← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 143

Sashe 71

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ina miki fatar alheri ina fatar yanzu ma kije ki samu mahaifiyarki ta farka, kuma ina miki bankwana zan wuce Abuja yau, zan dawo satin sama amman lallai ne idan na dawo yin aikin na biyo ta nan ba, maybe ki ganni nan kusa maybe kuma sai nesa ina mik fatar alheri”

Dagowa nai na kalleshi sai ya sakar min murmushi ya nufi kofar fita daga falon ya bar ni tsaye ina juyo na kalleshi.

“Aisha”

Kiran Momy na yasa na fito daga falon na same ta gurin mota, a front seat na shiga ita kuma ta zauna a mazaunin direba tai ma motar key aka bude mana gate muka kama hanyar asibitin.Ban san dalilin rashin jindadin kalaman Muhseen ba, yanayinsa da yadda yake min maganar ba cikin farinciki ba ne, and i feel like kamar ba zai sake dawowa ba, wata kila wani abun Momy da Aliyu suka ce masa shiyasa ya yanke wannan hukuncin, wata kila kuma ra'ayin kansa ne ban sani ba amman sam kalamansa ba su min dadi ba. Bayan Momy ta yi parking motar ya na bude na fita ita ta bude ta fito sannan ta fito da kayan na rika wasu ta rika wasu muka nufi cikin asibitin, kusan mutane duk wadanda nake cin karo da su babu mai kallo ďaya mazan dai duk wanda ya kalleni sai ya sake kallona wasu har da sakar min murmushi suke. Ni dai in biye da Momy har muka isa cikin dakin da Nana take, Doc Bukar muka samu a ciki da Laraba Doc Bukar na duba Nana wacce ki kwance idonta bude tana kallon mutane, Momy ce ta karasa cikin yayinda ni na tsaya bakin kofa ina kallonta na kasa karasawa tsoro na ke kar na je kusa da ita tace min bata gane ni ba, Doc Bukar na ta sakar min murmushi ni kuma idona na kan Nana har na fara hawaye.

“Karaso mana Ataa”

Cewar Doc Bukar daker na iya daga kafana na fara takawa cikin dakin, karar sautin takalmin kafata ne yasa Nana ta kalli inda na ke wani abun mamaki sai na ga ta sakar min murmushi, dadi na ji da sauri na karasa kusa da ita ina ta kallonta kamar zan cinye ta.

“Nana”

“Na'am Ataa”

Mantawa nai da tiyata ce a jikinta ya rumgume ta ina kukan dadi, bata manta ni ba ko da ta manta komai ni bata manta ni ba, sai da Momy ta dago ni tana dariya ta ce.

“Karki ji mata mana yi a hankali”

Na kalli Doc Bukar ina hawayen farinciki na ce.

“Doc bata manta ni ba”

“Bata manta komai ba sai dai ki yi mata fatan samun lafiya”

“Al-hamdulillah Allah mun gode maka”

Na fada ina daga hannuna sama, dadin da make ji a yanzu ba zan iya misalta shi ba, duk wanda ya kalleni ya san ina cikin farinciki a wannan lokacin, ba ni da wani buri face samun lafiyar Nana da alama muka yanzu ta doro hanyar samun.Kasa cin abinci safen mai saboda murna sai an nemi yunwa na rasa, Ita kuma Momy ta hada mata tea ta bata da kanta a hankali tana sha har ta sha ya isheta.

“Na gode Momy Allah ya saka muku da alheri”

Murmushi tai ta aje kofin tana fadin.

“Ba komai ai yi wa kaine”

Ta dade a asibitin sannan ta fita ita da Laraba wai zata je gida tai wanka ta gyara ta dawo. Aka bar ni asibitin ni da Nana ina kula da ita, cikin muryarta na marasa lafiya take tambayata.

“ataa ina kika samo mutanen nan? Suna da kirki sosai”

“Wannan matar dan ta ne ya taimaka mana, daga gidan da nai aiki a abuja ya biyo ni zuwa nan na fada masa matsalata da kuma dalilin aikin da nake a can gidansu an Abuja shine ya fadawa Mahaifiyarsa sai suka taimaka mana suka kawo ki asibiti ya biya kudin aikinki kuma jinin da aka saka miki jiya ma ance shi ya bada jinin, kuma yanzu haka a gidansu nake zaune su suka ba ni wannan tufafin ma”

“Allah dai yana da kirki sosai Allah ya saka masa da alheri shi da babarsa, bayan Doc Asim mun sake haduwa da wani mutum mai taimako”

Na yi shiru ban ce komai ba, domin Doc Asim ko sunansa ba na son a ambata.

ALIYU POV.

Daga masallacin da yai sallah ya wuce gurin Momy, duka kanensa suna zaune tsakar falon suna cin abinci a plate daya, a tare suke gaishe shi ya amsa musu da dan sakin fuska sai dai ba Sosai ba ya nufi dakin mahaifiyarsa. Zaune ya same ta gaban madubi tana shafa mai a jikinta, juyo tai ta karba masa sallamar da yai tana kallonsa.“Wa'alaikassalam”

“Momy barka da rana”

“Yauwa, ka je asibitin kuwa?”

“No yanzu da na ke son na leka, ban sani ba ko wa a wuce da wani abu shiyasa na biyo”

“Yau Ataa tana cikin farinciki”

Ya kalli Momy da mamakin farincikin nata, Momy bata jira ya tambaye ta ba ta ce.

“Mamanta ta farka kuma bata manta komai ba”

“Wow”

Ya fada yana murmushi.

“Har tea na bata ta sha, yau Ataa har da min godiya”

Ya dada fadada murmushinsa shi kansa ya jidadin jin hakan balle kuma da aka ce masa Ataa tana farinciki, ya gyara zamansa yana kallon Momy ya ce.

“Ban sani ba ko idan na fada miki wani abu za ki yarda”

“Minene?”

“Jiya lokacin da kai abincin dare na samu Ataa bata nan har na kawo Husna na koma bata dawo ba, na tambayi Laraba tace min bata san inda take ba, sai na hankali ya tashi na zata ko Muhseen ya fita da ita ko kuma Doc Bukar domin shi ma kamar yana dan rawar kafa akanta, amman na fara zuwa gidan da na dauko ta na fara dubawa ko taje daukar wani abun kamin na kirasu, sai na same ta tana bachi bakin kofar dakin na kwano, na ji tsoron tashin ta saboda kar ta min masifa so i decided nai gadinta saboda ina jin kamar idan na barta a nan wani zai iya zuwa ya yaga mutuncinta, da daman na mota ya ishe ni sai na fito gurin kwanon na zauna a kasa na jingina....”

Yayi shiru na wani lokaci kaminnya cigaba.“For the first time Momy jiya na zauna akan turda, na ji wani yanayi na dabam da ban taba ji ba, gurin babu ac babu katifa, sai hasken farin wata, garin yayi tsif kamar ba bu mai rayuwa a duniyar nan, Momy abunda na fara tunawa da shi shine kabrina, wata rana zan kwanta kamar haka a cikin kabarina, babu shimfida mai kyau babu gado ko katifa, babu haske sai na aikina, duk wani abun dana tara na dukiya da kawa a nan zan bar shi, zan rayu ni kadai a cikin kabarina”

Ya fada idonsa da kwalla Momy ta yi murmushi cike da kaunar danta.

“Secondly Momy na ji yadda wandada basa da shi suke ji, na taba kasa na zauna a kai i feel it bata da dadi amman a haka wasu suke kwana a samanta a haka wasu suke rayuwa a cikinta, then i realise there are billions of her da abinci kawai suke nema da muhalli, not like thousands of us da idan muka ga dama ba a Nigeria kwana ba a wata kasar ne, i never thought akwai mutumen da zai iya rayuwa a irin wannan yanayin sai yanzu, i never thought there a alot of homeless people da zasu raba a gidan wani kamar haka sai yanzu, Momy na ji wani a cikina some thing differently, wani abun da ban tana tunanin jin sa ba”

Murmushi ne har yanzu a fuskar Momy.

“Shiyasa Musulunci ya koya mana taimakon marasa shi, ko abinci ka taimakawa wani da shi zaka samu lada kuma zai jidadi ya rika ganinka da kima, yatsun hannyen mu Allah yayi su dabam balle kuma.mutane, dole akwai mai arziki akwai mai talauci akwai mai tsakiyar shi ba mai arzikin ba kuma ba mai talaucin ba, sai dai abunda aka fi so, arzikin da tsarki zuciya, a lokacin da nake nuna maka kyamar talaka ba abu ne mai kyau ba, sai kake ganin kamar ban fahimta ba ne, saboda Fulani ta nuna maka wata tarbiyar ta dabam wacce ba ita na so na dora ka akai ba, talakawa mutane da ya kamata ace an rikesu an nuna musu kulawa da kauna ko da ko su din basa son ka, ka yi dan Allah shi zai baka lada, a lokacin da mutum yake cikin yunwa idan ka ka bashi abinci zai dauke babban masoyi, wanda yake kishi kuma ka shayar da shi, zai ga ba shi wani mai sonsa a duniya kamar kai, balle kuma wanda lafiya ta gagareshi ka tsaya nema masa ba zai taba mantawa da kai ba, kuma ragowar rabon yana gurin Ubangijinka, akwa su da yawa marasa mayafi lokacin sanyi marasa abincin lokacin yunwa marasa mafaka lokacin damina, abu kadam su ke son samun su yi farinciki, while kai Allah ya hada maka komai arziki ilmi lafiya hankali da komai, wani yana can shi hankali ma yake nema ya samu be samu ba, shikenan kai dan Allah ya hada maka komai sai ka ce ka fi kowa? Wata kila ma mutanen da kake rainawa sune a gaba ranar alkiyama kai kana baya a kaskance kuma shine babban talauci”

Ya kawar da fuskarsa yana sauke ajiyar zuciya maganganun Momy sun kara taba zuciyarsa ya karanta ya sani amman ya take saninsa saboda yana jin shi din wani ne, yana jin ya fi kowa kuma babu wanda ya isa da shi saboda yana kudi alhalin dukiyarsa ba komai ba ce a gurin Allah.Momy ta share hawayen da suka zubo mata tana dauko zancen Muhseen.

“Dazu Muhseen ya fada min cewar kana takura masa akan Ataa hya fada min sonta yake kuma yana son na shige masa gaba”

Aliyu ya kalleta da sauri mamaki a fuskarsa karara.

“Muhseen din ya fada miki?”

“Eh yace ya fada mata ma”

“Me kika ce masa?”
Chapter 71 · 0% Book details