← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 126

Sashe 68

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen ha
ora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini.

Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank
in sa ya fi na Jamil.

Akwai aiki da
ari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai.

Bashi da aiki banka
a, da tonawa mugwayen
asa asiri.

A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa
asa
arna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka
aramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka
i bashi goyon baya, a hukunta wakili.

Shi kuma ya
i sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya
i ji.

Ya koma ya banka
o wata tawaga, da suke yi wa kansu la
abi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a
ungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na haya
i, an rubuta THE SMOKE.

Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji
ishin walili zai tsayar da
an sa takarar senator, shi kuma za a
auke shi vice president, su yi takara, da
an takarar da zai tsaya shugabanci
asa.

Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu.

Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya ha
a tasa tawagar, da lauyoyi, da ma'aikatan Efcc, da
an jarida da suke da burin yi wa
asa aiki saboda Allah.

Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna ri
Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta
wafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal.

Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta.

Saurayin babbar
ar Mummy, Surayya, Wambai ya ha
ata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so.
arshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu.

Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a
an mai martaba,
aya shi ma ya li
e Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan.

Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane.

Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama.

Iman ba ta da wata
awa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar
akinta Aisha matar takawa.

Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta ta
a nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah.

Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son
an ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take.

Wambai ya yi ta fa
a ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne.

Cikin ikon Allah, Iman kan ta yi candy, wani
anin abokin Adam ya fito zai auri iman,
an babban gida ne sosai da sosai, aka saka rana tana kammala sakandare ayi biki, ta cigaba da karatu a gidansa, dan Ammi ta fara tsorata da mazan da suke bin Iman.

Adam kuma shekara hu
u da aure, ciki ya gagara zama a jikin Aisha, ciki na
arshe da ta samu, Ammi suka yi shawara a kan Aisha ya je ta yi rainon cikin a saudiyya, wurin wani wan Ammi da yaki zaune a can shi da matarsa.

Ya ce karatu za ta tafi
arowa
asar waje, aka din ga surutu a kai, ya ce babu mai tsara masa rayuwarsa, tun da matarsa ce.

Iman kuma watan da za a yi biki, wanda zai aureta ya aiko a kar
ar masa kayan aurensa wai ya fasa.

Hankalin ammi ya tashi, ta aika a tambaye shi dalili, iyayensa suka ce su manyan mutane ne a
asa, ba za su kar
i sirika da ba ta da asali ba.

Ammi ta sha kuka, laila da ba ta
asar ma, abun ya ba
anta mata rai, ta cewa Ammi visa za ta yi wa Iman, a tura mata ita can, Ammi ta ce ba mai rabata da
ar ta sai mutuwa ko aure.

Ammi ta yi shawara da baba uwani, a kan ta bata shawara ko ta ro
i Mahmoud ya auri Iman, dan ta lura wannan mugun tabon da Mummy ya yi mata, ba zai bari ta auru ba, baba Uwani ta ce ai ita babarsa ce, dan haka bakomai.

Daga nan ta kwashe ta je ta gaya wa Mummy.

Ammi ta keta billenta, ta je ta samu Mummy, ta ce mata dan Allah ta na son yin magana da Mahmoud, ta ce mata za ta turo shi.

Sai dai kan ya je, Mummy ta zauna ta kitsa masa, tare da sauya masa tunani.

Ammi ba zata iya tuna rabonsa da sashinta ba.

Ta ro
e shi Allah ma'aiki, ya auri Iman, ko ita ka
ai ce alfarmar da zai iya yi mata a rayuwa a matsayin ta na mahaifiyarsa.

A take ya
ashe
asa, ya cewa Ammi shi ma ba zai auri
ar da ba ta da asali ba.

Ba
in cikin abun da Mahmud ya yi mata, ya sanya ta kamu da hawan jini, saboda ta yi kuka ba ka
an ba, ta shiga damuwa.

A lokacin Adam ya je umara, ya ga Aisha, cikinta ya girma sosai, ana ta addu'ar Allah ya sa ta haife shi lafiya, bayan ya dawo ya samu labarin, abun da ya faru tsakanin Mahmud da Ammi, ya din ga yi wa ammi mitar meyasa za ta ro
i Mahmoud ya auri Iman, ita kuma gani take ba ta da wata mafita sai wannan.

Ammi sai da suka kwanta da Iman a asibiti, dan ta so Al'amin saurayin da ya fasa aurenta, haka zalika ta so ta samu Mahmoud, duk da yana cikin wa
anda take bala'in jin tsoro, saboda dukan da yake yi mata da hantara idan sun ha
Kuma zance ya fita a dangi, Giwa ta na neman kai da shegiyar
ar ta, ta
i auruwa, kuma ta karya billenta ta nemi alfarmar
an ta, ya
i yi mata.

A zahiri za ka ga ammi kullum cikin fara'a take, amma
asan zuciyarta, tana cikin damuwa da tashin hankali a kan iyalanta.

Gaba
aya jikin rumaisa ya yi sanyi, ta rungume Iman da take ta shar
ar hawaye, ta rungumeta ita ma ta fara kukan, ta kasa rarrashinta.

Sai da suka yi mai isarsu, danna rumaisa ta din ga share mata hawaye ta ce "Ki yi ha
uri Anty iman, tun da dai ammi ta san iyayenki, meyasa za ki damu dan an ce miki baki da iyaye?

Ki fuskanci rayuwarki kawai, kuma in Allah ya yarda zaki auri miji na gari, wanda zai kula da ke, ki daina kuka"
Ta yi maganar tana sharewa iman hawaye, Nusaiba ta yi sallama a
akin, suka amsa, ta
an yi turus tana kallonsu, yanayinsu ya nuna mata akwai wani abu, amma ta share, ta
arasa ta
au Sabir da ya yi barci, ta fice daga
akin".

Jabir kuwa rai a
ace ya koma
akin Ammi, ya dubi ammi ya ce "Ammi, dan Allah idan ban takura miki ba, ina son mu yi magana ne".

Ammi ta ce "To" ta tashi ta bar
akin, Adam ya bi su da kallo.

Falonta suka koma, Ammi ta ce "Ya aka yi ne?"
an sunkuyar da kansa
asa, sannan ya numfasa ya ce "Ammi wani abu ne ma da
e ina son in gaya miki, amma na kasa ban sani ba ko zaki bani dama".

"To ni
in ba
uwar ka ce?

Fa
i ina jin ka".

"Dama..dama game da Iman ne Ammi, dan Allah idan babu wani a
asa yanzu, ni a bani mana, ina son ta".

Ammi ta ce "To fa!

Babbar magana, ya aka yi ba ka gaya mini tun da wuri ba?".

"Ina jin nauyi ne Ammi".

"To meye na jin nauyin ban da abunka, ka san yanayin da take ciki, ta daina saurarar kowa ta daina bawa kowa dama tunda abubuwan nan suka faru, amma na yi mamakin da baka ta
a fa
a ba".

"Ammi Iman ai
anwata ce, na da
e ina
oyewa ne, yanzu kuma na ga yakamata na fa
a, wata
ila dama rabona ce".

"Haka ne, amma ka san dai case
in da yake kanta, kuma babu lallai hajiyarka ta yarda, na san ba za ta amince ba".

Jabir ya ce "Ammi zan shawo kan ta, in dai kin amince shikenan, idan har ba a cikinmu ba, haka zamu zauna mu cigaba da zuba ido, kowa ya zo ya fasa, Saboda wani dalili mara tushe, ina ga ni
in na fi dacewa, na san abun da yake faruwa da ita".

Ammi ta ce "Na yi farin ciki sosai Jabir, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ai kai
ana ne, na gode da
arin share mini hawaye ni da marainiyar Allah, Allah ya biya ka".

"Amin Ammi, na gode sosai, ina ga zan yi wa mai girma wambai Magana, a nema mini aurenta, zan yi
ari ya shawo kan Hajiyata ma".
Chapter 68 · 0% Book details