab dinta ta kama hanya. A gurin Rahma tai tsaye har Aliyu ya iso da motarsa harabar gidan ya faka. Sannan na soma takawa a hankali ta karaso inda yake, fito yai daga cikin motar ya bude mata front seat ta shiga ta zauna ya rufe ya koma cikin motar yai nata key ya danna horn aka bude musu gate.
Lokacin daya hau titi ya fara tafiya sai ta kwanto jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa yana taba kanta da yake ji da zafi.

“Kina jin rashin lafiya ne?”

“Eh”

“Since when?”

Ya faka motarsa gafen titi ya juyo yan fuskantar da kyau.

“Dear miyasa kike wasa da lafiyarki ne? Ba ki san lafiyar ki tana da amfani a gurina ba? Tun yaushe kika so ma jin zazzabi”

“Da yamma nan, yanzu ne ya fi min sosai”

Wayarsa ya ciro ya kira Doc Asim bugu biyu ya dauka.

“Doc same ni gida yanzu, jikin Rahma ya tashi”
Chapter 21 · 0% Book details