← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 143

Sashe 72

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Na fada masa ita yanzu ba soyayya ne a gabanta ba, domin mahaifiyarta babu lafiya, wata kila kalaman nawa ba su masa dadi ba, na tafi kai abincin asbibiti tare da ita ko da na dawo na tarar ya tafi, ni kuma ban jidadin hakan ba”

“Miye abun rashin jindadi a ciki Momy? Ai gaskiya kika fada masa mahaifiyar yarinya ba lafiya ban dan rashin tunani ba har ya dube ta ya fada mata yana son ta? Kuma yarinyar nan yanzu abunda take bukata ilmi, bata san komai akan addinta ba, yarinyar da bata iya banbance muharrami da ajnabi, ko mahaifiyarta ta samu lafiya ai ilmi ne first abunda take bukata a yanzu i never thought akwai jahilan mutane irinta Wallahi”

“Akwai sosai ma, bara fa take wai kaga ba lallai ne ace tana zuwa makaranta ba,ni kaina na fada masa hakan ne saboda na san be kamata yai mata maganar a yanzu ba, shi kuma be fahimci ni ba”

“Babu wani rashin fahimta, taya zai ce yana son yarinyar da be san familynta ba? Kuma yar talakawa kamar wannan ai yasan Mama Fulani ba zata taba Amincewa ba”

“Shiyasa yake son ma shige masa gaba, kuma ni mai masa komai ce idan hankali ya kwanta”

“Idan tana son sa ko?”

Ya fada yana mikewa tsaye domin shi sam baya son maganar ma.

“Mi zai sa ba zata so shi ba, miye Muhseen ya rasa?”

“Ina abincin yake?”

“Yana kitchen”

Ficewa yai daga dakin zuwa kitchen din, yana ta tunanin halin Muhseen da son banbancewa idan da haske son Ataa yake ko aa, and if ma son ta yake da gaske ai be dace ya fada mata a irin wannan yanayin.Har ya isa asibitin be daina jin haushin Ataa ba shi ya rasa wace irim yarinya ce da har zata tsaya ta saurareshi, he wonder wace amsa ma ta bashi, yaushe ya fada mata zuwansa a nan ko kuwa tun suna Abuja? Wannan karon ba kamar yadda ya saba shiga dakin ya shiga ba, da sallama ya shiga tsabanin baya da sai dai ya tura kofar ya shiga a haka ba tare da sallama ba. Laraba ta amsa masa Ataa kusa na zauna saman gadon da Nana take tana ta mata fira baki har kunne. Da wani irin far'a marar misaltuwa Ataa ta kalleshi kyau da tai da far'ar data haska fuskarta sai ta tasa gabansa faduwa a karon farko. Ba laifi ya saki fuska sai dai ba sosai ya karasa gurin Nana yana mata ya jiki.

“Nana wannan shine Aliyun”

Ataa ta fada mata tana nuna mata domin a yanzu shi Aliyun ne ta gama bata labari da kanansa da kuma mahaifiyarsa.

“Ba mahaifiyarki ba ce kike ce mata Nana?”

“Haka ake kiranta”

“Idan haka ake kiranta ke sai ki kirata haka?”

Tayi shiru tare da yin kasa da kanta.

“Karki sake kiran sunanta ba kyau kiran sunan mahaifiya”

“Ba sunanta na gaskiya bane, sunanta na gaskiya Asma'u”

Wata uwar harara Aliyu ya watsawa Ataa daman wani bakin haushinta yake ji na rashin dalili. Ko minti goma be yi a dakin ba yace zai ta fi sai Nana ta ce.

“Mun gode sosai Ataa ta fada mana yadda kake ta hidima da mu kai da yan'uwanka Allah ya saka da alheri ya kara rufa muku asiri ya tsare ku daga ko wane irin sheri ya kara arziki da wadata”

“Amin”Ya amsa har karkashin zuciyarsa ya jidadin wannan adduar kusan a rayuwarsa sai yace be taba samun wani talaka ya masa irin wannan addu'ar ba, ba ma talaka kadai ba, ko mai arzikin dan'uwansa be taba masa irin wannan addu'ar ba. Bayan ya amsa da Amin din ya juya ya fice daga dakin. Yana fitowa daga ward din ya hadu da doc Bukar sama sama suka gaisa da Doc Bukar din har Bukar yake labarta masa yadda sukai da Ataa ranar, a nan Aliyu ya warware masa zare da bawa akan maganar tun daga farko har karshe.

“Daman ai na san ba zaka aikata ba, ga shi kuma an yi tiyatar cikin nasara gaskiya Doc Muhseen yayi kokari sosai yanzo in time kuma ya maida hankalinsa kam aikin sosai, Allah ya saka hannu a ciki ba a samu wata matsala ba”

Aliyu ya yi shiru be ce komai ba har suka jero suna tafiya gurin motarsa.

“Ni Wallahi yarinyar ta ba ni tausayi sosai irin wannan idan mutum ya same ta ai sai ya rike ta amana”

Ya fada daidai lokacin da Aliyu ya bude motarsa zai shiga ya zauna, kallonsa Aliyu yai sai kuma yai yar dariya mai sauti ya rufe motarsa ba tare da ya ce komai ba, Doc Bukar din ma dariya yake domin shi har ga Allah Ataa ta masa duk da kasancewar matarsa ma fara ce kuma ba shi da niyar kara aure amman ganin Ataa ya ji yana son ta yanayinta da komai nata sun masa.
Sai da Aliyu ya kama hanyar wurno road sako ya shigo wayarsa, yana dubawa ya ga number Rahma.

_Aliyu kana ina_

Be bata amsa ba ta sake aiko masa wani.

_Naga Amina ta saa shegiyar yarinyar a status dinta daman tana gidanka ko?_

_I Love you_

Shine reply dinsa a gareta yana murmushi.

_Kana can gurinta ko Aliyu?_

_I Love You_

Ya sake aika mata da reply.

_Daman na sani ai tana nan cikin ranka amana ta za ka ci ko Aliyu_

_I love you_

Ya sake aika mata as reply.

_I hate you_

Ta rubuto masa a take, wani kasaitaccen murmushi yai ya kara gudun motarsa yana karba kiran Nasir da ke shigowa wayarsa a yanzu.MUHSEEN POV.

A ka'ida sai gobe zai koma Abuja kamar yadda ya siya ticket amman ya kasa hakurin zama gidan na minti talati ma balle har ya sake kwana, a yanzu ya fahimta ba Aliyu ne kawai baya son alakarsa da Ataa ba har da Momy domin a yanayinta da ya gani da kuma irin amsar da ya ji a gurinta yasa shi fahimtar hakan, wata kila ita ma bata son ya so Ataa saboda dan ta yana sonta, wanda yake ganin hakan kamar nuna masa banbanci ne tsabanin Aliyu da Mama Fulani take nuna masa kauna fiye da Muhseen din da ta haifa. Shi har yanzu be ga laifinsa dan ya nuna son Ataa saboda tana da kyau ba, ya sani musulunci ma be hana a so mace dan kyauta ba, idan kuma har Aliyu zai nuna kebewarsa da ita matsala shi ma din be dace ya kebe da ita ba, domin shi din ma ba ma a sumi ba ne. Har ya isa Kaduna Momy bata daina kiran wayarsa ba shi kuma be daga ba, be ko tsaya kwana a kaduna ba haka ya bi hanyar Abuja, wani bangare na zuciyarsa yana ba shi hakuri akan ya kyale Ataa ya cire a zuciyarsa yayinda dayan kuma ke zuga shi akan idan har ya barta ya nuna Aliyu ya ci galaba akansa kenan kuma be kamata ya kyale Momy da Aliyu yayi musu hallacci ba idan su din ba su masa ba.

Ya shiga Abuja late domin uku na dare ta yi, ya dade yana danna horn kamin a bude masa gate din. To his surprise da ya shiga ciki sai ya samu Mama Fulani da Abbah da su Maryam da Rukaiya duka farke har Baby ma sai fira suke ana cikin nishadi. Ba karamin tsoro da mamaki suka ji ba ganinsa, domin ba saka ran dawowarsa yau ba ko dai zai dawo ba cikin dare kamar yanzu ba.“Lafiya ba ku yi bachi ba?”

“Muna celebration ne mutumen nan na Nijar da na ke fada maka ya siye kamfanin har an biya kudi kuma ya danka ragawar kamfanin a gurin Abbah ku, har da wasu gyare gyare ma zai yi”

Mama Fulani ta fada baki har kunne.

“Mashallah abu yayi kyau Abbah congratulations”

Ya mikawa Abbah hannu sukai shaking.

“Congratulations to us, Muhseen ya za ka biyo hanya a dare nan? Lafiya dai?”

“Ba lafiya ba Abbah amman da safe za mu yi magana”

A take murmushi da murnar da ke fuskarsu suka gushe. Bama kamar Mama Fulani da bata son damuwar yaranta.

“Ka fada mana ko minene a yanzu ba sai da safe ba, ba za mu iya jira ba”

“Ki bar shi idan ya huta da safe sai mu ji ko mienene tashi kaje dakinka”

“Na gode Abbah”

Ya fada yana mikewa tsaye ya fice daga falon cikin yanayin damuwa.

“Ko fada sukai da Aliyu? Ko kuma matar da kaje yi ma aikin ce ta mutu ko wani abun ya faru ba”

Maryam da Rukaiya sun fada.

“Ko ma minene za mu ji da safe, ku tashi muje ku kwanta”

Abbah ya fada yana mikewa tsaye ya fice daga falon zuwa part din Ammy. Lokacin daya shiga part dinsa wanka fara yi yai sallah isha'i da samu yi ba sannan ya saka kayan bachi ya hau saman gadon ya kwanata. Kasa bachi ya yi sai juyi yake akan gadon, duk wani so da yace yana ma Ataa a da sai a yanzu ya gane wasa ne, domin a yanzu ne yake jin matsifar son ta cikin ransa da kuma tsanar Aliyu, tabbas ba zai iya yafewa ta ba, domin a yanzu na gane duk na da ma wasa ne yanzu nen yake sonta da gaske. Kamar kar Aliyu ya fadi cewar yes son ta yake sai ya ji ya kara tsanar Aliyun son ta kuma na karuwa a ransa.

*Khadeeja Candy*

*ZAKI

By Khadeeja Candy

35...
Chapter 72 · 0% Book details