← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 126

Sashe 11

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce "Hmm mai sunan baba ai sai dai Allah ya shirya,
a ne gasu nan kowa da halinsa, ki yi ha
uri kin ji iman, ban ji da
i ba wallahi"
Adam ya ce "Ammi lokaci fa, ina son yau zan kwana a gida, zan yi wani aiki".

Ammi ta ce "Haka ne, dare ya fara yi, rumaisa, ba zan fasa godiya ba, ubangiji Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sanya muku albarka, sauran magana duk yadda ake ciki zan yi magana in Allah ya yarda.

Suka fito tsakar gida, takawa ya kalli rumaisa wani takaici ya
ule shi, wannan fitsararriyar abar ce zai aura.

Yaya Abubakar ne ya shigo, ammi ta kalleshi ta ce "Malam faruku kai ne ka razana mini
a ko?

Kuma ka ce baka son in ha
a auren
ana haba mai sunan baba laifin me muka yi haka ne"
Abubakar ya yi murmushi ya ce "Ina wuni"
"Lafiya
alau ya gida ya
ari?"
"Alhamdilillah"
Iman ta
ura masa ido, kamar ba wannan ne mai muryar nan ba.

Mama ta ce "
an uwan mai sunan baba ne, shi gashi can a bayanki yana jinki, wannan dattijon arziki kenan malam habu"
Ammi ta ce "Au, ashe fa
an biyu ne ai ni duk kama suke yi mini" ta waiwaya ta kalli mai sunan baba ta ce "Mun zo neman aure gidanku ka hana, a sassauta adawar nan ba a san in da rana za ta fa
i ba, ina da tarin
an mata a gidana kar ka zo neman aure nima na rama".

Suka yi dariya gaba
aya, mai sunan baba ya
an sunkuyar da kai be ce komai ba.

Ammi ta
ora da "Dan Allah ayi mana addu'a, na samu duk sun amince in sha Allah lamarin nan alkhairi zai zama, tun da Allah a ka nufa da lamarin, ba za aji kunya ba, karatun rumaisa da komai zamu kula da shi, kuma adam zai ri
eta cikin mutunci da kulawa, mu sanya a ranmu wannan ha
in Allah ne, a tayamu da Addu'a".

Mai sunan baba ya ce "Allah ya tabattar da alkhairi "
Ammi ta ce "Amin ya haiyyu ya
aiyyum, yauwwa mai sunan baba ko kai fa, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarku, ya baku mataye nagari sanyin idaniya, ya tsare mana ku daga sharrin zamani".

Ya amsa da amin.

Abubakar ya ce "Hajiya babu wata damuwa, har kullum alkhairi muke fata, kuma dama babban burinmu bai wuce rumaisa ta yi ilimi, sannan ta samu abokin rayuwa nagari ba, Allah ya sanya ha
in nan ya zama alkhairi".

"Amin ya Allah, na ji da
i sosai na gode da karamcinku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya yayi muku jagora".

Adam har ya fara
ulewa, gaba
aya ya gaji so yake su tafi, har ya je ya kunna mota, amma ammi tana ciki tana ta faman hira.

Iman tuni ta bi bayan Adam ta shige cikin motar, sai sauke numfashi take, saboda ba
aramin razanata mai sunan baba yake yi ba.

Aka yi sa'a mama ta yi musu sallama ta fito, ma
wabtan su rumaisa har sun fara surutun, yawan zuwan da mota daban-daban take yi
ofar gidan su rumaisan.

Suna tafe a hanya ammi tana fa
in "Alhamdilillah, na ji da
i an gama da wannan babin, gobe in Allah ya yarda zan je na samu turaki, sai dai dole mu yi shiru da bakinmu, babu wanda zai ji wa za ka aura, sai Allah ya kaimu lokacin".

Adam a ransa ya ce "Sai ka ce wata matar arziki, ni dan ta ni ba wanda zai san ma an yi auren, wannan har wani aure ne"
Ammi ita ka
ai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana sa
e-sa
ensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka
arasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi.

Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba
aya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a
akin mama ya ce "Ya muka yi da ke?

Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko?

Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi.

Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin
alubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki
arata".

A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake fa
uwa.

"Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin
addarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wata
ila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wata
ila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah"
Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba.

Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha.

Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na
an bashi lokaci tukuna"
"Amma har zuwa yaushe tukuna?

An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback"
"To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa"
Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon"
"Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya
addara sai ya fara aurenta ne"
"A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman
in, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman".

"Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa"
"Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam"
alo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil".

"Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya"
"To Allah ya sauwwa
Ya amsa da amin ya fita.

Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba
aya ba ta da karsashi yau, abinci ma da
yar take ci.

Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa"
Ruma ta
ago ta kalli mama.

"Meke faruwa ne?

Ki ci Abincin mana"
Rumaisa duk
aunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na
oshi tafiya zan yi"
Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta
arasa ta zauna a gaban mama.

"Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh.

"Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da
an unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu"
Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?"
Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi".

"Dan Allah mama ki gaya mini"
"Ba zan fa
a ba tashi ki tafi, karki makara"
Ganin mama ba ta da niyyar fa
a mata, ya sanya ta
au jakarta ta fice, ta
udurce a ranta sai ta san ko menene.

Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana
wala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta
araso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?"
Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan"
"Amma meyasa, kin ha
ura da kar
an?"
"A'a, zan kar
e shi"
"Hmm kin ji abun da ake ta cewa a kan ki ko, wallahi ma
ociyarku munafuka ce"
Cikin mamaki rumaisa ta ce "Me ake cewa?"
Habiba ta ce "Au baki sani ba?"
"Ban sani ba"
, to da suka je asibiti dubaki, suka ga
a, suke cewa wai
anki ne, cikin shege ki ka yi, aka kai ki garinku ki ka haihu, yanzu an sallamoki kin dawo gida babu jaririn wata
ila kasheshi ku ka yi"
Galala rumaisa ta bi habiba da kallo ta ce "Cikin shege kuma?

Kamar yaya, to ai ko a gurin
an bindiga, bana yarda su ta
ani, sai dai bisa tsautsayi ya za ayi ciki ya fito mini na haihu, na yi abun kunya fa kenan,
an anty aisha ne fa ta mutu ta bar mini shi"
Habiba ta ce "To wallahi duk wadda aka ce ta yi cikin shege, to
ar iska ce"
Rumaisa ta yi tsaki ta ce "Sai su yi ta yi ai, na tafi kar na makara,ke ma ki tafi makaranta"
Habiba ta ce "To shikenan, amma dai wallahi ma
wabciyar nan ta ku munafuka ce"
Rumaisa ta yi gaba, sai dai maganar Habiba ta din ga yi mata yawo a ka.

Har ta je makaranta ta dawo, ba ta cikin nutsuwar ta, mama ba ta kawo komai a ranta ba, sai rumaisa tana cikin alhini ne kawai na batun auren nan, ita kuwa rumaisa tuni zancen aure ta ajiye shi a gefe, zancen da habiba ta yi mata ya cigaba da damunta.

A islamiyyar ma kasa sakin jikinta ta yi, maganar ta cigaba da ci mata zuciya.

Har a yanzu rumaisa ba ta da takamaiman ajin da take zama, duk in da yayi mata kawai tafiya take zauna.

Yau ma a ajin su Yasir take, ta matsa ku sa da wata
aliba, duk
an ajin mata da take mutunci da su, yayata take ce musu.
Chapter 11 · 0% Book details