← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 143

Sashe 139

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sati daya da wacan taron muka sake komawa sai da wannan karon bayan Shukura har da mutanen data fada cewar su ma an cire musu wani bangare na jikinsu, sun bada shaida kamar yadda Shukura ta fada, kuma dukansu kodar aka cire musu da alama dai Doc Asim ya kware a bangare cire koda ko samar da kodar a gurin masu nema a biya shi ta hanyar kwarai ko akasin hakan. Da aka tambaye su shin suma ba su da ilmi na kamar ne dayar wacce ta kasance matar aure ce kuma babbar mace ta amsa da eh. Ta saka hannu ne saboda bata san komai a kai ba, kuma ta fada mata yayarta na da ulcer dole ai an mata tiyata ashe dan ya cire kodar ne. Namijin ma be saka hannu a takardun ba an likitan ne ya saka hannu da kansa sai ya bashi dayar ya saka hannu wacce ita ce akai wa mahaifinsa aiki akai da sunan kodarsa daya ta lalace zai masa aiki a kyauta. Ba karamin mamaki sukai da jin lamarin ba, da aka nemi jin ta bakin Doc Asim sai ya amsa da cewar shi dayar ce kawai ta siyar masa da koda sai kuma ni amman sauran duka akan ciwonsu yai musu aiki. A lokacin da aka tambayeta ya akai ta san koda aka cirewa Yayarta sai ta amsa da cewar ita ma dai ta yi gwaji a wata asibitin kamar ni su suka fada mata cewar an cire mata kodar, sai dai ganin cewar ba su da inda za su sake kaita a karbetaa bata magani mai tsada da zata ji sauki yasa suka dawo da ita asibitinsa har ta rasu a nan, dukansu su ukun nan sun rasa majinyantansu shi namijin ma sai a yanzu yake gane cewar an cire wa mahaifinsa koda, sai dai biyun kamar ni ne wato talakawa masara galihu waenda ko za su ihu su nuna fushinsu da bakincikin da bacin rai ko son daukar mataki babu mai kawo musu dauki ko kula balle har ya shige musu gaba gurin karbar hakkin na su, ni ma din ba dan da Mai Martaba ya shiga ciki ya mika lamarin a gurinsu ba da ni da su duka ba za a karbo mana hakkin mu ba, babu wanda zai san da zancen an yi mana haka din idan kuma har mu kai unkurin yin wani abu na hukunta shi zai siye masu kamar yadda yai min, amman idan daga manyansa ne matukarvsuna son adalci dole su bi gaskiya kuma su kwato mana hakkinmu su kuma wanke kansu daga bata musu da aiki da yake kokarin yi.

Ba mu bar gurin ba sai da suka suka fada mana cewar za su tisa keyar Doc Asim kotu tare da na su hujojin idan sun kara bincike, hakan kuma ba ni kadai yai ma dadi ba har da sauran mutanen. Balle kuma Nana da ba a magana, sai dai sun bukaci dukan mutanen da ni kaina mun kawo takardun da suka nuna hakan kuma suka ba ce za su kai Mama asibiti su sake bincikawa.

Gobe zan yi long post In-Sha-Allah 🙏uzuri ne ya rike ni yanzu nai typing wannan.

AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.
Na fara zuwa makarantar koyon girki da ke badon 3bedroom, a ranar da aka fara da sabin dabibai. Ban wani sake sosai a ranar ba saboda ina jin kunya da nauyi saboda yawan daliban da ke gurin, malamar ta rubuta mana abubuwan da za mu siyo da kuma abubuwan da za mu fara koya.
  Kamar wasa na fara maida hankali ina koyon dukan abubuwan da suke koya mana, wani lokacin idan na dawo gida kuma sai na gwada, da na fara sabon da yan mata da kuma wasu sabin aure da suke makarantar sai ya zama idan ma naje bana son dawowa saboda samun kawaye da nai kuma kawaye masu mutuncin da sanin ya kamata. Mun yi musanyar number wya da wasu daga cikin yan matan da kuma matan auren, yawan matan auren da suka girmi sai dai na kira su da Anty ko Maman wane saboda ina jin nauyin fadin sunansu hakan nan kawai wasu su kira na da yata kasancewar ina da sunan yarsu wasu kuma su ce min kanwata.
Daga lokacin na fara fa'idantuwa da wayar da Hamma ya siyo min, domin ta nan nake chat dasu idan sun ga wani abun mai amfani sai min sharing su tambayi tafiya da ta miji, masu grps suka saka ni wata babban a cikin mu kuma ta bude mana wani grp na koyon girkin d muke, wai ko da akwai abunda Malama tai jawabi wanda mutum be gane ba sai yai tambaya a fada masa ko a kara wayar masa da kai. Na kara ilmi ba kadan ba, domin a cikin groups din da nake ana yawan turo abubuwna da suka shafi matana aure na inganta zamansu yadda za a iya kula da miji yan'uwan miji da sauransu, a cikinsu akwai wani wai shi Women Diaries na wata marubuciya, ina karuwa da grp din sosai abunda ban fahimta ba kuma sai nai tambaya a take za a fayyace min komai.
   Daga ranar da akai wacab case din ba ba su sae kira ba, har na sawon wata daya, sai da suka kara bincikensu suka tattara dukan hujojinsu suka tabbatar da abunda ake zargin Doc Asim da shi bayan sun tsananta bincike sannan suka mika shi kotu. Wani abun mamaki Doc Asim har da daukar lauya mai kare shi, ni da Mama ma lauya ne yake tsaya mana duk wani abincike ko gabatar da shaida shi yake yi. Hakan ya saka wani lokacin ba da ni ake zuwa kotun ba domin cikin nawa wani lokacin sai ya taso min da zazzabi wani lokacin kuma kamar ba ni ba. A cikin wannan halin Hamma ya dauke ni muka koma Abuja daman wani lokacin  yana tafiya yana dawowa saboda aikinsa, ni kuma baya son tafiya da ni saboda koyon girkin da nake. Yanzu kuma na kamalla daman ajin akwai na wata daya akwai na wata biyu uku hudu biyar har shakera uku ma ya danganta da wanda ka zaba. Ni kuma ya biya min na wata biyu ne kawai kuma babu laifi na iya abubuwa da dama na zamani da kuma irin na da da ake saffarawa a girka tun daga kan na sha wato home drink's har abincin. Wani abun kuma ina ra'ayi zan leka YouTube na duba na fada masa ya siya min kaza da kaza idan babu ina son na hada.
Muna saura kwana biyu muje Abuja Hamma yake fada min zancen baikon da za ayi ma Amina, na yi murna sosai ina jin na taka wani da za a kira matar yaya kuma a fada min wani abun na kanen mijina idan za ayi. Sosai na so mu fasa zuwan har sai an yi baiko amman Momy ta hana saboda tana son na walkilce a gidan Mama Fulani na kai lefen Muhseen da za'ayi wanda ba zata samu zuwa ba saboda baikon Amina ita ma Mama Fulani ba zata samu zuwa ba saboda kai lefen.
  A ranar da muka sauka Abuja a gidan Mama Fulani muka sauka kamar yadda Hamma ya saba idan yayi tafiya zai sauka a gidan Mama Fulani idan a sokoto ne kuma zai sauka a gurin Momy. na yi mamakin yadda muka samu Mama Fulani ta murje ido kamar ba ita ba, sai marhabun take mana da far'a da komai irin yadda take tarbar Hamma, tana ta nuna kulawarta akaina ni dai ban sake jikina sosai ba sai dai na lura hakan ba karamin dadi yai ma Hamma ba, ba ita kadai ba har su Maryam da Rukaiya sun murje ido suna sakewa da ni kamar komai be faru ba, ni kuma na kasa mantawa a duk lokacin da na kalle su ko kuma suka min wani abun na karramawa ko kulawa sai na tuna da baya. Suna ta shirye shiryen kai lefen Muhseen da za'ayi kamar yadda Momy ta fada.
Sai da muka huta a gidan sannan muka doshi gidanmu da ke can Abujar, an gyara ko'ina na gidan kamar muna ciki muna rayuwa.

“Na yi mamakin ganin gidan nan a haka, haka wacan zuwan na tararda gidan wanke fes”

“Gyarawa ake”

“Wa ke gyarawa?”

“Aljanu”
Chapter 139 · 0% Book details