← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 143

Sashe 35

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama Fulani ta fada tana kallon cike da kyama daga can saman dinning da take zaune ita da yaranta suna karyawa, ba musu na nufi garejin na cire hijab dina na saka dankwali a kaina wanda hakan ya bayyana gashin kaina da na yi masa tsoro daya ya sauko har gurin mazaunaina. Da na tashi ban dawo part din Mama Fulani ba sai na wuce part din Ammy da alama ita ce da girkin tsakanin jiya da yau, domin ban same ta a falonta ba sai Anty Zee tace min Ammy tana part din Abbah amman ga abincin nan ta aje min, farfesun kaza ne a wani karamin plate sai wainar kwai da dankwalin turawa a plate daya da kuma katon burodi, da tea a wani babban kofi, duka an hade su a tray daya. Daukar tray nai zan fita sai Anty Batulu da ke murzawa fuskarta wani farin mai mai kamar sabulu ta ce.

“Ina za ki je?”

“Waje zan je na zauna na ci?”

“Zauna a nan ki ci?”

“Ammy ba zatai fada ba idan na ci a nan? ”

Sai duk suka saka min dariya.

“Hala Mama Fulani ta miki fada da kika zauna a falonta?”

Anty Zee ta tambaya sai nai kasa da kaina ban ce komai ba.

“Ammy ba ruwanta, idan ma muka saba sai ta fi son ki da mu,ba kamar wacan bakar matar ta ke ba”

Anty Zee ta fada sai Anty Batulu ta kalleta.

“Anty Zainab Ammy ta ce ki daina cewa haka”

“Ke na fada tashi kije ki Fadawa Ammy ki ce na ce Mama Fulani mai bakin hali, munafuka kawai”

Tana fadar hakan ta tashi ta nufi upstairs tana jan tsaki. jin hakan yasa na zauna a kasa na soma cin abincin hankalina a kwance har na ci na koshi, rabon da na ci abinci da naman kazan tun asibiti lokacin da Doc yake siya mana na restaurant, duk sai na ji babu dadi ina ma ace Nana na kusa da ni da na bata naman ta ci, sam bana son na ci wani abu mai dadi ba tare da Nana ba, hakan yasa na yanke shawara na shanya naman idan ya bushe sai na tarawa Nana idan naje sai na sake dafa mata shi ta ci.

“Anty Batulu zan iya shayawa idan na koshi”

“Eh to sai idan Garden za ki shanya shi, inda kowa ba zai gani ba”

Tana bani amsar na tashi tare da ragowar naman na koma gareji na dauko wani dankwalina na nufi garden din na shimfida daga inda rana take haskawa na baza naman sannan na dawo part din na gyara ko'ina kamar yadda nai a part din Mama Fulani. Bayan na gama gyaran Ammy ta shigo part din jin kamshi na tashi yasa ta murmushi tana ta yaba min.

“Kai haka na ke son yarinya da kuzari kazar kazar da ke, ai to za mu shirya kuwa idan kina son aiki ba kamar yaran gidan nan ba, manya da su amman sai dai a gyara suna zaune”

“Ai daman Anty Zainab ta fada cewar nan da kwana biyu sai kin fi son ta da mu”

Anty Batulu ta fada tana dariya, ni ma nai murmushi sai Ammy ta nufi upstairs tana fadin.

“Eh mana to me ake da mu”

Bata dauki lokaci ba ta fito rike da tufafi kusan kala biyar ta miko min.

“Ungo idan kin yi wanka sai ki canja naga jikinki sun dan tsufa”

Cikin wata irin murna da jindadi na saka hannu biyu na karbi tufafin ina godiya.

“Allah ya saka da alheri na gode sosai”

“Ba komai”

Cike da jindadi na nufi garejin dan ajewa, kasa hakuri nai har sai na yi wanka na saka sai na soma gwadawa ina ta jujjuyawa rabon da wani yai min kyautar tufafi har na manta, kana ganinsu ka san masu tsada ne, na san ba zai wuce na Inteesar ba, domin ita ce kamar ni ganin yadda tufafin suka min cif kamar daman can nawa ne. Sam na manta da zancen gyarawa Ya Muhseen part dinsa har sai da na koma Part din Mama Fulani sai ta rufe ni da fada tana ta zagina kamar wacce bata san inda na fito ba.

“Gidan uban wa kika je kika zauna? Ba na ce ki je ki gyarawa Muhseen part dinsa ba? Shine dan kin maida ni shashasha kika tafiyarki ko? Zo nan”

A tsawa ce take min fada kamin ta ce na zo, ni kuma duk tsoro ya kamani jikina nata rawa kamar nazari idona har ya fara hawaye, domin na fahimcin kiran da take min dukana za tai.

“Aa ni nace ta bari sai gobe”

Ya Muhseen ya fada yana kashe min ido daya, kasancewar duka yan 'uwansa basa nan daga ita sai shi ne a dinning din.

“Ko?”

Sai na gyada kai.

“Eh haka ne, shi yace na bari sai gobe”

“Yaushe ka ce mata haka?”

“Dazu, dauki ga abincin ki can”

Ya karasa yana nuna min kasa kusa da Mama Fulani. Sai na kasa zuwa na dauka ina ta jin tsoro shi kanshi ya lura da hakan.

“Mama gaskiya tsoron ki take”

“Tsorona dodo ce ni?”

Ta daka min tsawa. Sai na amsa mata da sauri ina girgiza kai.

“Aa”

Ya Muhseen ya tashi ya nufi inda abincin yake ya dauko ya miko min yana dariya tare da fadin.

“Ko ni da kika haifa a tsoronki na ke balle kuma ita”

“Aa ni ban haife ka ba, dana ya can sokoto Aliyu dan albarka”

Mama Fulani ta fada tana mikewa tsaye daga dinning din. Sai Ya Muhseen ya saka dariya

“Kowa ya ganshi ai yaga danki halinku daya Mama, har ya fiki rashin tausayi”

“Kanka ake ji”

Ta fada tana tabe baki sannan ta nufi kitchen, shi kuma ya miko min abinci ina karba tana fitowa daga kitchen din tana fadin

“Idan kin ci abinci ki aje wannan plate din da cup din a gurinki, da shi za a rika saka miki abinci”

“To”

Sannan na juya na fita, tea a cup din sai wainar kwai da dankalin turawa a plate din da burado kadan, ban ci komai ba kasancewar na riga na ci na bangaren Ammy na koshi, sai kawai na aje a garejin na kwanta a saman tabarma ina ta tunanin Nana, ko a wane hali take yanzu oho, gashi ba ni da waya balle na kira ta ji muryarta.
After like one hour har bachi ya fara daukata na ji an taba garajen ina dagowa sai na ga Ya Muhseen cikin shiga ta kananan kaya ya dora rigar likitoci a sama, kayan sun karbe shi sosai ga fuskarsa da far'a yana aiko min da murmushi, ni ma murmushin nai masa kadan na tashi zaune.

“Zo ki bude min gate”

“Ba akwai mai gadi ba?”

“Ke nake son ki bude min”

Na tashi kamar yadda ya bukata ina gyara daurin dankwalina na fito daga garejin na nufi gate din, sai da na wuce gate biyu sannan na iso a babban gate din nai ma mai gadin magana ya nuna min yadda ake budewa na bude sannan na hango shi ya taso motar ya nufo inda nake tsaye da gudu kamar mai shirin kade ni, ni ko na ratse gefe na rufe ido ina jiran ya kade ni sai kawai na ji ya saka min ya jefeni da chocolate. Murmushi nai na duka na dauki chocolate din ina kallonsa.

“Sarkin tsoro, daman saboda na gwadaki nai kuma na ga gashin nan na ki”

Ya fada sannan yai gaba abunsa, ni da mai gadin muka bi shi da kallon mamaki, ni dai ina jin son barkwancinsa da yadda yake da son wasa da ni. Mai gadin ya riko dayan gate din ni kuma na riko dayan za mu rufe na ji an ce.

“Ke”

Juyowa nai sai na hango wani fari saraurayi tsaye jikin wani katon gate da ke facing din na su Mama Fulani yana sanye da uniform din sojoji. Ba musu na saki gate din na nufi inda yake tsaye cikin mugun tsoro domin Allah ya zuba min tsoron soja fiye da dan sanda.

“Ina wuni”

“Ina kwana dai”

Ya gyara min yana murmushi.

“A can gidan kike?”

“Eh"

“Gurin wa kika so?”

“Aiki na ke a gidan”

“Aiki?”

Ya maimaita, yana kallona kasa da sama.

“Wa kike yi ma aiki? Mama Fulani ko Ammy?”

“Dukansu”

Na amsa muryata na gargada.

“Ki daina jin tsoro ba wani abun zan miki ba. Ya sunanki?”

“Aisha”

“Ashe mamana ce ke, kina da kyau Aisha ke fulani ce?”

“Aa buzuwa ce”

“Shiyasa kike da kyau sosai ga gashi, an taba fada miki kina da kyau?”

Na shiru ina yin kasa da kaina sai yai dariya.

“Kar ki ce ban saba ganin kyawawa ba, na saba ganinsu ni ma ai kin ga na fiki kyau ko?”

Na dan dago na kalleshi sai ya shafa kansa yana dariya.

“Sunana Kamal Isma'il Isa, nan ne gidan mu kuma ni soja ne, idan kikai wani abu sai na kama ki, dan haka ki yi hankali”

Ya fada yana fiddo yar karamar bindigasa ya nuna ni da ita, aiko ba shiri na ranta cikin na kare cikin wani irin gudu da ban taba sanin ina da shi ba na zarce cikin gida, ina waigensa ya biyoni yana ta dariya.

*Littafin nan na kudi ne*
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
19.

Nasir ya fada masa a unguwar da ak fada masa ya sa an bincika amman ko fulani ba a samu a unguwarba balle wasu buzaye, zancen wani ja gini duk karya ce.
Jin wannan yasa Aliyu ya zabi ya cire nemanta da kokari fahimtar da ita idan ya ganta a ransa, tun da be san inda take ba, and gashi garin nemata har suna kokari mom samun matsala da Rahma, and idan ma yace dole sai ya nemota ya ai wani sabon aikine a gareshi, but he know one thing for sure tunanin zalincin da akai ma yarinyar nan ba zai taba fita a zuciyarsa ba, kyauta kuma ba zai taba gushewa a idonsa ba.
Chapter 35 · 0% Book details