← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 143

Sashe 51

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da ya bar asibitin gidansa ya koma ya, yana shiga ya samu guri ya kwanta ba dan yana jin bachi ba sai dan ya samu sauki abunda ke zuciyarsa, matsalar iyeyen Rahma da kuma ciwonta a dayan bangaren kuma ga Ataa ta ta tsaya masa arai a yanzu yake tunanin ta ina zai fara taimakonta, what is best now is ya taimaki mahaifiyarta ta samu lafiya, sai dai be san ta inda zai samu mahaifiyar ba domin be san inda take ba, and Ataa bata bashi wata dama da zai iya sanin Familynta ba, sai dai yai ma kansa alkawarin zai taimake ta tai shiga rayuwarta ya nuna mata halinsa mai kyau da be taba nuna kowa ba, wata kila hakan zai sa ta aminta dashi har ta bashi damar sanin inda mahaifiyarta take, and ya ma kansa alkawarin ba zai sake bari a takura mata a cikin gidan nan ba, shine mataki na farko da zai dauka. Haka dai yai ta tunaninsa ta bangaren Rahma kuma idan ya fara sai ya rasa ta ina zai tuke, zancen neman wata kodar a yanzu be ma taso ba, ba dan kudi ba sai dan gudun kar a samu irin wacan matsalar idan kuma ba a samo mata wata ba, hakan na nufi nan da wani lokaci zata mutu kenan? Ko kuwa akwai wani magani da za a bata wanda zai saka kodar ta samu lafiya, ya kamata ya san wannan, idan ma zaa samu kodar a yanzu to dole ne sai ya ga mai ita kuma ya yi magana da mai ita ya aminta, da kuma amintaccen likita ba kamar Doc Asim ba. Idan kuma ba za a samu ba ya zame masa dole ya cire tashi daya ya bata domin yana son ganin matarsa a raye, and zai iya sadaukar mata da komai na sa ciki kuwa har da ransa idan da dama.
Yana kwance Siyama ta kira ya ga kiran amman ya ki ya daga domin ba shi da time din wani magana ko wani abun dabam a yanzu, sam ya manta da zancen zuwan Momy ma tsabar tunanin daya saka a gaba. Bathroom ya shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin wasu kayan ya fito yana ta kamshin turare ya sauko kasa ya nufi wata motar dabam ba wacce ya shigo da ita ba ya shiga ya dauki hanyar asibitin.
  Ko da ya shiga dakin da Rahma take ya same ta zaune saman gadon mahaifiyarta kuma akan kujera suna ta kuka, ba a fada masa ba, ya san cewa mahaifiyar Rahma ta fada mata gaskiyar ciwonta. Ganinsa yasa mahaifiyar ta tashi tana share hawayenta ta fice daga dakin shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar da ta tashi tana ta kallon yadda Rahma take kuka. Hannunsa ya kai ya kama hannunta yana fadin

“An fada miki gaskiyar ciwonki kenan?”

Sai ta kalleshi cikin hawaye ta ce.

“Ina son rayuwa Aliyu, amman rayuwa bata so na, tun ina karama na ke ta fama da matsalar kodar nan, ima gidan aurena aka cire min daya saboda ta lalace, dayar ma aka ce sai an samo wata a dasa min, duka yaushe aka min kashen koda da har za a ce wannan ta lalace?”

Tashi yai ya koma saman gadon kusa da ita ya zauna ya ja zuwa jikinsa ya rumgume cike da tausayinta....Gyara kanta tai a kirjinsa tana hawaye.

“Babu abunda Allah ya rage ni da shi sai lafiya da haihuwa, ina da Uwa Uba yan'uwa miji duka a raye kuma duka suna so na, amman ba ni da lafiya kuma ban haihuwa, yanzu idan na mutu na zama mai yankaken baya kenan?”

“Za ki samu lafiya Rahma sai mu cigaba da neman haihuwar ki daina zancen nemam haihuwar nan a yanzu”

“Wata kila zan iya samun ciki na haihuwa ban mutu, amman zancen samun lafiya na warke kamar kowa na san ba zan taba samu ba, a da na yi zaton na warke idan aka dasa min wannan kodar amman sai gashi yanzu kuma ance ta kone”

“Dan ta kone ba shi yake nufin ba zaki rayu ba, kika sani ko ki samu sauki mu cigaba da rayuwarmu”

“Samun sauki ba abu ne mai sauki ba Aliyu, samun saukina yana nufin samun wata kodar, kai ma kuma na san ka fara gajiya da ni, Mommy ta fada ka ce ba za a sake samo wata kodar ba...”

Dago kanta yai ya rika fuskarta.

“Ban ce ba ba a sake samun wata ba, amman dai ba ta bangaren Asim ba, saboda gudun abunda ya faru ya sake faruwa”

“Amman da ada ne kome zai faru ai zaka aminta ya faru ni na rayu, amman a yanzu ka canja wata kila ka fara gajiya da ni ne”

“Taya zan gaji da ke Rahma miyasa bakinki zai rika furta irin wadannan kalaman? Ai nasan da ciwon ki kuma na aureki a haka neman kodar nan da akai har aka dasa miki ita ba wayayi ba ni ba? Idan na gaji da ke ai ba zan dauki duk wannan dawainiyar ba, amman maganar gaskiya ba zan sake yarda a cutar da wata saboda ke ba, zam iya komai dan ki rayu amman ba zan kashe wani ko na gulgunta rayuwar wani saboda ki rayu ba, ba kuma zan yarda a cire ko da kowa dan zalinci a dasa miki ke ki rayu ba, ko da kuwa hakan na nufin idan ba a saka miki ba ba zaki rayu ba, ba zan zalinci wani na raya ki ba Rahma duk kuwa da irin son da nake miki I'm telling you this form the bottom of my heart, sai dai zan yi dawainiya da ke har ki samu lafiya”

“Ko kuma na mutu ba, saboda kai ka san zaka iya auren wata mata idan bana raye amman ni na tafi kenan. What if maybe kana daukar dawainiyata ne saboda kai baka haihuwa ni kuma ba ni da lafiya, sai mu taru a haka mu mutu? Ban san yadda zaka dauki abun nan ba Aliyu, amman lokacin da ba Mommy ta fada min cewar koda ta ta kone, mutuwa ce farkon abunda ya fara zuwa min a rai, da kuma haihuwa idan na mutum ban bar baya ba, na tafi kenan, amman idan na haihuwa zan iya barin abunda za a rika tunawa da ni idan ana kalleshi”

Murmushi Aliyu yai irin murmushin nan da yafi kuka ciwo, yau wai Rahma ce take fada masa wadannan kalaman yasan tana son haihuwa kamar yadda shi ma yake sonta, tabbas mai irin matsalar ta zai son ganin zuri'arsa ko ba dan mutuwa, shi kansa yana son haihuwa amman gudun shiga damuwarta yasa shi kawarda tashi. Iyakar abunda zai iya yi a yanzu nuna mata kalamanta basu bata masa rai ba, domin idan har ya bari bacin ransa yai tasiri akansa zai iya fada mata magana marar dadi ko kuma yai fushi da ita wanda yake ganin hakan be dece ba a yayinda da take cikin rashin lafiya. Ba karamin kokari yai ba na kai bakinsa yai kissing goshinta kamar yadda ya saba yana sauke ajiyar zuciya a hankali.

“Ki kwantar da hankalinki idan kin samu lafiya za mu nemi haihuwa”

“Wata kila matsalar da daga ni ne, da yanzu Mama Fulani da Momy sun saka ka kara aure saboda ka haihu, domin ko wannensu yai min gorin haihuwa, amman da yake ka boye musu gaskiya kace dukanmu ba mu da matsala sai suka daga min kafa suna ganin kamar wata rana zan iya haihuwa, ni ma haka na ke ta saka rai ni da iyayena shiyasa na dage gurin neman magani ashe matsalar ba daga ni ba ne”

Sakinta Aliyu yai ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu ya tsaya gaban windows dakin yana kallon waje zuciyarsa na masa mugun kuna. Rahma kuma ta bishi da kallo tana hawaye, har ga Allah tana son Aliyu kuma tana kaunarsa amman matukar ta tabba matsalar daga shi ne dole zata hakura da shi ta auri wani saboda ta samu haihuwa domin ba zata yarda ta bar duniya ba tare da ta bar baya ba, and tana da tabbacin wata kila da ita ce da matsalar da ba zai zauna da ita ita kadai ba, da yanzu ya yi aure ko ma ya rabu da ita gaba daya kamar yadda mahaifiyarta ta fada mata a lokacin data labarta mata gaskiyar cewar matsalar daga Aliyu ne a wacan lokacin kamin rashin lafiyar ta kamata. Sai dai me wata kila idan babu Aliyu a rayuwarta ba zata iya rayuwa ba, wata kila ba zata iya komai idan babu shi ba, domin ta shaku da shi kuma tana kaunarsa irin kaunar da ba zata iya misaltawa ba.

Aliyu be juyo ba har sai da yaji an taba kofar dakin an turo an shigo. Momy ce ita da siblings dinsa. Yayi kokarin boye damuwarsa amman ya kasa har sai da Momy ta karanci yana cikin damuwar a fuskarsa. Ita kuma tai saurin share hawayenta tana kokari kirkiro murmushi, tsaye sisters dinsa sukai suna mata sannu Momy kuma ta zauna a kujera tana ta duban yanayinta da na Rahma. Aliyu ya yi farincikin ganin Momy domin be tsammaci za tai saurin zuwa a yau ta duba Rahma ba saboda yawan complain din da take cewar Rahma bata son zuwa inda take, sai dai be yi mamaki ba dan yasan halin Momy da dattako da kuma maida komai ba komai ba.

“Yanzu kuka zo?”

Aliyu ya fada yana kai hannu ya riko hannun Inteesar, sai ta dawo kusa da shi ta tsaya tana dariya.

“Tun dazun muka zo, ai na saka Siyama ta kiraka baka daga ba”

“Na ga kiranta amman ban dauka tare ma muka zo ba, na dauka rokonta ne ya tashi”

Sai dai duk sukai dariya ban da shi da yai maganar, sam ba zaka kalleshi ma ka ce shi yai maganar ba, daman haka yake ko abun dariya ya fadi na kasafai yake dariyar ba.Bayan sun gama ganinta Momy ta kallesu ta ce.

“To ai sai ku wuce ku koma, kar likitocin su zo suce mun yi yawa, kuma mun baro Fulani ita kadai gashi beta gama fucewa ba”
Chapter 51 · 0% Book details