← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 126

Sashe 46

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bakomai, Takawa ne ya ce mini, kin fita daga
akina ranki a
ace, kamar baki ji da
in abun da na yi miki ba, ki yi ha
uri dan Allah.

Sannan zan din ga yin aikin saman, zan din ga gyara komai".

Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar
akina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi"
Ruma ta ce "A'a na iya aiki, zan din ga yi da kaina".

Baba uwani ta bi rumaisa da kallo, ta shiga cikin kitchen
in, ta
ebi indomie, da abubuwan da take bu
ata.

"Indomie zaki ci?

Ko in turo barira ta dafa miki".

"A'a na iya girki" ta juya ta nufi stairs.

Mamaki ne ya cika baba uwani, sai a yau ta fuskanci yanayin rumaisa fetsararriya ce.

Ko da rumaisa ta je kitchen
in ta na saman bene, babu gas a cylinder ta, dan haka a kan electric ta dafa indomie da tea ta zauna a kitchen, ta ci kayanta, ta yi wanke-wanke.

"Ke amarya kina ina ne" ta ji muryar Aliyu a bazata.

Da gudu ta fito falon, ta
ane jikin Aliyu tana murna.

Shi da mai sunan baba ta gani, ta saki Aliyu ta nufi mai sunan baba.

Murmushi yayi ya ri
eta da hannu
aya ya ce "Ya kike?"
Take ta fara kuka ta ce "Yaya shi ne ku ka
i zuwa"
"To yanzu ba gamu ba, idan kuka zaki yi zamu koma".

Ta share hawayen ta ce "na daina"
Zama suka yi Aliyu yana ta kallonta yana "Inyee amarsu ta ango, to yanzu ma mama ba ta san zamu zo ba, wai kar mu saka ki kuka, yaya Umar ya ce mu zo mu ganki"
"Aikuwa kuka na din ga yi, yau ne kawai ban yi kuka ba".

Aliyu ya ce "Ke, na ga wasu mata a
asa su waye?".

Rumaisa ta ce "Wai hadimai ne, su suke aikin gidan".

"Saboda me, ke baki iya bane?".

"To ya zan yi, ammi ta ce gidan yayi mini girma ba zan iya aikin nika
ai ba".

"Ke, wannan dattijuwar za ta yi saka ido, kamar mara gaskiya kin ga yadda ta din ga binmu da kallo, wai su waye mu daga ina muke?"
Rumaisa ta ce "Ni ina ruwana, tun da ba a kaina suke ba".

Mai sunan baba ya ce "Da ruwanki mana, ki dai kula da kan ki sosai ".

Sallamar iman ce ta kaste musu hirar, rumaisa ta ce "Yeee, yau ba
ina da yawa"
Idonta bai sauka a na kowa ba, sai cikin na mai sunan baba.

Da sauri ta dur
usa ta ce "Ina wuni"
"Lafiya
alau " ya amsa yana kawar da kansa.

Ta gaida Aliyu ma, ya amsa mata cikin sakin fuska.

Rumaisa ta kar
i Sabir tana murna.

Kamar kullum, tsoro da fargaba ya mamaye iman, kasancewar, mai sunan baba a wurin.

"Anty iman, na zaci ba za a kawo shi ba fa".

"A'a za a kawo shi, amma ba bar miki za ayi ba, sai an ha
a masa kayansa tukuna".

Zuwan Iman ya sanya mai sunan baba tashi ya cewa Aliyu su tafi.

Kamar rumaisa ta yi kuka ta ce "Mai sunan baba baku da
e ba fa".

"Eh, ai mun zo dai, tafiya zamu yi sauri muke yi "
Iman ta ce "Idan saboda ni ne, bari in tafi, takawa ya mayar da sabir
in".

Ta yi maganar tana tashi.

"Meyasa zamu tafi dan kin zo?

Nemi wuri ki zauna ba zama zamu yi ba dama" ya mayar da idonsa kan rumaisa ya ce "Take care"
Daga haka yayi wa Aliyu alamar su tafi, rumaisa ta ce zata rakasu, amma ya ce ta yi zamanta, ya ajiye mata ku
i, suka fice.

Kuka rumaisa ta yi ta yi, iman tana rarrashinta, ita kan ta tana mamakin irin halina bawan Allah nan.

Kasancewar iman na nan, ga kuma Sabir, ya sanya rumaisa ta ha
ura, suka shiga kitchen ita da iman suka yi girki, iman ta tayata ta
ebo wasu daga kayan abinci daga kitchen
asa zuwa na sama.

Iman ta din ga mamakin yadda rumaisa ta iya girki.

Rumaisa ta ce "Hmm, tun ba a barina na yi a gida, in yi in jagwalgwala har na iya, yaya Abdallah tare muke girki, har a YouTube yake ganin girki mu gwada, daga baya na gane girkin wahala ce, na daina".

Iman har bayan la'asar tana nan, baba uwani na yi tana hawa benen, wai ko suna bu
atar wani abun.

Direba har ya zo
aukar iman, takawa bai dawo ba, haka ita ma iman ta tafi, gidan yayi mata shiru da yawa.

Sai yanzu take jin haushin tafiyar su mai sunan baba, ko a waya basu kira mata mama ba.

Baba uwani ta shigo falon da sallama da kayan abinci, ta ce "Uwar
akina, ga abincin mai gida, da naki na dare".

Rumaisa ta ce "A'a ai mun yi girki da iman, mun rage masa".

"To wannan
in a koma da shi kenan?"
Rumaisa ta ce "Eh, abincin ma a daina kawowa kawai".

"Amma saboda me?".

Ruma ta ce "Saboda na daina wahalar da ku, na iya girkin nima"
'Amma ai giwa ba ta ce mana haka ba".

Ruma ta ce "Da gaske nake na iya, kar ki damu"
Baba uwani ta fara jin haushin, rashin yaddar da rumaisa take nuna wa yadda ta
i sakin jikinta da ita.

Rumaisa ba ta damu da sanin dawowa ko fitar Adam ba, idan ba wani abu take bu
ata ba, dan haka har ta yi bacci ba ta san ya dawo ko be dawo ba.

A cikin bacci yake jin kuka sama-sama, ya bu
e idonsa ya ji ana ta
a shi ana kuka.

Ya tashi sosai ya ce "Waye wannan?"
ar siriryar muryarta ya ji tana cewa "Ka tashi zan mutu, dan Allah ka tashi!"
A burkice ya tashi, ya kunna fitilar wayarsa ya haskata, rumaisa ce a tsaye ri
e da hannunsa, tana kuka.

Ayshercool
08081012143
*Paid book ne,
500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu
atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book
in.

Kar ku manta da subscribing YouTube channel
inmu na Cool hausa novels, domin samun da
an litattafan hausa na sauraro, ciki har da
anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please
A gigice ya tashi zaune yana tambayar rumaisa ko lafiya.

Idanuwanta duk sun yo waje, sai sauke numfashi take yi, hannunta
aya ri
e da cikin ta, tana kuka.

"Ki yi mini bayani, menene meya same ki?".

"Cikina ciwo, zan mutu dan Allah ka taimakeni, wayyo mama" a gigice ya sauka daga kan gadon, ya kunna fitila hakse ya gauraye
akin.

Tana dur
ushe ta ri
e cikinta, hankali tashe ya bu
e wardrobe
in sa, ya saka jallabiya, ya
auki mukullin motarsa, ya tafi
akinta da sauri, ya
auko mata hijjabi, ya saka mata, ya ri
o hannunta.
yar take iya takawa, sai yarfe hannu take yi tana kuka, suka saukko
asan benen.

Baba uwani na jin motsi but kamar fitar tusa ta fito, "Ranka ya da
e lafiya?

Meya samu
ar ta wa?".

"Ba ta jin da
i ne, zamu je asibiti".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya sameki haka?"
Rumaisa ba ta amsa mata ba, ta cigaba da kuka.

"Yalla
ai ko biyoku zan yi, ko za a bu
aci wani abu, ba ka tafi asibiti kai ka
ai ba, daga kai sai ita".

Adam ya ce "A'a baba uwani, ki yi zamanki dan Allah, ba sai mun wahalar da ke ba, zan iya kula da ita".

Ya saka rumaisa a mota, ya kunna ya fita.

A cikin motar ma, she was very restless, ta rasa in da za ta sanya kanta, ta juya nan ta juya can, sai kuka take yi.

"Ko dai wani abun ki ka ci ya
ata miki ciki?

Ko kuma abincin da suka yi ne ya saki ciwon ciki, na ji da yaji abincin".

"Nima ban sani ba, cikina zai ha
e da
afata duk ciwo fa suke yi mini, na shiga uku".

"Meye wani kin shiga uku kuma, ki yi addu'a, sannu".

Wani private hospital suka je da yake kusa da su, aka bu
ewa rumaisa file ya shiga da ita.

Suka gaisa da likitan, ya tambayi abun da yake damun rumaisa.

Ta ce masa "Cikina ne da
afafuwana, da bayana na farka na ji suna ciwo, na kasa bacci ciwo suke sosai".

Cikin tausayawa likitan ya ce "Wajen ina ne yake yi miki ciwon?"
Ta nuna masa mararta, ya ce "Kin fara al'ada ne?".

Cikin kuka, ta ce "Meye ma al'ada?".

"Period, ko in ce jinin al'ada" Adam ya bata amsa.

"Ban sani ba ko na fara, amma lokacin da ka watsa mini ruwan kwata, na yi rashin lafiya, na yi fitsari da jini, yaya Aliyu ya ce wai Al'ada ne".

Takawa ya ce "To kuma ruwan kwatar ne ya saka ki ka fara?"
Ta ce "Eh, tun da ai ni da ban ta
a yi ba"
Likitan yayi murmushi ya ce "Za a kai wata nawa da farawar?

Kuma tun daga wancan lokacin kina yi ne, har zuwa yanzu duk wata?".

"Ni fa na manta, cikina ne kawai yake ciwo" tayi maganar tana rimtse idonta.

Adam ya ce "Za ayi watanni takwas".

Likitan ya sake tambayarta, ko da ta yi fitsari ta kuma ganin jinin, ta ce masa a'a.

Yayi counseling
in ta a kan personal hygiene, amma ba ta san ma me yake cewa ba.

Ya rubuta mata magunguna da allurai, Adam ya kar
a ya ja hannunta suka fita.

Ta bashi tausayi ba ka
an ba, lokacin yana tare da aisha, tana gaya masa irin azaba da wahalar ciwon, ita da ta san ciwon kanta ma kenan, balle rumais da hankali bai gama isarta ba.

A dur
ushe haka take tafiya, ya zauanr da ita, ya sayo magungunan, suka je ayi mata.

Sai dai ta ce Allah karta ba za a bu
e mata jiki a ganta a gaban Adam ba.
Chapter 46 · 0% Book details