← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 126

Sashe 57

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan masifar da ha
ilon, idon rumaisa mursisi, ba ta yi dana sanin abun da ta aikata ba.
akinsa ya wuce da ita, ya rufe
ofar gam, ya tanka
ata kan gadonsa, ta zauna da
as, ita kokowarta kar towel
in ta ya fa
asa.

"Ki gaya mini me ki ka sani game da mutuwar aisha, da saceta?".

"Wai ya ka ke tamabyata kamar ni na sace ta?

Ni ban san komai ba, ni ma fa sace ni aka yi".

"Amma kin san wani abu, akwai abun da ki ke
oye wa, atleast a bayaninki akwai wani abu da zai taimaka, na gane idan saceta ha
in baki ne".

Ta ce "Oho, ni dai ban san komai ba, zanena kawai nake yi, idan kun ji haushi, tun da ku jami'an tsaro ne ku din ga aiki tsakani da Allah, ni ka daina yi mini masifa, ba abun da na sani".

Cikin matsananci fushi, ya ce "So ki ke na illataki ko?

Idan ki ka bari na yi miki illa, na yi wa banza, ke zaki nakasa ba ruwana.

Kin san muhimmancin aisha a wurina kuwa?

She don't deserve, such kind of death, ki yi mini bayani kan na yi miki illa"
A karo na biyu ta sake kawar da kai, ta na zum
ura masa baki.

"Kalleni"
"Ni ba zan kalleka ba, kai baka ganin abun da yake fitowa daga idonka?".

Ba ta yi tsammani ba, ta ji ya ri
e gashin kanta ya ja, sai da ta kusa shi
ewa, ta mi
e tsaye tana
arin
wacewa.

Ga mamakinta, sai ta ga fuskarsa ma ta fara ba
i, duk ya yi wani iri.

A take mafarkin da ta ta
a yi, ya fara
arin zama gaskiya, dan faratansa ya fara karta mata a wuyanta, ya kuma sha
eta ya na wani irin kakari.

Da fari su barira sun biyo bayan baba uwani, baba Uwani ta kasa kunne a jikin
ofar, ta na jiyo abun da suke cewa, sai dai tun da rumaisa ta yi
ara suka ji shiru.

Jiki na rawa barira ta ce "Baba uwani, ko mu kira masu gadi, a ceto ta, kar ya yi mata illa".

Baba uwani ta ce "Ke ina ruwan ki?

Dalla ku wuce ku je ku cigaba da aikinku"
Rumaisa kuwa bayan ya yi mata wannan sha
ar, sai da
ta suma, ya saketa ta fa
asa, sannan ya yanke jiki ya fa
i a gefenta, cikin yanayi mai kama da bacci.

Asiya kasa nustuwa ta yi, ta ce "Barira, tsoro nake ji fa, kar ya kasheta, ko police station aka kaimu bayar da shaida an cucemu".

"Bari kawai, wallahi nima a tsorace nake, ga matar nan ta hana a nemo taimako".

Asiya ta ce "Bar
ar rainin hankali mana".

"Ita ma dai, ta na da azabar taurin kan tsiya, ni ina girki kawai na ga ta shigo da gudu, ta tura abu a wuta, zan yi magana ta ce in yi shiru, sai ga shi ya biyo ta, amma na ji yana magana a kan Aisha, wata
ila abu ne mai muhimmanci da ya shafe ta".

"To waya sani, ni dai fatana kar ya illata kawai".

Bayan sa'oi uku, Adam ne ya fara yin juyi, dan ji yake kamar barci yake yi, kawai ya ga rumaisa a kwance a
asa, ita daban towel
in ta daban, da ga ita, sai gajeren wando.

Tashi ya yi zaune yana
arin tuna abun da ya faru, kawai dai ya iya tuna yadda ya janyota har
akinsa, amma daga nan komai ya goge a kansa.

Tsura mata ido ya
an yi, yana tunanin ko barcci take yi ne?

Amma sai ya ga yanayinta bai yi kama da haka ba.

'Ko wani abun na yi mata?' ya tambayi kansa.

Matsawa ya yi kusa da ita, ya
agota, ya ga jikinta a sake.

A gigice ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, i lose my sense again?" Rabon da ya fita completely daga hankalinsa haka, an kai shekaru goma, ko ya yi loosing control, ya na iya tuna abun da ya faru, amma completely yau ya kasa tunawa.

Wuyanta ya kalla, duk shedar an karceta da farce.
an girgiza ta ya na kiran sunanta.

"Rumaisa!" Amma shiru ba ta motsa ba, ya ta
a hannunta, ya ji zuciyarta na bugawa, numfashi da take yi a hankali.

Ya kwantar da ita ya shiga ban
aki, ya
ebo ruwa a hannunsa, ya dawo ya shafa mata a fuskarta, ya
ure gudun Ac da na fanka.

Bai
aura mata towel
in ba ya
yaleta, ya lullu
e ta da shi, ya tsura mata ido yana fatan Allah ya sa ta farka, dan kuwa idan ya
auketa ya kai ta asibiti, asirinsa zai iya tonuwa, dan babu lallai ta yi shiru, kuma dole a tambayi mai ya sameta, ya cigaba da addu'a Allah ya sa ta tashi.

Babu tsammani, kawai ya ga ta tashi zaune, tana ganinsa ta ja da baya, ta kare jikinta da hannunta.

Sai a lokacin ya yi ajiyar zuciya "Ki
aura towel
in mana" ya fa
a a sanyaye.

"Dole ka ce na
aura mana, bayan ka yi mini tsirara, za ka kasheni, wallahi gida zan gudu, ba zaka kasheni ba?

A hakan zan gaya maka abun da na sani
in?

Dama ban san komai ba ma, wallahi ba zaka kasheni a banza ba, ka sha
eni kamar wata
arauniya".

A hankali ya ce "Ya ilahi, i attempt to kill her?'
Ta saka hannu ta ja towel
in, ta rufe jikinta, ta yin
ura ta tashi, ta fice daga
akin.

A hankali ya lumshe idanunsa, ya bawa hawayen da suka taru a idonsa damar zuba, ba zai so ammi ma ta ji wannan maganar ba, iya rayuwarta a hanyar nema masa magani take, ana murna abu ya
an yi sau
i sai abun da ba a rasa ba, kwatsam yau abu ya dawo kamar da.

Sai ya ji tashin ciwon nan nasa, ya shafe abun da rumaisan ta aikata masa.

"Mahaukaci ne ni?

Ko kuma maye?

Ko kuma namiji mai mutanen
oye, wato aljanu?" Tambayar da tun da ya shekara takwas a duniya, yake yi wa kansa da ya gaza samun amsarta.

Ba shi da tabbacin rumaisa ta rufa masa asiri, haka zalika bai san ta ina zai fara yi mata bayani, ta fahimce shi ba, sai a lokacin yake ganin rashin kyautawar da aka yi, na rashin yi musu bayanin larurarsa.

Madigar kuwa ta na zuwa
akin ta, gado ta hau ta cigaba da bacci.

Baba uwani kuwa, ta fita ta zagaya, jikinta na tsuma, ta kira lambar Mummy.

Aka yi sa'a mummy na kusa, ta
ag wayar, gulma na cin ta ta ce "Allah ya taimake ki"
"Ina jin ki".

"Akwai abun da ya faru".

"Je ki kai tsaye".

Baba uwani ta waiwaya sannan ta ce "Ranki ya da
e, muna cikin aiki muka ga ya biyota afujajan, a kan wani littafi, sai dai kan ya cimmata ta tura shi a wuta, na ji yana magana cewa, abun da ya shafi aisha ne, baki ga sha
ar da yayi mata ba,
arshe dai ya shiga da ita
akinsa, ya rufe su, sai yanzun nan ta fito".

Mummy ta ce "Good, kin fuskanci ya yi mata wani abu ne?"
"Ban san me yayi mata ba da ya rufe su, amma na ga ta fito tana kamar magagin bacci".

"Kin sanar da samha ne?"
"A'a Allah ya baki nasara".

"Kar ki sanar da ita komai, sai abun da na umarce ki".

"In Allah ya yarda".

"Ki koma, ki cigaba da sanya mini ido a kan duk wani motsinsu".

Baba uwani ta ce "An gama uwar
akina".

Ta katse wayar ta koma.

Adam kuwa ya yi sallar azahar, ya jingina da jikin gado, ya yi shiru yana tuna abubuwan da suka shu
e, gaba
aya jikinsa ya yi sanyi.

Kiraye-kirayen, sallar azahar ne ya tashi rumaisa, ta je ta yi alwala, ta saka kaya, ta tsaya a gaban mudubi, ta na kallon wuyanta, da ya shata yake mata zafi.

Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta ta
a ganin wannan abun a mafarki, ko kuma ya ta
a faruwa.

"Wallahi sai na gaya wa mama, tun da kasheni zai yi, sai na gudu na bar gidan nan"
Can kuma sai wata zuciyar ta tunatar da ita, muddin mama ta ji a kan meye, ya yi mata abun da yayi mata, ba zata goya mata baya ba, fa
a za su yi, a bata rashin gaskiya, kuma a kirsheta ace sai ta fa
i abun da ta sani, bayan ta riga ta ce ita ba ta san komai ba.

'Subhanallah, na fasa fa
a, bari na yafe masa, wataran ya na da kirki, amma wallahi ko zai kasheni ba zan fa
a masa komai ba, sai lokacin da na ga dama, bari na lalla
a na san yanzu ji yake kamar ya kashe ni' sai kuma ta
an yi shiru ta ce "To da ya sha
e ni kuma sai na yi bacci, oho dai?

Ta gama abun da Allah ya nufe ta da yi, ta yi salla ta fito dan yunwa take ji.

Adam ya tashi ya nufi
akinta, domin ya duba ko ta na lafiya ta gama wartsakewa, sai dai ya jiyo motsi a kitchen.

Ya le
a kitchen
in, ya hango ta taka kujera, tana saka
an wake, kamar babu abun da ya sameta.

Abun har mamaki ya bashi, kamar ya yi mata magana, sai kuma ya fasa ya fita.

Baba Uwani na ganin fitar Adam, ta lalla
o ta hawo benen.

"Sannu
ar nan, ina fatan bai yi miki komai ba?"
Rumaisa ta waiwayo ta kalli baba uwani ta ce "Yayi mini me?".

"Ai ganin yadda ya janyo ki
in nan, abun ya tsoratani, ke ma da ko me yake bu
ata kin bashi kin wuce wurin, idan ransa ya
aci hankalinsa gushewa yake wasu lokutan, zai iya yi miki illa.

Ko dai hakkinsa ki ka hana shi ne?"
Rumaisa ta juyo gaba
aya ta kalli baba uwani ta ce "Wane irin ha
i kuma?".

"A'a ha
in aure mana".

"Meye ha
in aure kuma?"
Baba uwani ta ce "Ahh shikenan, bari maganar kawai".
Chapter 57 · 0% Book details