← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 143

Sashe 63

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba ko dai za mu yi, kuma idan Allah ya min yadda na ke so ya kamu da son daya daga cikinku”

Ta fada tana fita daga dakin zuwa dakin Rukaiyah domin tashinta.

ATAA POV.

Sam bana jin dadin ganina Aliyu a yanzu, saboda jin kai da yake fama da shi ga uban nuna isa da yake yi kamar shi ya fi kowa a duniyar nan. Wato shi ba zai iya cewa ya jikin Nana ba, ba kuma zai iya shigowa da sallama ba, sai amsawa mutane magana tsaitsaye da gadara. Abincin daya kawo ma kin ci nai saboda shi ya riko dan haka ni ba zan ma ci abincin daya kawo ba. Sai kawai na zuba na rana da Momy ta kawo mana na sake cinsa sannan nai sallah isha'i na kwanta.
Ba laifi yau na tashi raina da dan sakewa saboda Nana ta gane ni kuma ta samu bachi mai kyau da allura da Doc nan yai mata jiya domin har yanzu bata farka ba. Duk kuwa da zuciya ta bata aminta da shi sosai ba saboda gudun abunda ya faru ya sake faruwa, sai idan na tuna abunda Allah ua kaddarawa bawa babu mahani sai na kwantar da hankali domin ko dauke Nana nai ban san inda zan kaita ba daga nan, ba ni da kudin magani kuma ban san wanda zai taimaka mana ba, idan ban yarda da Aliyu ba ina kokarin yarda da Momy saboda yanayin da na gani a fuskarta kamar ba zata iya cutar da wani ba.
  Misalin takwas da wasu yan mituna Husna da Amina suka shigo suka kawo mana abun karyawa, ina cikin amsa ya mai jikin da suka min Nana ta farka wani abun mamaki sai ta tashi zaune da kanta sai dai fuskarta ta dan kumbura kadan, a nan suka shiga gaisheta suna mata ya jiki ta amsa musu da hausar ta da bata fitowa sosai, sannan suka min sallama suka tafi ba laifi sukan suna da son mutane babu nuna kyama ba kamar su Maryam da Rukaiya ba. Toilet na shiga na dauko karamin bokiti da ruwa a kofi na kawo na wanke ma Nana baki da kaina sannan na zuba tea din da Momy ta aiko mana na bata ta sha sannan na rika ta sauko daga kan gadon ta shiga bandakin da taimakona tai alwala muka fito ina rike da ita na saka mata hijabina tai sallah daga zaune.

Bayan ta gama ta koma saman gadon ta kwanta, wani likita ne ya shigo ya dubata ba wacan na jiya mai far'a da son mutane ba, wannan fukarsa a daure take, tsabanin wacan daya sake min fuska ya tambayi sunana da garinmu har ya dauko laptop dinsa ya nuna min rawar yan garinmu. Bayan fitar Doc din wata nurse ta shigo ta bata magani sannan ta fita sai a lokacin ni kuma na zuba abincin ina ci ina amsawa Nana tambayar da take min wai yaushe na dawo.

“Tun shekaranjiya, amman baki sani ba”

“Bana iya gane komai, na sha wahala sosai bayan tafiyarki Ataa babu mai kula da ni ga yunwa tun ina iya tashi har kai bana iyawa idan na tashi sai na fadi, na yi ta cewa Farida ta kira Maman Salma ta fada miki cewar ki dawo ki kula da ni kamin na mutu amman bata kira ba”

Da yaren buzanci take fada min wannan maganar, ban san lokacin da idona ya cika da hawaye ba na aje abincin da nake ci ina kallonta na ce.

“Ai yanzu ba zan sake tafiya na barki ba Nana”

“Bana son ki sake tafiya ki bar a nan, da ki je neman kudin maganina ki bar ni mutu a wulakance kara ki tsaya kusa da ni a haka na mutu a suturce, kar ki bari na zama ta farko a tsatson sarautar mu da za tai mutuwar wulakanci”

“Allah ya raba mu da mutuwar wulakanci Nana ba zan sake barinki ba In-Sha-Allah”

Na fada ina share mata hawayenta, sannan na zauna kusa da ita ina dauko mata labarin Abuja sai dai ban yarda na fada mata zancen korata kai ba, cewa nai dawowa nai na ban tsaya na karbi kudin aikina ba domin da sunan ganin gida na zo.

“Ki bar musu kudin can ba zaki koma ba, waya kawo ni asibiti?”

“Wata Hajiya ce ta taimaka mana”

Haka ta fada min ni kuma nai murmushi ina tuna Kamal ko ina yake a yanzu oho. Misalin sha biyu Muhseen ya shigo dakin da muke fuskarsa da murmushi kamar yadda ya saba, ina ganinsa dadi ya lullube ni na hau murna domin na san shi ne likitan da zai mata aikin kuma na san shi ba mugu ba ne kamar Doc Asim ko da yake ba a fuska abun yake ba.

“Pretty Pretty”

Ya fada yana min dariya sai nima nai masa murmushi.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa ya jikin Mamanmu?”

“Da sauki”

Ya karasa kusa da ita ya rika hannunta ya sumbace shi sannan yai mata sannu.

“Sannu Mamana Allah ya baki lafiya”

“Amin na gode”

Sannan ya nufi files din da suke nan yana dubawa sai ya fita da su, bayan wani lokaci ya sake lokowa ya kira ni, sai na tashi na fita na same shi tsaye jikin kofar.

“Pretty ya kin yi missing dina?”

Na yi kasa da kaina shi kuma sai kallon kirjina yake da fuskata kasancewar babu Hijab a jiki.

“Wani abun nake son na tambaye ki, miyasa kika bari Mahaifiyarki ta siyar da kodarta?”

A take fuska ta canja.

“Ba siyar tai ba, likitan nan ne ya cuce mu ya cire mata”

“To gaskiya ya cutar da ku, domin aikin nan da za a mata akwai yiyuwar bayan aikin ta iya manta wani bangare na rayuwarta ko ma gaba daya zuwa wani lokaci saboda abun ya taba kwalkwalwarta”

“Wani abun zai sake samunta kuma?”

Na tambaya hankali a tashe.

“No zata samu lafiya amman akwai yiyiwar hakan ya faru shiyasa na fada miki haka tun yanzu, gaskiya likitan nan da Aliyu sun cutar da ku, ko da yake Aliyu ya ce siya yai amman gaya zaka siye abu kamar wannan koda fa guda ace baka mai shi ba kuma har ka yarda kai amfani da ita”

Hawaye ne ya fara sauko min sai ya miko min wata takardar da pen ya ce na saka hannu.

“Ki kwantar da hankalinki wannan na dan lokaci ne amman zata samu lafiya, saka mim hannu zan mata tiyata”

“Muhseen na baka amanar mahaifiyata dan Allah karka cutar da ita”

Na fada bayan an saka hannun a inda ya nuna min na mika masa. Sai ya kai dayan hannunsa ya shafa kaina tare da yanjo tsoron dake bayana ya dawo da shi gaba.

“Ba zan mata komai ba, ba kowa ne kamar Aliyu ba, bari naje na saka kayan theater amman ki min alkawari ba za ki yi kuka ba?”

Na gyada kai ina hawaye.

“Good girl”

Ya fada sannan ya wuce ni kuma na resina a gurin ina kuka. Wasu nurses ne suka zo da kujera suka dora Nana akai suka fito da ita daga dakin ni kuma nai saurin share hawayena gudun kar na sakata a damuwa.

#Team Muhseen
#Team Aliyu
#Kamal
#Team Rahma
#Ataa

Wane Team ya fi yawa?.🤔
Ni dai Ina Team Rahma kishi gaskiya ne 🙄😏

*ZAKI

By Khadeeja Candy

31...

Kiran sallah asuba ne ya farkar da shi daga bachinsa da yake, kasancewar karar loudspeaker masallacin ta shigo sosai har cikin dakinsu saboda daukewar wutar nepa da akai misalin uku da rabi na dare. Sake maida idon yai ya lumshe ya saka hannuna na dama ya murza saman fatar idon sannan ya sake budewa ya kalli Rahma dake kwance kirjinsa tana sharar bachinta a hankali. Dagata ya fara yi daga jikinsa sannan na sauko da kafafunsa kasa ya zauna bakin gadon ya dafe kansa ya farka da Ataa a ransa kamar yadda mafarkinsa ma ita ce a ciki, ajiyar zuciya ya sauke sau biyu sannan ya unkura ya tashi jikinsa ba tufafi ya shiga bandaki, wanka ya fara yi kamin alwala sannan ya dauro tawul ya fito ya nufi wardrobe ya dauko karamin jean ya saka ya dora Jallabiya a sama sannan ya dauko kasa ya nufi masallaci. Bayan ya sauke farilla da addu'o'i ya dawo gida yana tafe a hanya yana tasbihi da hannunsa har ya iso, yana kokarin hawa stairs mai gadinsa ya kunna sola gidan ya gaske gaba daya, dakinsa ya shiga ya zauna bakin gadon tare da kai hannunsa yana tashin Rahma a hankali.“Dear tashi ki yi sallah”

Daker ta motsa saboda bachin dake cikin idonta domin jiya bata samu bachi da wuri ba daga ita har Aliyu da nuna mata yadda yai maramarinta a tsakanin kwanakin nan. Sai ya tabbarar ta farka sannan ya dauki qur'anensa ya sauko downstairs ya zauna a saman kujera ya bude yana karantawa. Yayi one hour ya a karatun sannan ya hau ya maida qur'anen a nan ya samu Rahma ta koma bachi sanye da Hijab din da tai sallah, Bedsheet yaja ya lulluba mata saman jiki sannan ya sauko ya shiga kitchen, daman idan suna sokoto shi yake shi ke hada musu breakfast ba kamar Abuja ba da mai aiki yake musu. Ruwan Lipton ya fara dorawa sannan ya fasa kwai ya ya kada ya je ya firaye dankalin ya zuba mai ya soma soyawa, da kansa ya share kitchen din bayan gama komai ya zuba a abun zuba shara sannan ya dauko kayan ya kawo dinning. Ya kunna tv ya zauna a gurin yana kallon news baya son ya tashi Rahma a yanzu domin yasan bata saba farkawa da 9 ba sai 10 balle yanzu da yasan ciwon nata yafi na da yafi son ta huta iya hutawa har bachi ya gintse ta.
  Yana zaune a falon har 11 Rahma bata farka ba, tana can tana bachin dadi shi kuma yana zaune yana labartawa Nasir abunda ya faru a waya.“Aliyu idan ka nuna Muhseen damuwarka idan yai maka abu, domin idan ya lura kana jin haushi zai yi ta jindadi ne yana ta bata maka rai wanda hakan zai kara bata zumuncinku ne kawai”
Chapter 63 · 0% Book details