← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 126

Sashe 33

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu me ki ke ganin za ayi masa wanda za'a tarbe shi da shi?"
Kai tsaye ta ce"Ruwa"
Abdallah da yake jiyo maganar ta su daga tsakar gida ya shigo, ya ce "Mama, ita fa wannan yarinyar taki, kamar namji take ba ta san komai na rayuwa ba, sai an karanta mata yadda yakamata".

Ya kalleta ya ce "Ke, ki nutsu malama, aure zaku yi, so muke idan ki ka tafi kin tafi kenan, ba zaki dawo mana gida ba, dole ki din ga yi wa mutane abun da ya dace, har zancen ma zan koya miki.

Yanzu mama ki kawo ku
i, mu sayo kayan meat pie, in taya ta mu yi, sai a ha
a masa da lemon roba da abinci"
"Duk shika
ai?

Gaskiya ni ba zan iya aikin wani meat pie ba, bacci zan yi, ni idan ya zo ma ban san me zance masa ba?

Sai dai Huzaifa ya rakani, ko Yasir"
Abdallah ya ce "Ka ga shashasha, tashi ki je ki yo cefanen meat pie
in nan"
Gaba
aya rumaisa ga rasa gane dalilin da ya sanya, kowa laifinta yake gani a kan Adam, kowa so yake lallai sai ta kyautata masa, haka mama ta saka baki, aka aiketa sayen kayan meat pie da za a kar
i Adam.

Abdallah da Huzaifa suka sakata a gaba, a kan aikin, amma ta
i mayar da hankali,
arshe su suka yi aikin suka
Yaya Usman ne ya dawo, ya tarar da su Abdallah suna ta kai kawo, an yi girki, kamar dai wani abu mai muhimmanci na shirin faruwa.

"Wai lafiya na ga ana ta wani shiri, ko bikin aka fara tun Yanzu babu labari, abu na masu hannu da shuni"
Huzaifa ya yi dariya ya ce "Yaya Usman, sirikin ne zai zo, yau zai fara zuwa zance, shi ne ake shirya masa abinci, kar azo a ji kunya.

Gara mu
kankaro kanmu, sai dai ita yarinyar ce ba ta da hali, ana saita ta a hanya tana fizgewa".

Usman ya nufi
akin mama yana fa
in, "ubanta kuwa za ta ci wallahi, dole a saita ta. ke kina ina?" Yayi maganar yana shiga
akin mama, rums ta yi
ai tana kallon Tv, tana cin kantu mai gishiri.

"Ba zaki tashi ki fara shiri ba, yaushe ya ce miki zai zo?"
Rumaisa ta
aga kai ta kalli Usman ta ce "Oho masa"
"Ke ina yi miki magana, kina amsa mini a haka, tashi zaune"
Rumaisa ta tashi zaune tana
ata rai.

Mama da ke gefe ta ce "Ai gara ku shiga cikin lamarin, tun da ni ba zan gaya mata ta ji ba".

Usman ya ce "Aikuwa da ni take zancen, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki yi masa rashin mutunci, ko wannan cin maganin, sai na yi miki bugun sakwara, ko ki zauna kina wannan
ata ran, ki na kumbura baki zaki ga yadda zan yi da ke"
"To ni yaya usy ya zan yi? ku fa ku ka ce mini ba ruwana da maza, ni ban ta
a zance ba ban san me ake cewa ba, sai dai Huzaifa ya rakani, ni tsoro ma nake ji".

Usman ya ce "Au idan aka yi miki auren ma, huzaifa ne zai biki gidan mijin, ya tayaki zama da kula da mijin?".

"Ni ba zani gidan kowa ba, sai dai shi ya dawo nan gidan ya zauna, kuma bada Sabir kawai zan kula ba, shi
ato da shi me zan masa?"
Huzaifa ya ce "Ki ce auren Bollywood za ayi, ayi aure miji ya tare a gidan su mata, yarinya sai dai kar ki yi zancen, idan ni zan rakaki".

Usman ya ce "Ni bari na koya miki abun da zaki ce, ya za ayi wani huzaifa ya raka ki, ya ji kalaman soyayya ya dawo yana tsokanar ki".

Ta kwa
e baki ta ce "Soyayya kuma?"
Usman ya ce "Eh mana, au da
iyayya?" Ta yi shiru, tana kallon Usman.

Ya ce "Idan ya zo, ba
ifi-
ifi zaki yi da ido, kina kallonsa kamar fusatacciyar kyanwa ba, ya ga alamar girmamawa a idonki, idan ya zo sai ku gaisa, ki tambaye shi ya mamansa, da
annensa da Sabir.

Cikin mutuntawa ba da zazzare ido ko harare-harare ba, ki na yi kina sunkuyar da kai, ban da tsyawa ki
ure shi da ido, na sa cikin naki, duk abun da ya tambayeki ki bashi amsa, ba cikin tashin hankali da masifa ba, sai dai idan kin ga yayi miki wani abu da ya sa
a shari'a da tarbiyyar da aka baki, sai ki zo gida ki gaya mana".

A ranta ta ce "Sa
a shari'a da tarbiyya na nawa kuma, dan dai kawai kar na zubar masa da mutunci ne, amma da sai na gaya wa kowa abun da ya yi mini".

Muryar Usman ce ta dawo da ita hayyacinta, da ya ce "Kin ji abun da na ce ko kuwa?".

"Na ji" ta amsa da
yar.

"To tashi ki je ki yi wanka, zan din ga yi ina zagawa in ga yadda ki ke zancen, idan ki ka kuskura, ki ka aikata abun da na hanaki, a gabansa zan tuburbu
aki".

"To yaya usy, ni fa na yi wanka da safe"
Huzaifa ya ce "Sokuwa, wannan wankan tarbar masoyi ne, wankan ganin baby".

"Allah ya kiyaye na ce masa wani baby, kamar wata
ar iska, sunansa Adamu"
Usman ya saka hannu, ya talle mata
eya, sai da ta kusa kifawa.

"Shashasha, ana koya miki abu kina iskanci, ki je ki yi shirme a auren, zaki gane baki da wayo, tashi ki je ki yi wanka" tashi tayi ta dafe
eya, ta fice daga
akin.

Mama ji take kamar ta yi dariya, yayyen sun zauna suna koyawa
anwarsu, yadda ake yin zancen.

Mama ta ce "Malam usman wannan lakcar, anya ba a zagaya zauruka da magariba?

Ba a ta
a bani labarin sirikar tawa ba"
Usman ya sosa kai ya ce "Mama a wurin abokaina nake ji".

Mama ta yi murmushi ta ce "Ba zan hanaka ba, ni dai fatana aji tsoron Allah, kar a din ga zuwa rage dare wurin yaran mutane, alhalin ba aurensu za ayi ba".

"Mama kar ki kawo komai a ranki ma, ba wurin da nake zuwa"
"Idan ma ana zuwan dai, ai dole na yi kashedi" Usman ya din ga murmushi yana sinne kai.
****
Iman tana zaune a kan gadonta, ta sunkuyar da kai, gefe Nusaiba na zaune, sai kuma jabir da ya saka Iman
in a gaba da kallo, kamar zai ha
iyeta.

"Talk mana iman ko na ji da
i, saboda an ce baki da lafiya ban gama abun da nake yi ba, na baro Germany, na zo na dubaki kuma kin
i magana, talk please"
Nusaiba ta ce "Please iman, stop treating our uncle J this way, ki yi magana mana".

Cikin sanyinta ta ce "Anty Nusaiba, maganar ce bana so in general, bana jin da
i sam"
"Amma duk da haka bai kamata ya yi ta magana ki yi masa shiru ba"
an kalleshi ta ce "Am sorry".

"To ya zan yi da ke jarumata, bana son yadda ki ke yi mini wula
anci, idan wani abun na yi miki am so sorry for it"
Ta girgiza kai ta ce "A'a babu komai"
"Shikenan, na ga kamar ina takura miki, bari na je gida, Nusaiba take a good care of her please"
Nusaiba ta ce "To uncle J, but you have pay for the service"
Yayi murmushi ya ce "Biyoni mu yi ciniki, za a biyaki ko nawa ne" ta yi murmushi ta tashi ta bi bayansa suka fita.

A hankali iman ta furta "Ohh Allah, ka iya mini, Allah ka yi mini za
i na alkhairi, Allah kar ka saka Jabir ya gayawa wani yana sona, he has no space in my heart.

Ni ba kowan kowa ba ce, duk za
in da ka yi mini ina so Allah, Allah ka iya mini" ta
arasa maganar tana kwanciya a kan pillowanta.

Sai dai tana kwanciyar, ta ji tamkar an sanys igiyar
arfe, an
aure mata jijiyoyin kanta, ta sanya hannu ta dafe kan ta fashe da wani marayan kuka, ta rasa me ma za ta yi, lamarin nan ya fara bata tsoro, dan kuwa ji take tamkar zata haukace.

Jabir ya kalli Nusaiba ya ce "Nussy, see how your sister is behaving towards me, just because i have feelings on jer, me yasa ba ta so na, meye aibu na?"
"Uncle J, yakamata ka yi mata uzuri, this girl suffer alot in this family, kalli yadda take samun manema, suna tafiya saboda abun da mutane basu da tabbas a kan sa, kalli saboda yarima ya ce yana son ta, kalli wula
ncin da fulanin yola ta yi mata da cin mutunci, har a gidan nan ma ba ta tsira ba, na waje ma idan sun biyota suna so, sai a samu mai zigasu su daina zuwa.

A yanzu ta riga ta ce ba ta son kowa ya ra
eta da sunan soyaya, ba ta son kowa, ka san abu na
arshe da ya faru a gidan nan ai, ba wanda bai ji ba, shi ma aka din ga surutu a kai.

Dan haka ta ce idan har mijin aurenta ya zo ko ba soyayya, ta ce za ta yi, amma for now, tana bu
atar hutu ne".

"Nusaiba, babu
an adam
in da baya fa
i tashi da gwagwarmaya da
addara, amma hakan ba ya sanya wa a sare, this is not an excuse da za ta yi denying kowa ya ce yana son ta, ni da gaske ina son iman, amma wace shawara zaki bani a kan ta?"
Nusaiba ta numfasa ta ce "Uncle J, ga ka da takawa, ga ka da Ammi, ai a duniya babu abun da za su ce ta yi, ta
i yi muddin bai sa
awa shari'a ba, ka bi ta wurinsu kawai, ina fatan idan komai yayi daidai, zaka kula mini da iman, ka kuma ji tsoron Allah a kan ri
on ta".
Chapter 33 · 0% Book details