← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 126

Sashe 72

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya bar sashin Mummy, ya je ya ga Sabir, Ammi ta yi masa ya jiki, tayi masa addu'a kamar yadda ta saba, sannan ya tashi ya tafi.

Kasancewar a cikin garin, gidan Jamil yake, ya sanya ya biya gidan Jamil, sai dai ya tarar baya nan.

Yau ya ji
warin jikinsa sosai, dan haka ya shirya dan tafiya aiki, ya saba idan da makaranta, shida da rabi, rumaisa za ta zo gyara masa
aki, idak bai tashi ba ma, ta din ga
wale-
wale kenan sai ya tashi ko baya so.

Amma har ya fito breakfast, ko alamunta bai gani ba.

Kai tsaye ya tafi
akinta, tana zaune dirshen da kayan bacci, ta cika akwatu da kayanta, tana zugewa.

"Ba zaki shirya tafiya makaranta ba ne?"
"Eh na daina zuwa, gidan matsiyatan iyayena zan koma, in cigaba da zuwa wadda na saba zuwa, sannan in cigaba da cin irin abincin da na saba ci, ba irin wanda nake ci a nan ba ake yi mini gori"
"Dalla tashi ki shirya zan makara"
"Sai kuma ka yi, ni za a din ga yi wa gori, saboda rashin adalci irin naka, da son kai, ka
ora mini laifi, kai
annenka ba sa laifi, wallahi ko ta katanga sai na haura na koma gida" tayi maganar cikin tsan-tsar takaici.

"Na baki mintuna goma, ki yanke shawara, idan kin za
i mu rabu, abu ne mai sau
i, amma ki sawa ranki, ba zaki sake ganin Sabir ba, har abada mintuna goma kawai gareki" saroro ta yi, ta bishi da kallo har ya fice.

Ko mintuna bakwai yi ba, sai gata cikin uniform, kamar zata fashe.

A ransa ya ce "Ni zaki yi wa zuciya, bayan na san lagonki?".

Suna tafe a hanya ya saya mata alawar madara, dan ya san tana son harkar madara.

Ta ce bata so, bai kulata ba ya ajiye a kusa da ita, suna zuwa
ofar makaranta, ta bu
ofar motar ta
au alawarta ta fice.

Yayi murmushi ya ce "Su mimi ba zuciya in dai a kan kwa
ayi ne" tana jin sa a ranta ta ce "So ka ke in kulaka, kuma ba zan kula ka ba".

Ana tashinsu ya je ya
aukkota, ya wuce da ita gidan Ammi, ya ajiyeta ya koma wurin aiki, tana jin da
in hakan nan, saboda yana
ebe mata kewa sosai, duk da su Iman na makaranta, ta yi ta hira da Ammi, tana wasa da Sabir.

Ammi ta ce "Rumaisa, ashe su Fauziyya ne suka je gidanki jiya?"
Rumaisa ta ce "Eh Ammi, sun je jiya da yamma"
"Ina fatan dai ba wata matsala"
Rumaisa ta ce "Eh Ammi babu komai, sun je duba shi baya nan"
Ammi ta yi murmushi tana dafa kafa
ar ruma ta ce "Ashe mutuniyar tawa tana girma, da har take iya
oye abu.

Ban san dai meyafaru ba, amma na san ba zasu je su dawo haka ba, sai sun yi miki wani rashin albarkar.

Babarsu ta zo
azu tana ta masifa, wai takawa ya je ya ci musu mutunci a kanki, kamar ba
an uwansa ba".

Rumaisa ta waro ido ta ce "Papan?

Amma ni kuma jiya yayi mini wula
anci, suka
ata
aki wai ni zan gyara".

Ammi ta ce "Ki yi ha
uri, ki cigaba da kula da kanki, ban da surutu a gaban wani"
"To Ammi in sha Allah"
Ammi kuwa da
i ne ya kamata, ganin alamun soyayya a tsakanin rumaisa da takawa, yadda suka din ga turjiya kan ayi auren, ba ta tsammaci haka ba bayan auren.

"Yauwwa, Ammi dan Allah kira mini mama mu gaisa, ke da ita duk kun
i zuwa gidanmu".

Ammi ta ce "Bari na kirata, to me zamu zo mu yi muku, ku ba gashi kuna zuwar mana ba".

Ammi ta kira mata mama, ta bata wayar sannan ta tashi ta fita.

Mama na yin sallama ta ji muryar ruma, mama ta ce "Ahh babar sabir,
ar gidan amminta"
Ruma ta ce "Mama na tabattar kin daina so na gaba
aya, baki ta
a zuwa gidana ba".

"Ai na san kina lafiya ne, ya
an naki ya maigidan?"
ana lafiya
alau, maigidan kuma mun yi fa
a bama magana"
Mama ta ce "Kun yi fa
a ba kwa magana saboda baki da hankali?"
Cikin sangarta ta ce "Mama fa
a yake yi mini a kan abun da ba laifina ba"
"Yi mini shiru, dan me ba zai yi miki fa
a ba, ya fita ya nemo ya kawo ki ci,
an uwanki sun ce mini baki nemi komai kin rasa ba, kuma dan yayi miki fa
a sai ki daina yi masa magana?

Idan ma daina yi miki maganar yayi, ke ba zaki yi masa ba?

Kin ga ki kiyayeni".

"To mama kawai sai na bashi ha
uri"
"Kar ki bashi, zan nemo masa wata matar mai
a'a, tun da ke ba kya ji"
Rumaisa ta ce "Mama ban gane ba, to wallahi ammi ta ce ba zai
ara aure ba, daga ni shikenan".

"Kar ki canza hali, na fasa zuwa gidan naki ma, sai kin yi hankali"
Kan ta yi magana, mama ta katse wayarta, ruma ta ajiye wayar tana tura baki.

Tayi shiru tana nazarin maganar mama, ba
arya duk abun da take so yana bata, ko bai amsa mata ba, za taga abun ya bata.

Kuma ga ammi ta ce ya je ya yi wa
annensa fa
"Ai shikenan, zan daina fushin, amma ba zan bashi ha
uri ba"
Har yamma tana gidan Ammi, sai magariba, sannan takawa yayi waya, ya ce Sidi ya mayar da ita gida.

Yawan zuwan nan da take yi, ya sanya ba ta damu lallai, sai an bata sabir ba, saboda tana samun sha
uwa sosai da sosai tsakaninta da Sabir
in, da kuma Ammi, gashi akwai fahimta sosai tsakaninta da iman, sannan a hankali take
ara sanin kan masarautar, dan wataran idan ammi za ta fita, binta take yi.

Tana tsaye tana
arin shiga motar sidi, sai ga mahmud.

"Daughter, ina ta so mu ha
u da ke"
"Ai ban san kana nan ba, da sai na nemeka".

"Kin san bana zuwa ko ina.

Jiya mijinki ya zo sashinmu, yayi wa Mamana rashin kunya, saboda su Fauziyya sun je muku gida"
Rumaisa ta ce "Ai gara shi, kishiyar mamansa ya yi wa, wanda yayi wa maman sa fa"
"Ba wannan maganar muke yi ba, idan muna irin wannan maganar, raina zai iya
aci.

Yanzu dai ina zaki?".

"Sidi ne zai kai ni gida".

"Duk an yi mini kashedin na fita harkarku, amma ba zan iya ba,
aukko mini Sabir sai na kai ki gidan, na dawo ni da shi"
Rumaisa ta ce "Babu lallai ammi ta bani shi, sai da ka zo mu je tare"
"Ina son yaron nan sosai daughter, mu je"
Tare suka koma Ammi ta din ga kallon Mahmud, Ruma ta gaya mata abun da ya ce, ammi ta ce "Banda abun sa ai shi ma
an sa ne, Allah ya tsare"
Ruma ta yi ta murna, ta
auke shi suka fita, Mahmud ya kar
e shi, suka shiga motarsa suka tafi.

Nusaiba ta ce "Ammi, kina ganin babu wata, ko takawa ya zo yayi fa
a?".

Ammi ta
an yi shiru sannan ta ce "Yarinyar nan ta zarce duk yadda nake zato, ko da ba ta gaya mini ba, na san
ari take ta sasanta tsakanin Adam da Mahmud, tun da ni na gagara yi, ban sani ba ko ita Allah ya sa ta iya, dan haka ba abun da zan iya, yi mata Addu'a, tare da goyon baya
ari bisa
ari"
Nusaiba ta ce "Ikon Allah, ammi kuma fa haka ne"
"Ku tayani addu'a, a dalilinta sau biyu Mahmud yana zuwa in da nake, in sha Allah ko bai dawo wurina gaba
aya ba, sai an samu daidaito tsakanin iyalina".

Nusaiba ta ce "Allah ya sa".

Har
ofar gida ya kai rumaisa, suna tafe suna tattaunawa a hanya, yadda za su fallasa baba uwani, domin sai an katse hanyar kaiwa Mummy sa
o, da samu hanyar dakatar da wasu ayyukan na Mummy.

Rumaisa ta sauka, shikuma ya tafi da shi da Sabir.

Sai wajen goma na dare, sannan takawa ya isa gida.

Rumaisa tana fallo tana kallon cartoon, kamar yadda ta saba.

Sallama yayi da kaya a hannunsa, ta tuna mama ta ta
a cewa, a zamaninsu idan miji ya dawo gida da kaya a hannunsa, jiki na rawa suke tashi su kar
Cikin basarwa, ta tashi ta mi
a hannu za ta kar
a, ya kalleta ya ce "Kin ci abinci ne?"
"Na ci a gida".

Ya ce "Dafo shayi cup biyu, ki sameni a
aki"
Ta jinjina masa kai, ta tafi kitchen.

Kan ta dafa ta dawo, har yayi shirin kwanciya, sai dai yana gefen gado, yana danna waya.

Ta ajiye cup da flaks
in, za ta fita ya ce "Zauna ki ha
a mana"
Su ruma da yake ba kowacce bisimillah take wucewa ba, ta zauna ta ha
a tea cup biyu.

Gasashshen nama ne, da
aton bredi, ba kunya ta saka hannu tana ci, tana basar da shi, ita dole ba ta daina fushi ba.

Hannu ya sa, ya matse kumatunta ya ce "Can't you smile, or say thank you?

Kin shanye mini alawar madara, kuma kina wani kumbura baki"
Tura baki tayi, ta cigaba da kora shayi, suka gama ciye-ciye, ta tashi zata kwashe kwanuka ta fita.

"Zauna zamu yi magana".

Ta zauna tana lashe hannu.

Ya
aukko tissue, ya goge mata hannun.

Sannan ya dubeta ya ce "Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je
aro karatu, na tsawon watanni shida.

Wannan asabar
in in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure".

"Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba?

Kuma wai ka tafi ka barni nika
ai?"
Takawa ya ce "Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta"
"To sai in daina ganinka?".

"Kina son ki dinga gani na ne?"
Ta ce "Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka"
Yayi murmushi ya ce "Abokin gabar naki?
Chapter 72 · 0% Book details