← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 143

Sashe 22

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana fadar hakan ya kashe wayar ya jana motar @360 suka iso gida, ba su yi minti ashirin da isa ba sai ga Doc Asim ya iso, tana zaunen falon kusa da Aliyu ya tambayeta abunda ta ke ji ta fada masa ya bata magani, sannan Aliyu ya rika ta suka shiga bedroom ya kwantar da ita, bakin gadon ya zauna kusa da ita yana ta kallonta kamar mai auna hawa da saukar numfashinta, har bachi yai gaba da ita, sannan na taso ya fito daga dakin shi ma saboda kiran wayar da Mama Fulani tai masa ne, saukowa yai kasa yana amsa wayar. Yadda fuskarsa take sake duk kuwa da irin tashin hankalin da ke ransa na ciwon matarsa, amman ka ga murmushi a fuskarsa ka san mai kiran yana da muhimmanci gare shi.

“Aliyu ka yafe kowa ka kyale mu ko?”

“Na isa Mama? Ai ko zan yafe kowa ban da uwata matukar ina neman albarka”

“To ya gida ya matar ta ka?”

“Gida kalau surukarki kuma tana nan yau jikin ya soma tashi”

“Subhanallahi fatar dai da sauki”

“Da sauki ta samu bachi ma”

“Masha-Allah Allah kara lafiya, zan je Dubai gobe, ba lallai idan na je can na kira ka ba, fada min abunda kake son na siyo maka da matarka”

“Ni dai perfume na ke so, ita kuma ki siyo mata duk abunda kika ga ya dace”

“To shikenan, a gaishe ta idan ta tashi”

“Zata ji thank you Mama”

“Allah maka albarka”

Daga haka tai hanging. Shi kuma ya tashi cikin rashin kuzari ya nufi kitchen, tea ya hadawa kansa ya dawo saman kujera ya zauna ya kunna tv for like ten minutes ya tashi ya koma dakin matarsa.

ATAA POV.

ban taba auna rashin imani da tausayin irin na matar nan sai yau, ta ba a gidan zan kwana ba amman ta kyale ni na zauna a waje bata ba ni abinci ba na wuni da yunwa ta bar ni a haka, yanzu kuma sha dayan dare ta ce na kama hanyar gidan, gashi ko abun hawa babu, tsoro da fargabar abunda zai same ni, wa zai tare ji a hanya barayi ko masu cin zarafin mata duk be dame ta ba, saboda kawai ina nema a karkashinta, shi kenan dan ina talaka ba ni da gata, ni fa ya ce kamar kowa ba daga sama na fado ba, amman saboda ba ni da shi ina talaka a yau an sake ni karfe goma sha dayan dare na kama hanyar gida. Ban samu a abun hawa ba, a kafa nai ta takawa ina ta addu'ar Allah ya kai ni gida lafiya. Ko da na isa unguwar babu mutane sosai domin daya saura na dare. A bakin kofar gidan na tsaya nai buga kofar ba a dade ba aka bude min, babu wuta a lokacin dan haka mahaifin Farida ya haske min fuska da fitila.

“Ataa ke ce cikin daren nan? Ina kike je?”

“Gurin aikin ne, muka fita ba mu dawo ba, sai yanzu”

“Ina kuka je?”

“Gidan iyayenta”

Sai ya bude min kofar na shigo yana ta kallona kamar be yarda da ni ba, sai da na shigo cikin gidan na hango Nana tsaye rike da bango tana kallona lokacin da na karasa kusa da ita sai na rasa me zan ce mata, na sani dole hankalinta ya tashi rashin ganin na dawo, gashi babu mai mata wata hidimar sai ni. Rikata nai muka koma cikin dakin sai da ta fara zama sannan na zauna kusa da ita na fada mata dalilin dadewar da nai ban dawo ba.

“Da wani abun ya same ki a hanya fa?”

“Nana matar nan da na ke yi ma aikin yar mai kangon gidancan ne wanda ya kore mu, ina ganin gaba daya danginsu basa da mutumci ko kadan”

Na fada cikin muryar da ke Nun a gajiye na ke ga kuma yunwa da na ke ji rabon da na saka wani abu a cikina tun karin safe da na sha koko da kosai. Sama-sama mu kai fira da Nana ta nuna min rashin jindadinta na dadewar da nai a can sannan muka kwanta ni da ita.
   Yau ma kamar jiya na tashi da wuri saboda matar nan ta fada min na rika zuwa tun karfe bakwai na safe, na san idan na tsaba lokaci wani abu zai iya biyo baya, waina na siyowa Nana ta karya sannan na fito na wanke kwanon da ta ci na maida na janyo ruwan rijiya na yi wanka na saka doguwar rigata ta atamfata kodaddiya, ban damu da saka dankwali ba, na fita waje na daddaka bakin gawayin na shafa a fuskata, na saka Hijab dina na fito na leda dakin Maman su Farida na gaisheta sannan na saki labulen dakin har na kama hanyar fita sai ga Farida ta fito sanye da uniform din makaranta tana cewa na tsaya mata.

“Har kin shirya zuwa aikin tun da safe haka?”

“Wallahi matar da na ke aiki gidan ta ne bata da mutunci ko kadan, tace na rika zuwa bakwai kin ga idan na tsaba zata iya korata gaba daya”

“Gaskiya kan bata da mutunci, tun da har zata rike ki ki kai karfe daya na dare sannan ki dawo, ni wallahi da za ki biye ni da kin yarda maman Salma ta sama miki aiki a Abuja, acan take samawa mutane kuma Wallahi albashi mai tsoka”

“Kai anya Farida zan iya zuwa har Abuja? Kin ga Nana ai bata da wanda zai kula da ita sai ni”

“Amman ai dan neman lafiyarta da abincin ta za ki yi, kuma idan ya wadace ku ya kamata ki dauke ta kuje har garinku ki nemi danginku, zama a nan babu kowa a tare da ku ba zai amfana muku komai ba”

“Nima ina tunanin haka, amman na fi son sai Nana ta samu lafiya tukuna”

“Allah ya bata lafiya, nawa ne suka dauke ki aikin?”

“8k ne”

“8k mi zai miki? Ai wannan kudin zai iya karewa a abinci kawai, gaskiya kara ma Abuja nan ance can fa irin manyan gidajen nan har 30k 50k ana bawa mutum, kin ga da kin hada na wata uku ai ya isashe ki”

“Da gaske Farida”

Na tambaya cike da kwadayin tabbatar da zancen nata.

“Wallahi haka Maman Salma ta ce min”

“Ai ba zuwan ba, kin ga dama ace Lukman yana da rai dazan samu sauki wanda zai kula min da Nana amman yanzu bata da kowa ai sai ni, ita kanta ba zata yarda na tafi ba”

“Gaskiya haka ne, amman indai ina nan ni kaina ai zan iya kula da Nana kin sani, ko da ba zan cire mata kewarki ba zan rage mata shi, ko ba zuwa aiki ba ai dole wata rana za ki yi aure ki tafi ki barta, ko da yaki kin ki bari ma aga fuskar na ki kullum sai boyo kike”

Na yi murmushi ina kallonta a yayinda muka kawo a hanyar da za mu rabu.

“Farida kenan, ni ban taba kawo wa kaina tunanin aure ba, ban taba lissafa kaina a cikin matan da za a iya aure ba”

“Saboda?”

Ta tambaya cike da mamaki. Sai na sake yin murmushi a karo na biyu na ce.

“Ba ni wannan lokacin da zan tsaya na yi fira da wani namiji ba, kullum tunanina ina abinci zai shigo, yanzu kuma tunani ina kudi za su shigo na nemawa Nana lafiya, bayan haka maza basa son yarinyar da bata da arziki a gidansu, sun fi son aure yar masu kudi ko mai rufin asibiti, amman irina idan aka ce za amin aure na san daga ni sai tabarma za a kaini, wanda na san hakan zai iya janyo min wulakanci da kankanci a gurin mijin da yan'uwansa”

Kallon hawayen da suka cika idona ta tsaya yi sai ta rumgume itama idonta cike da kwalla.

“Za ki yi aure kawata, In-Sha-Allah za ki auri mutumen da zai dauki dawainiyarki har da ta Nana ma, na saka ki gaban mota yai ta yawo da ke a garin nan”

Na sake ta ina yar dariyar zancenta.

“Farida kenan, wa zai yi mace irina haka? Mace da batai boko ba, bata waye ba, bata iya komai ba sai bara da roko a titi? Babu wanda zai so auren makaskanciya”

“Ataa karki yanke kauna daga rahamar Allah, dan jarrabe ki a haka ba shi yake nufin ba za ki samu jindadi a gaba ba”

“Na sani, kawai ina duba yanayin rayuwar ne, duniyar ta canja ba kamar da ba ne, ke dai ki tafi makaranta kar ki yi latti”
Chapter 22 · 0% Book details