← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 143

Sashe 30

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya maimaita, bayanin ma yana jin ba zai iya mata ba, sai dai ya saka wani yai nata ko ya rubuta mata a rubuce, balle kuma har kalmar bada Hakuri ta shigo tsakaninsu, abunda yake jin ya zama wajibi akansa kawa ya wanke kansa daga kallon azzalumin da take masa ne.

“Amman kasan inda take?”

“No”

Ya bawa Nasir amsar a takaice sannan ya kashe wayar ya mike tsaye ya nufi upstairs...

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Ko da ya shigo dakin ya samu Rahma ta gama sallah tana kokarin tashi tsaye, haka ta dauki carpet din ta jefar gurin akwatinta dan bata iya ninkewa sannan ta aje.

“Dear ina da ina Daddy ya ke gina gidajen da be karasa ba?”

“Gurare da yawa wani abun ne?”

Ta tambaya tana kallonsa sai ya zaunar da ita ya zauna a kusa da ita yana sakar mata murmushinsa kadan.

“Da ina da ina?”

“Akwai wani Clapperto road, akwai a ali akilu akwai a guiwa da sauran gurare, mi za kai?”

“Ina son na duba mai girma ne sai na yi ma Daddy magana mu bude karamin kamfani da shi”

“No Aliyu ni fa bana son zamanmu a garin nan, gaskiya ni Abuja na ke son mu koma cikin satin nan ma”

“Ba dole ni zan zauna ba, zan saka wasu ne”

Ya fada yana mata kiss sannan ya mike tsaye yana kallon kansa a madubi.

“Idan kina son Abuja za mu ko, amman ni zan dawo na karasa wani aikin”

“Fita za kai?”

Ta tambaya tana mikewa tsaye

“Yes fada min abunda zan zo miki da shi”

Hannu ta kai ta raka rigarsa tana kallon cat eyes dinsa.

“Aliyu ina za ka je?”

“Momy ke nema na”

Ya bata amsa kai tsaye, wanda hakan yasa ta sakinsa ba dan ranta ya so ba, domin zuciyarta ta fara yi mata zargi akansa, sai dai ba damar hana shi fitada kuwa karya yai mata tunda ya ambaci sunan Momy.

“Bana son komai amman ka dawo da wuri”

Ta fada cikin yanayin da ke nuna bata son fitar tasa. Sumbantar goshinta yai

“Sure”

Sannan ya juya ya fita yana wasa da keys din hannunsa. Gurin windows ta nufa ta tsaya daga can sama tana kallonsa har ya tashi motar aka bude masa gate ya fice, ajiya zuciya ta sauke zuciyarta na raya mata wani abu marar dadi, yadda ta ke ganin Aliyu yana maganar yarinyar kwana biyu ta soma rashin yarda da fitarsa, ta san ba abu ne mai sauki ya samu gabinta ba, ba kuma lallai ya tsaya neman yar talakawa kanar wannan ba, amman zuciyarta na raya mata cewar mijinta zai iya son yarinyar saboda kyauta.

“Ba lallai ne ya so ba, nasan Aliyu baya son talaka, kuma ko da ma yana son ta da gaske idan na nuna masa bana so ba zai yi ba”

Ta furta ma kanta a kokarinta na kusar da abun a zuciyarta, domin saukar numfashinta yake tarewa a duk sa'in da tai tunanin cewar Aliyu zai hada son ta da wata.

“Wadanda ma suka fita arziki, tsabta kwalliya sun kula Aliyu amman be kula su ba, balle wannan yarinyar, shi kansa ya san ba sa'ar da zai kawo ma kansa wannan a zuciyarsaba ne”

Wannan karon murmushi take tana fadin wannan maganar, kamin zuciyarta ta kawo mata wani tunanin na dabam.

“Miyasa ya ke cewa ya kamata mu taimaka mata?. Saboda yana ganin kamar ta taimake ni na samu lafiya ne! That's it,”

Wani shaukin son mijinta ne ta ji ya lullubeta, ta sani sarai Aliyu yana sonta baya son bacin raita kuma be hada sonta da son kowa ba, miyasa ma zatai wannan tunanin tun farko? Sai a yanzu take jin kamar ba ta kyauta masa ba, da tai tunanin zai iya son wata yar talakawa can kamar Ataa yar talakawa ma kuma yar aikin gidansa, ji tai kamar ta yi wani katon sabo, shi kansa ta san idan ta fada masa zargin da take masa ba zai jidadi ba, kuma zai yi fushi da ita.

ALIYU POV.

Clapperto road ya fi tsaya masa a rai, domin tana fadin sunan unguwar ya tuna da lokacin da ta fashe masa gilashin mota ya biyo titi sai gashi ya ganta ta shiga kangon gidan, sai dai be taba tunanin cewar mahaifin Rahma ne da gidan ba. A hankali yake driving dinsa har ya isa unguwar daidai inda yasan gidan yake ya tsaya, daga cikin motar ya yake kallon kwannon da aka saka aka zagaye gidan, kofar shiga gidan a rufe, hakan kawai ya samu kansa da kin son barin gurin, and baya jin zai iya fitowa daga cikin motarsa ya tambaye wani ina masu gidan ko abunda ya shafesu, yana daga cikin abunda ya tsana neman wani abu that's why sai dai ya saka a masa, but this time around yana jin kamar da kansa yake bukatar yin gudun kar wani yai masa fahimta baibai.
  Sai da ya hango wani tafe kusa da motarsa sannnan ya sauke gilashin motar ya bude baki kamar baya son magana ya ce.

“Malam ina masu gidan nan?”

Mutumen da aka tambaya ya tsaya daidai gilashin motar Aliyu yana kallonsa ya ce.

“Mai ainahin gidan kake tambaya?”

Aliyu yai shiru na yan mintuna kamar ba zai sake cewa komai ba.

“Wata fulanin yarinya na ke tambaya”

“Oh Ataa buzuwa ga inda suka koma can, gidan na shiga kwanar akwai wani karamin gida ba sosai ba, ka tambaya suna can”

Mutumen na gama yi ma Aliyu kwatan gidan da ke nesa da wannan, Aliyu ya daga gilashin motarsa ba tare da yai ma mutumen godiya ba, ba kuma tare da ya sake cewa komai ba. Har mutumen ya ji haushin bata lokacinsa da yai yana masa bayani. Inda mutunen ya kwatanta masa ya nufa amman ya ki ya shiga kwanar ya tsaya yana hangon gidan da yake sa ran shine mutumen yake nufi. Idan ma ya ganta mi zai ce mata? Shi ya fi tsaya masa a rai, yasa ba zai iya bata hakuri ba, and ba zai iya tsayawa yi mata bayani ba, then miye na neman inda take har ya nemi ganinta.

‘No idan na ganta da ido na tabbatar tana nan zan saka wani ya zo yai mata bayani, ba ni da hannu a ciki’

Zuciyarsa ta raya masa, gamsuwa da wannan yasa shi shiga kwana ya tsaya daidai kofar gidan, babu wanda zai aika ciki and wa zai ce a sallamo masa ma idan ya aika din? He decided ya danna horn idan an fito fine idan ba a fito ba kuma ya kama gabansa. Sau biyu ya danna kan yai na uku Farida ta leko ganinta yasa shi sauke gilashin motar yana aika mata da wani kallo. Tabbatar da kofar gidansu ake horn din yasa ta koma ta saka Hijab dinta ta fito ta nufo inda yake fake da Motarsa yana kallon kofar gidan na su.

“Ina wuni?”

Ya gyada mata kai alamar ya amsa gaisuwar gaisuwa sannan ya motsa bakinsa kadan ya ce.

“Wata buzuwa na ke nema ance suna nan”

Gaban Farida ya fadi, jin cewar Ataa yake nema, gashi daman daga ganinsa ba zai yi mutumci ba, abunda ya fara zuwa a ranta mi Ataa tai masa da ya zo nemanta, mi zai mata? Miyasa yake nema? Duk a lokaci daya tai ma kanta wannan tambayar.

“Sun tashi daga nan”

Ya sake kallonta kasa da sama ba tare da yace mata komai ta shiga masa bayani domin itama kanta tana jin kamar zai gano karyarta ne.

“Eh mai wacan gidan ne ya ce sai sun tashi, saboda an fada masa maciji ya sari maman Ataa, da aka kaita asibiti suka dawo nan shine ya sa aka watsar da bukkarsu aka koresu ya zagaye gidansa, sai suka dawo nan shekaranjiyar nan suka koma Kaduna”

“Ba su gida ne?”

“Ba su da gida daman bukka ce suke kafawa da mutumen ya koresu suka zauna nan na kwana biyu sai kuma shekaranjiya suka koma Kaduna”

“Kaduna wane unguwa?”

“Na'am...”

Tai shiru tana ta tunanin unguwar da zata fada domin ko a sokoto ba ko wace unguwa ta sani ba balle kuma a Kaduna da bata taba zuwa ba.

“Rijiyar Zaki... ”

Ya sake kallonta da kyau gashi fuskarnan tashi babu annuri duk sai tsoro ya kara kama ta.

“Aa ba can ba unguwar mai malala... ”

“Malali?”

Ya gyara mata jin kamar ba ta fada daidai ba.

“Eh eh can fa, kusa da wani gida mai jan gini zaka ga bukkarsu a gurin”

Hannunsa ya saka ya dauko katinsa da ke cikin motar ya jefara kasa.

“Ga kati nan idan kin samu labarin gaskiyar inda take ki aika min sako ta number, ko kuma ki tura min number ta”

Dukawa tai ta dauki katin tana fadin.

“Su da ke neman abunda za su ci ina ma zata samu waya, amman miyasa kake nemanta ta maka wani abun ne?”
Chapter 30 · 0% Book details