Sashe 32
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Za ki sha wahala idan kika ce kunyata za ki ji, ga toilet can je ki yi alwala sai ki zo ki ci abinci”
Ina nufar inda ya nuna min sai Mama Fulani dake saukowa ta daka min tsawa.
“Karki kuskura shiga toilet din nan, yarana su shiga ke ki shiga akan me?”
Tsayawa nai cak ina kallonta kamar yadda shi ma yake kallonta.
“Sallah za ta yi fa Mama”
“Ko mi za tai taje can a tab din garden ta yi karta shiga mana toilet”
Kamar zai sake cewa wani abu sai kuma ya kalleni ya ce.
“Idan kin fita daga falon nan za ki ga wani gurin ai kin san Garden ko?”
Na gyada kai.
“To can za ki je”
Na juya na fice daga dakin ina hangen yadda Mama Fulani take watsa masa harara da alama bata jindadin yadda yake min magana ne. Fitowa nai daga part din na nufi garden din, ina shiga na samu kaina a cikin wani irin katon guri mai shuke shuke kala kala ga wani bangare an ware anyi pool mai zubar da ruwa gwanin sha'awa. Inda na hango fanfo na nufa na kunna daya nai alwala na shimfida dan kwalina kamar dazun nai sallah, da nai sallah sai na yi zamana a gurin ina ta kalle-kalle kamar an ce na juyo sai na hango mutum ta windows mai gilass yana kallona, kasa nai da kaina ina jin tsarguwa da kallon wata kila ma ya dauki tsawon lokaci yana kallo ban sani ba. Tasbihi na shiga yi da hannuna ina tasbihi da na gaji na tashi na koma part din dan na fara jin yunwa sosai, ina ko shiga na samu su sukansu a dinning suna cin abincin, a inda na zauna dazun na sake zama na labe bayan kujera.
“Yar kyakkyawa zo ki karba”
Muryar Ya Muhseen ce hakan yasa ni lekowa sai yai kirana da hannu, ba musu na tashi na karasa inda suke sai ya miko min plate din abinci cike da nama.
“Muhseen you know me well bana son haka, bana son wani ya ci abinci da kwannon da muke ci”
Mama Fulani ta fada tana kashe ido.
“Yunwa take ji”
“Dan tana jin yunwa sai ta ci abincin a plate din ka? What nonsense is this? Ke tara dankwalinki ki zube, kamin a duba miki wani gurin”
Mai nema sai hakuri, a haka na cire dankwalin kaina na aje akasa sannan na karbi abinci na zube a dankwalina yana ta kallona cikin yanayin da ke nuna be jidadin hakan ba, na dauka na fito daga falon gaba daya na koma garden na zauna na ci abuna sai da na koshi sannan na bude fanfan ko na sha ruwa na wanke dankwali na shanya. Ina gurin wani matashin saurayi dan kazo na zo ya same ni a gurin yana fadin.
“Ke zo a nuna miki gurin kwananki”
Tasowa nai na biyoshi yana gaba ina biye har muka isa gurin motocin gidan, wani tsohon gareji ya bude ya nuna min shi.
“Nan za ki rika kwana”
“To na gode”
Sannan ya juya ya tafi ni kuma na zauna a gurin, ina ta kallon yadda yai datti, ba a dauki lokaci ba sai gashi ya dawo da tsintsiya ya bani wai na gyara gurin, haka kuwa akai na share gurin tas sannan ya sake dawowa ya miko min tabarma yai tafiyarsa. A gurin na shinfidata na koma part din Mama Fulani na dauko yar ghana most go dina na dawo dakin na aje, sannan na dauko dankwalina. A gurin an kwana har safe asubar fari na farka daman ban yi bachi kirki ba, sakamanon rashin abun rufe gashi garin da sanyi, garden din na nufa nai alwala na sake dawowa nai sallah. Ina gamawa na nufi part din Mama Fulani ina taba kofar na ji ta a bude na yi mamakin hakan ganin jiya da muka zo da Maman Salma sai da aka bude mana, kitchen na nufa neman tsintsiya ba dan na san tana nan ba, sai dan neman tunda babu wanda zan tambaya, ta can kofar fita daga kitchen din ta dayan bangaren na samu tsintsiyar da mopper na dauko na zo na share falon tas kamar yadda aka fada min sannan na fara mopping.
Ina gaf da gamawa Ya Muhseen ya shigo falon yana sanye da Jallabiya.
“Eyyy ashe jaruma aka kawo mana, tun da safen nan kike mopping”
Na risina har kasa ya gaishe shi.
“Ina kwana”
“Lafiya kalau”
Sai ya amsa min da kamar mamaki.
“Amman tarbiyarki ta burgeni, ya sunanki ma?”
“Aisha”
“Ashe ki Mamansu Ammy ce, amman ke Fulani ce ko?”
“Buzuwa”
Na bashi amsa a takaice. Sai ya zauna saman sofa yana fadin
“Kina makaranta?”
Na girgiza masa kai.
“Miyasa ba ki san karatu yana da amfani ba”
“Na sani”
Na bashi amsa a takaice zuciyata na sosuwa da tambayarsa, na san da ace ina da halin karatun da babu abunda zai kawo ni nan, kuma babu abunda zai saka Doc Asim ya cuce ni.
“Ni nan da kika gan ni babu ruwana da karatu bana makaranta”
Kallon mamaki nai masa kamin na ce.
“Ka kare dai”
“Aa ban kare ba ni ban taba yin karatun ba”
“Likita ne kai fa”
“Inji wa?”
“Ranar da na ganka uduth da kayan likitoci na ganka kuma wani ya ce Doc”
Ya dan wara ido.
“Kai ashe kin iya gulma”
Kunya ce ta baibaiye ni har na kasa sake daga kai na kalleshi shi kuma ya saka min dariya. Ni dai ban ji ta kansa ba har nai na gama na koma kitchen din na gyara na wanke komai na aje, ina kokarin ficewa sai gashi ya shigo ya nufi gas yana fadin
“Kin iya amfani da gas ki dafa min Lipton?”
“Ban taba ba”
“Okay bari na nuna miki saboda wata rana, and wadacan plates din ba haka ake aje su ba, idan Mama ta gani zata miki fada gogewa ake sannan a jera”
Shi ya nuna min yadda ake kunna gas din sannan ya nuna min inda kyalle yake na dauko na goge komai naje a yadda ya nuna min. A yadda na lura Ya Muhseen ne ya fita dabam da mahaifiyarsa da kuma yan'uwansa domin mutum ne mai son fira ga far'a ba shi matsala da mutane domin a jiya kawai da na zo gidan zuwa yau da safe na ji na sake da shi kamar na sanshi.
Bayan na gama da falon na nufi falon Ammy ita na gyara mata, ko da na dawo part din Mama Fulani na samu duk sun fito daga dakunansu sai na sauki tsintsiya na nufi upstairs da zimmar gyara musu bedrooms dinsu sai Mama Fulani ta ce da ni.
“Idan kin gama kije ki gyara part din Muhseen”
“To”
Na amsa a ladafce sannan na haye sama na tura dakin farko.
1️⃣6️⃣
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
18.
A hanyarsa ta gida ya kunna datarsa ya aikawa Nasir sako ta whatsapp.
“Yarinyar an ce tana Kaduna unguwar Malali, ka sa a bincika min ita daga gobe, ka saka kudi a nemota”
Yana rubutawa Nasir hakan ya aje wayar da a cinyarsa ganin Nasir din baya online ya cigaba da driving dinsa, a hankali yake tukin har ya isa gidansa, horn daya ya danna aka bude masa gate din, be shigo ciki ba sai ya tsaya a jikin gate din yana kallon katon gidansa, wani dogon numfashi yaja ya sauke yana kara duba tsarin gidan kamar wanda ya fara ganinsa a yau, maganar nan ta dazun ce ta tsaya masa a rai, how on earth za a ce wani be da gidan kansa kuma be da kudin da zai iya biya ya kama haya? Mai gadin ne ya zo gurin motar ya dan risina yana daga masa hannu.
“Ranka ya dade lafiya dai?”
Ya tambaya dan a tunaninsa ko shi yai masa wani abun da ba daidai ba. Kallonsa kawai Aliyu yai ya dauke kansa yaja motar zuwa harabar gidan yai parking.
“Shiyasa take yin bara take wankin mota a titi aikin maza?”
Ya furta yana fitowa daga motar, be san dalilin daya hana shi jindadi ba jin cewar su Ataa basa da gida har sun raba a wani gurin an koresu, he know be cika damuwa da sha'anin kowa ba but wannan ya tsaya masa a rai for no reason.
“Zata iya jefa kanta a matsala saboda kyauta”
Ya fada yana ta tuna fuskarta, dagon hancinta manyan idanuwanta masu kamar madara ga gashin daya gani a bayanta duk kuwa da kasancewar ba a gyare yake ba amman dai ya fahimci tana da long hair.
‘Ina ruwana da halin da zata jefa kanta, ni dai abunda na sani an cuceceta and ya kamata na fahimtar da ita abunda akai ba laifin mu bane that's all, babu ruwana da wani rayuwarta can be ma kamata nai wannan tunanin ba’
Sai ya ji kamar darajarsa ta rage taya ma zai yi wannan tunanin tun a farkon fari, rufe motar yai ya nufi kofar shiga falon wayarsa a hannunsa daf da zai shiga wayar tai vibration sai ya shiga ya samu kujerar da ta baya stairs baya ya zauna yana mayarwa Nasir da amsar sakon da ya turo masa.
“Zan saka a bincika, amman Momy ta san da maganar kuwa?”
“Kai dai ka saka a bincika kawai, idan an ganta ka fada min zan fada maka next abunda za ayi”
“Za a bincika In-Sha-Allah”
Thanks.
Yana rubuta masa haka ya kashe datar ya mike tsaye sai ganin Rahma yai a bayansa idonta taf da hawaye har wasu sun fara sauko mata, saurin aje wayar yai a kujera ya zagoyo inda take ya dafa ta.
“Minene?”
“I was such a fool da na yi tunanin ba zaka iya son yarinyar nan ba, ashe ita kaje nema? Yanzu kuma ita za aka saka Nasir ya nemo maka? Why Aliyu? Kazamar yarinya kamar wannan”