Sashe 143
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Cikina na da wata uku Hubby ya sama min admission a american university da ke Abuja, a lokacin da ya fada min yadda tsari da daliban makarantar suke sai abun ya tsorata ni sosai ina ta ganin kamar ba zan iya ba, ashe abun saka kaine kuma karatun ya zo min da sauki saboda na yi nisa a qur'anen ina daf da sauka ma, sai hasken karatun ya kara bude min kwakwalwata, da safe kullum sai Hubby ya biya min na qur'anen a na bokon ma inda ban gane ba yana min karin haske, domin ya fada min abunda ban gane ba na rika tamyarsa ko wata mace, amman be yarda na tambayi wani namiji ba da sunan class mate dina. Makarantar ma kamar wacan sai na rufe komai na ke tafiya shiyasa babu wanda ya san fuskata sai matan da muke shiri da su sosai shi ma waenda suke da contact dina muke ziyarar juna ko suke ganin status dina.
Lokacin da na fara zuwa na maida hankalina da kuma yawan tuna burina sai abun ya zo min da sauki, sai dai wannan cikin ba kamar wacan ba ne, wannan na sha wahalar sa sosai ga shi kuma ina farko farkon fara karatun ne. A haka nai ta fama har cikin ya girma a lokacin muna daf da fara exam din shiga ug 2, a haka nai jarabawar cikin wahala Hubby na ta tausayina kamar yadda na saba sai dai baya karya min guiwa saboda ya san burina kenan.
Bayan exam da sati biyu na haifi yan biyu duka mata kyakkyawa, wannan karon ma sai da aka min kari kamar dai wacan, a gidana akai bikin dattijiwar da ke kula da gidan ita ke hada ruwan zafi tai ma twins wanka wato mai sunan Mama Fulani da mai sunan Mama na sai akai musu lakani da Nimra da Namra. Bayan wata biyar fa haihuwar twins muka je Nijar bikin Mama da wani dan'uwanta, ni abun har dariya ya ba ni wai Mama za tai aure sai dai na san auren shi ne darajarta da martaba da kuma mutuncinta.
BAYAN WADANSU SHEKARU.
Wa zai gan ni a yanzu ya ce ni ce a wacan lokacin nai bara da roko a titi, ni ce na sha wahalar rayuwa na fuskanci kalubale na rayuwa kala kala, mai hakuri madawaci kuma wanda ya rike Allah baya faduwa kasa, duk kuma wanda Allah yai masa gata to ya huta kuma ya dace. Na rike Allah na yi hakuri kuma na ci ribar hakurina Allah kuma be barni na yi kunya ba, da duk wanda yake kallona a matsayin banza marar amfani ya koma yana min kallon kamar babu wanda ya kai ni gata ya fini dacewa da komai a rayuwata. Duk wanda ya gan ni a yanzu zai zata daga sama na samu arzikin ko kuma arzikin ya zo min sai wanda ya san wahalan da na sha kamin na samu wannan.
Wai ni ce rike da takardar bautar kasa na yi, na yi karatu kan burina na cika na yi degree in business administration amman bana karatu ba ko da yake ina da burin aikin sai dai na san Hubby ba zai bar ni ba. Na canja daga burina na karatun likita zuwa na gadon gidan mu wanda Mai Martaba yake son kowa yai saboda yin aiki a karkashinsa da kuma sanin ilmi akan kasuwanci da yadda zaka iya tafiyar da shi yadda ya dace. Al-hamdulillah ko a haka rayuwata ta kare ba tare da na yi aikin da Hubby baya son nai na samu abunda na ke kuma na gode Allah na, wata kila a gaba ya canja ra'ayinsa ya bar ni na cigaba da karatun wata kila kuma ba zai yarda ba, daman kuma ba duka buri ne yake cika ba, ba komai ake nema a samu ba, ba kuma duk a abunda kake so ne alheri a gurinka ba, sai dai ba zan kasa gode masa ba akan dukan kulawa da goyon bayan da ya bani har na samu cikar burina da ba ni damar amsa sunana AISHA UMAR MRS ALIYU MUHAMMAD.
*AL-HAMDULILLAH*
Dukan yabo da godiya su tabbata ga Allah mai kowa mai komai wanda ya ba ni ikon rubuta littafin mai suna Z A K I da kuma kareshi cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Na sadaukar da wannan littafin a gareki Mama Aisha Kabir A A Ladan.
Godiya ga dukan masoyana waenda suke cikin paid groups, na gode sosai da irin kaunarku a gareni Allah bar kauna. Waenda suka karanta ba su biya ba kuma na bi ku bashi indai hakkina ne.
Sai mun hade da ku a littafi na gaba idan mai rai da lafiya ya yarda. Ba littafi ne irin na yau da kullum ba littafi ne da zai tabo wani bangare na rayuwar wasu mutane da kuma wata macen da kaddara ta fada mata.
Ba kaddarar talauci ba ce kamar ta Ataa (Zaki)
Ba kaddarar Aure ba ce kamar ta Nawwara (Rai Biyu)
Ba kaddarar soyayya ba ce kamar ta Zinneera (Zabin Rai)
Ba kaddarar gudun iyaye ba ne kamar na Namra (Zagon Kasa)
Ba kaddarar asiri ba ne kamar na Hafsatu Manga (Hafsatu Manga yarinyar kauye)
Ba kaddarar rashin uba na gari ba ne kamar na Jodo (Khadijatu)
Ba kaddarar Ciwo ba ne kamar an Minal (Babban Goro)
Ba kaddarar kauyanci ba ne kamar na Maryam (MAIRO)
Kaddara ce dai wata ta dabam, wata kalar kaddara ce bata rashin gata ko ilmi ba ba kuma ta shashanci ko wauta ba. Labari ne tafe da rayuwar wasu mayu, da suke cikin wata alkarya.
Labari ne mai maida mace namiji ba, namiji a siffa da kamani, namiji a zuciya da jini.
Labarina na wata duniya biyu mai cike da abun mamaki da al'aji, labari mai hada Kasar Katsina da Bauchi a wata hadaka ta ba zata. FULANI labari na daman na Fulanin asali❤
*Daga yar Mutanen turankawa Fulanin kwarai, jinin Shehu Khadeeja Candy ce👌Yar mutane sakkwatawa*