← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 126

Sashe 120

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan haka sai ka za
aya, fito na fito da masu
asa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba.

Sai dai fa ka yi ha
uri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin
asa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza.

Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai ta
a furta sunana ko na
a na ba.

Dan haka gara ka watsar da duk wani yin
urinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama
aita ku" ya katse wayar.

Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.

Ruma ce ta mi
e tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?"
Gabanta ya
arasa, jiki a matu
ar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi
arfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin
warin gwiwa.

Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode.

Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wata
ila ba dan ke ba, ba zan gane bara gurbin da suke rayuwata ba" Hawaye yake zubarwa kamar
aramin yaro, cike da
unar zuciya.

Lallai fa
a da aljani ba da
i, shiya san bai isa cigaba da fito na fito da wannan mutanen ba, in dai a Nigeria ne, mutane sun san ta'addancin Smoke, sai dai basu san suwaye ba, kuma wani abun shaidar rumaisa kawai ba zata wadatar ba, hakazalika da rayuwar rumaisa ta salwanta gara ko menene ya ha
ura da shi, yarinyar tayi sacrificing alot".

Rumaisa ta dur
usa ta ce "Papa dan Allah ka tashi, ka sakani a duhu, ni ban gane me ka ke nufi ba, ka tashi dan Allah, a gaban mutane ne fa"
Mahmud ne ya tashi ya kama Adam, ya mi
ar da shi tsaye, ya ja hannunsa ya cewa rumaisa su tafi.
an sanda suka tattara duk wasu bayanai da suka kamata, wanda rumaisa ta bayar, da zanen Abdallah da aikin da Yasir yayi, Bashir ya kar
e ya ce sai sun kammala na su binciken tukuna, zasu gani idan da yiwuwar ba wa
an sanda.

Wambai kansa ya girgiza da jin lamarin, tausayin
an uwansa turaki ya kama shi.

Sosai babar Jamil ke kuka, tana cewa turaki ya saka baki, ya
aryata abun da suka fa
a, ya sanya a saki Jamil.

Wambai yayi mata tsawa, ya ce su tashi su tafi sai ya sake nemansu.

Mummy godiya ta yi wa Allah, da ba a fa
i komai a kanta ba, Hajiya Lubabatu ta zube tana yi wa wambai magiya ita ma a kan a taimaka a sanya baki, a saki Jabir.

Mummy ta ce "Wallahi ba ta isa ba, ba zai lalata mata
a ya ci bulus ba" jin abubuwa babu Allah a ciki, dagulewar lamuran yayi yawa, ya sanya wambai cewa su tafi su je su
arata a wurin
an sanda.

Sai da ya rage daga shi sai turaki, sannan turaki ya samu zubar da hawaye, ya da
e matar nan tana citar da shi da Aisha, amma ba ya iya
aukar mataki, dama tun a farko rumaisa ta gaya masa komai, sai dai bai tabattar ba sai a yanzu.

Wambai ya dafa kafa
arsa ya ce "Ina neman afuwarka
an uwana, na rashin tsayawa in fuskance ka a abubuwa da dama.

Dama na san biyayya ce ta sanya ka auri Sa'adatu, sai dai wannan abu ba kai ka
ai ya shafa ba, zan yi iya
arin ganin cewa maganar nan ba ta fita ba"
"Kar ka yi haka, ko kayi hakan, ko ba kayi hakan ba, dole sai maganar ta fita, Allah ya ji
an fulani da mahaifiyarta, rumaisa kuma Allah ya yi mata kyakykyawan tukuici da ita da iyayenta.

Mahmud kai tsaye har gida ya kai Adam da rumaisa.

Adam na kwance a jikin rumaisa kamar uwa da
a, sai aikin rarrashin sa take yi, tana bashi ha
uri.

"Rumaisa, ni wakili yake gayawa sai in dai in yi ha
uri, ran matata ya salwanta a banza, saboda wautata da rashin hankali, kuma wai ba wani abu da zan iya yi a kai"
"Ban gaya maka ba?

Na ce zaka iya bincike ne kawai, amma in dai a
asar nan ne, kar ka yi tsammanin samun adalci, mu bar wa Allah papa, you try your best, Allah shaida ne"
Mahmud ya ce "Takawa dan Allah ka daina kukan nan haka, kar ka tayar mata da hankali, ga ciki tana fama da shi".

"Mahmud baka san me nake a zuciyata ba, ba zaka gane ba"
"Na sani mana, saboda sau
a maka ra
in da ni da rumaisa muka yi aiki tare dan sau
a maka aiki.

Ina mai baku ha
urin rashin exposing Mummy, amma ita ma very soon in sha Allah, ka yi ha
uri dan Allah"
Cikin kuka ya sake cewa "Jamil fa mahmud, a
akin Ammi muka yi wasa tare muka fa
i muka tashi, amma ni Jamil zai din ga yi wa wannan cin dunduniyar?

Me nayi masa?

An kashe mini mata kuma ya cigaba da bibiyata da
arin
ora mini sharri?

Me nayi masa ne?"
"Baka yi masa komai ba Papa, hassadar ka fi shi komai ne kawai da kwa
ayin abun duniya ya sanya shi ha
a kai da ma
iyanka, gashi wanda ka ke yi wa kallon ma
iyin, shi ne ya taimake ka, duk lalacewar
an uwa naka ne papa".

"Na gode mimi na gode sosai"
"Dan Allah ka daina yi mini wannan godiyar, ni ba abun da na yi "
Mahmud ya mi
e ya ce "Daughter, ki kula mini da shi sosai dan Allah, zan je gida wurin ammi, na san tana cikin damuwa ita ma"
Ruma ta ce "Wait, wai ba daga gadon asibiti ka taso ba?"
"Rabu da ni na warware "
"Amma ka yadda maman jabir tayi maka wani abu?"
Ya ce "Na yarda, Kamar yadda muka saka Yasir bibiyar wayar Mummy, ya kunna mini wayar da Mummy tayi da Hajiya Lubabatu.

Na kar
i duk wata shaida ta hannunsa, jibi in Allah ya kaimu zai tafi wurin Anty laila, kar ma a samu wata matsala saboda aikin da ya yi mana"
Ruma ta ce "When are you exposing her?"
"Soon in sha Allah"
"Idan ba zaka yi ba, allow me to do it"
"I will in sha Allah" ya juya ya fita.

Haka ruma tayi ta aikin rarrashin Adam, dan abun ya dake shi sosai da sosai, duk iya tunaninsa bai ga ta ina zai iya jayayya da SMOKE ba.

Kuma dolensa ya ha
ura da cigaba da duk wani yin
uri a kan garkuwa da aisha, saboda rayuwar rumaisa.

Kwanaki uku kenan, gidajen sarautar suka shiga
imbin tashin hankali, komai ya damalmale, ba kama hannun yaro, aka gaza samo bakin zaren abubuwan da suka riga suka dagule, Kodayake ba komai ne zai gyaru ba, kasancewar wata
arakar ta samo asali ne tun shekarun da suka gabata, ba tare da an mayar da hankali an gyara su ba.

Kodaye rumaisa ta kawo gagarumin cigaba da kuma gyara wasu abubuwan.

Ba tare da wani cikakken shiri ba, Mahmud ya ce lallai sai Yasir ya tafi canada, Yasir ya so ayi bikin yaya Abubakar yana nan, amma ba dama, aikuwa sai da yayi kuka saboda rabuwa da mama da
an uwansa.

Mahmud kuma ya
arfafa yin hakan ne, kar wani abu ya samu Yasir, saboda aikin da yayi musu, dan a wata fuskar laifi ne abun da ya aikata
in, kutse da satar bayanan mutane ba tare da izinin su ba.

Haka ya tsallaka ya tafi ya bar Nigeria.

Abdallah kuwa Bashir ya ce sai sun tafi da shi Abuja, mama ta tashi hankalinta ganin kamar ana yi wa yaranta
auki
aya-
aya, amma ya bata tabbacin babu wata damuwa, a kan Jamil ne ita ma rumaisa Adam ne zai wakilce ta, saboda tsohon cikinta.

Ranar da zasu tafi Abuja, takawa yayi ta rarrashin ruma, tare da bata tabbacin, Abdallah zai dawo lafiya, tun da har da shi zasu tafi.

Rumaisa suna ta shirin fara Waec, sai dai fa nauyin ciki ya hanata sukuni sosai, tun da ta dawo daga makaranta, mararta take yi mata ciwo da
afafuwanta, kuma takawa ya riga ya tafi, dama ya ce mata idan ba zata iya zaman gidan ba, ta tafi gida wurin mama ko ammi.

Jin ciwo ya
arewa, ta kira Usman a waya, ta ce ya zo zata mutu.

Ya je ya tarar da ita duk a firgice, ta bashi mukullin
aya daga motocin takawa, ta ce ya kaita asibiti.

Suna tafe a hanya ya ce "Ko dai haihuwa zaki yi?"
"Edd
in bai cika ba fa"
Ya ce "Ikon Allah, muna zaune yarinyar da muka goya, muka yi wa wanka za ta haihu, haryanzu muna gararamba, bakomai akwai lokaci"
Bakin rumaisa bai mutu ba, sai da aka ce mata haihuwa ce a asibiti, ita dai ta san lokacin haihuwa da saura, aka ce usman ya je ya kwaso kayanta.

Maimakon ya kira mama a waya, ko ammi, kawai sai ya kira Aliyu da Huzaifa, sannan ya
arasa gidanta, ya
aukko akwatin da ta kwatanta masa, dan tuni takawa ya gama sayen komai na jariri.

Mamaki ya kama nurses
in, suka ce babu wata mace wadda za ta zauna da ita duk sai maza.

Huzaifa ya ce "Hajiya gidanmu ita ka
ai ce mace, babarmu kuma tsohuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, duk abun da mata zasu yi, mu ma zamu yi"
Nurse
in ta ce "A dai duba dangi a samo wata"
Usman ya ce "Hajjaju, wallahi zamu iya komai, ki
yalemu kawai".
Chapter 120 · 0% Book details