← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 143

Sashe 78

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

After Nana ta huta, Amina ta nuna musu bq ita da Ataa. Sai ya rage falon daga shi sai Momy.

“Momy Rahma bata gida har yanzu”

Kallon mamaki Momy tai masa.

“Ban gane ba?”

“Tun wacan lokacin da muka samu misunderstanding akan matsalar Ataa shikenan tai fushi ta tafi gida”

“Kana nufi duk tsawon lokacin nan bata gidanka?”

“Tana gidansu”

“Kuma iyayenta ba su kira sun bincike matsalar ta ba?”

“Da za su kira ai da sun kira ko kuma Abbah ta ya kira Daddy ya ji ko mienene matsalar”

“Hmmm Allah ya kyauta, abunda suke yi ma yarinyar suna ganin kamar so ne ko gata Wallahi suna lalata mata rayuwa ne kawai, abun kadan yarinya tace ta tafi gidansu sai kace wata mai shan nono”

“Ni dai Momy so na ke a shirya mu da ita na yi alkawarin ba zan je bikonta da kaina ba domin ni ne mai gaskiya”

“Ai da ka bi ta tawa ka barta can gidansu ta dandana zaman gidan ta ji idan da dadi kamar na gidan miji, kishi hauka ne ko cewa kai tana son Ataa laifi ne balle baka furta ba, haka ake rayuwa”

“Momy ni dai ayi hakuri a dawo min da matata dan Allah”

“Na ji sai Daddyn ka ya dawo ai ko?”

“Tau na gode”

Ya fada, ba dan komai yake son a dawo masa da Rahma ba, sai dan yasan ita kanta tana cikin damuwarsa a yanzu duk kuma abunda ta aikata saboda shi ne, domin tana son sa tana kishinsa ne, after that yana son matarsa a kusa da shi shi kanshi ya san yayi hakuri iya hakuri har na sati biyu ba tare da Rahma a kusa da shi ba, hakan na matukar damunsa domin ya san ita kadai ce a duniyar ke iya yaye masa wannan kishin da yake ji matukar ba alfasha zai aikata ba.

Husna ce ta fito manne da waya a kunne tana tambayar Momy ina Ataa.

“Wake nemanta?”

“Ya Muhseen ne ya ce a akai mata waya”

“Tana bq”

Momy ta bata amsa sai ta nufi hanyar fita daga falon, Aliyu ya bita da wani kallo kamar ita ce Ataa.
ZAKI

By Khadeeja Candy

37...

“Momy idan ba ki takawa Muhseen burki tun yanzu ba, zai iya wuce guri fa”

Momy ta masa kallon rashin fashimta.

“Wuce guri kamar ya?”

“For god sake Momy taya zai rika nunawa yarinyar wata soyayya a yanzu? Allah kadai yasan irin kalaman da ya ke furta mata”

“Shi kiranta a waya har wani nuna soyayyah ne? Idan ma haka din ne ai sonta yake sai ya fara nuna mata yana sonta? Dan wajen Fulani ka rika kyautatawa Muhseen zato, ka fi kowa sanin cewar ba mugun mutum ba ne kuma ba dan iska ba ne”

“Na sani, amman ke kanki Momy kin san Mama Fulani ba zata bari Muhseen ya auri Ataa ba saboda tana ganin darajar Ataa da ita ba daya ba, shi kansa ya sani kawai yana son ya batawa yar mutane lokaci da rayuwa ne kawai, daga lokacin da ya samu damar kaiwa ga jikinta Wallahi ba zai sake cewa yana sonta ba, domin kyauta yake gani, kyaun da idan ya samu dama zai iya zaga mata rigar mutunci shikenan kuma ta daina burge shi, idan ba a taka masa burgi yanzu ba nan gaba karatun da ake son ta yi ma kasawa za ta yi domin soyayya kawai zata sakawa gaba”

Murmushi Momy tai tana ma danta wani kallon na fahimtar wani abun da shi Aliyu be san da shi ba.

“Idan ma haka ne, ai sai ta aureshi ta cigaba da karatunta a gidansa ja ga babu wani zancen daukar hankali, kai ka kanka mai nemawa Muhseen aurene fa, balle kuma ni da na ke uwarsa, hankali dai ya kwanta kawai”Mikewa Aliyu yai tsaye domin maganar Momy sam bata masa dadi ba, dinning ya nufa ya zauna ya zubawa kansa abincin rana da be samu ci ba ya maida hankalinsa yana ci ba dan abincin yana masa dadi ha duk kuwa da kasancewar abunda yake so ne aka girka, ba kuma zai iya fadar dalilin rashin jindadin abincin ba, ci yake hankalinsa na can gurin Ataa wacce Husna ta kai mata waya, kamin ta dawo duk ya takura, ji yai ba zai iya hakura ba ya tashi ya fice daga falon gaba daya zuwa bq, a gurin aje motoci ya samu Husna tsaye tana jiran Ataa dake can gefen fulawoyi ta gama wayar ta bata wayarta.

“Ke kar Muhseen ya sake kiran wayarki ya ce ki bawa Ataa ki kai mata, na hana daga yau”

“To ba zan sake ba”

Ta amsa da sauri tana gyada masa kai. Ya nufi inda Ataa take zaune wayar a kunnenta tana murmushi hannu kawai ya mika mata alamar ta bashi wayar, sai ta tsaya kallonsa ba dan ba ta fahimce shi ba sai dan jira take sai ya furta.

“Wani wayar”

Ya furta da karfi sai ta mika masa tana kallonsa da fararen idanuwanta masu kamar madara ta turo masa baki alamar ta ji haushi, katse kiran yai sannan ya nuna ta da wayar.

“Karki sake waya da Muhseen a cikin gidan nan”

Bata ce masa komai ba bayan idon da ta sakar masa shi kuma ya juya ya koma gurin Husna ya mika mata wayarta sannan ya bude motarsa ya shiga ya bar gidan.
Duk abunda suke Momy na hangensu ta windows din kitchen murmushi tai tana ta kallon yadda Ataa ta turo baki, ta sani da ace wata ce a cikin kanensa wata ta turo masa baki yau sai ya fasa bakin nan amman da yake Ataa ce gashi ya tafi ya kyaleta, yadda Aliyu yake nuna kishinsa akan Ataa ta sani sarai son Ataa yake ba wai yana gudun shigarta wani halin ne kawai ba, sai dai shi din be san yana yi ba. Shigowar Husna a kitchen din yasa Momy barin jikin windows ta kalleta still tana murmushi.

“Momy kin ga Ya Aliyu da fusata wai kar na sake bawa Muhseen wayata su yi waya da Ataa, gashi Yanzu Ya Muhseen din kiran ma yake na ki dagawa ban san mi zan ce masa ba”

“Ina hangenku ai, idan ya sake kira kice ni ya kira a wayata zan bata su yi wayar”

“Okay tau”

Husna ta juya ta fice daga kitchen din, Momy ta dafa kitchen cabinets tana fadin.

“Lokaci da yana zuwa, zancena zai tabbata wata rana, zaka duka har kasa kana rokon yar talakawa ta so ka lokacin da ba zan iya maka komai ba, domin ba zan zabe ka na bar Muhseen ba ko kuwa ina son hakan, amman ko ba komai son yarinyar nan zai maida kai namiji na jidadin da kake kishi a yanzu, at least zata koya maka kishin matarka, zaka fahimce wayewar zamani da boko ba komai ba ce idan aka hada ta da addini”Ita kadai take magana da kanta cikin yanayin na rashin jindadi. Ba ta bar kitchen din ba sa da ta dora girki dare. Yau Daddy dawowar maraice yai domin ana daf da kiran sallah magariba ya shigo gidan, direbansa ne ya bude masa mota sannan ya fito ya dauki jakarsa ya shigar masa da ita part dinsa, Daddy kuma ya nufo part din Momy yana gyara zaman babbar rigarsa, tun kan ya kai hannu ya bude kofar ta bude masa fuskarsa da murmushi.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa”

Ya amsa yana naso kafarsa cikin falon, kujerar da ke kusa da kofa ya zauna yana sauke agajiya, Momy ta nufi gurin freezer dake gefen dinning ta dauko masa gorar ruwa da kofi ta kawo masa.

“Yau dawowar wuri akai SSG?”

“To mun gama abunda za ayi, zama na me kuma?”

“Ai ko ka dawo a daidai, da na so ma na kira kuma ban samu dama ba”

Sai da ya sha ruwan da ta mika masa sannan ya kalleta ya ce.

“Wani abun ne?”

“Dazun ne Dan wajen Fulani yake fada min cewar wai Rahma bata gidansa tun sati biyu da suka wuce”

Daddy yayi fuska manya irin ta mamaki da son tantace magana.

“Tana ina?”

“Wai ta yi fushi”

“Fushi? Fada suka yi?”

“Ba fada suka yi ba, kawai dai akasan yarinyar nan da ke jinya asibiti, ita Rahma ta saka aka je aka daketa da zo na fada masa shi ne tai fushi”

Daddy ya kyalkyale dariya kamar ba wanin abun ba.

“To ko kishi take? Yaushe akai abun?”

“Tun sati biyu da suka wuce dazun ma aka sallamo Nana daga asibitin, ni ban ma sani ba sai dazun yake fada min wai a masa bikon matarsa”

“Kuma fa muna yawan haduwa da Alhaji Nasiru Gobir be taba min maganar ba”

“Wata kila yana maka kallon ka sani ne”

“To Allah kyauta mutanen ne basa da dattako sam, ace yarka ta dawo gida har na tsawon sati biyu ai ya kamata ya bincika ya ji miye dalili”

“Dalili ya wuce bin bayan yarsa, kasan duk abunda ta fada shine daidai, sam ba su mata tarbiya mai kyau ba, ace abun kadan ka debi kafafuwa zuwa gidanku, yarinya lafiya ma bata isheta ba duk dawainiyar da yake da ita basa gani, wani lokacin Wallahi har tausayi yake bani, kwata kwata dan wajen Fulani ba san dadin aure ba”

“To shi kuma a haka son abarsa yake, da dai ya samu wata ya kara ai ita ma zata bawa kanta lafiya, mace idan tana ita kadai kuma tana ganin gata ya mata yawa zata ta yi abubuwa da dama ai, ko da yake Aliyu dan boko ne ba son mata biyu yake ba”

“Ba wani gata rashin tarbiya dai ne tun a gida ba a koya musu tarbiya mai kyau ba, ni da gatan be saka na yi wani abun ba”

Daddy ya mike tsaye yana zolayar Momy

“To ke duk kika gwada yi ai sai a kawo miki kanwa, ga mata nan duk inda na shiga kallo na kawai suke”

Momy ta dan harare shi.

“Ai ba kai suke kallo ba mukamin ka da kudinka suke kallo, idan ba dan kudi ba waye zai so tsoho? Ko ma watan ka kawo ai na gama cin moriyarka kuma na zama uwargida mai yayan gida sai dai ta bi”
Chapter 78 · 0% Book details