← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 126

Sashe 64

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunanta Bintu,
ar wani babban malami ce a garin, shigaban manoma na wannan yankin, dan haka ya na da rufin asiri.

Babanta ya na
aunar fura da nono, akwai wata riga da take zuwa sayo masa, duk juma'a, a titi suke ha
uwa da Sharif, ya
auke ta a babur su tafi cikin rigar nan, Bintu ta saba da su sosai, bafulatanar da take sayen nonon a wurinta, ta mayar da bintu kamar
ar ta, haka Sharif ma sun saba sosai, dan kakar bintu ma yake ce mata.

Kwatsam aka je aka gaya wa baban bintu abun da yake faruwa, ya din ga yi mata fa
a, aka hanata fita, hakan ya damu Sharif, ya kasa jurewa, ya bita har gida.

Yayyen Bintu suka kore shi, amma ya
i tafiya, sai da ya ha
u da mahaifin Bintu, ya ce masa idan har son ta yake ya turo manyansa ayi magana.

Baban bintu yayi haka, dan ya kori sharif.

Sharif ya koma gida ya sakawa mai martaba rigima, shi fa baya son wannan jamilar, Bintu za a aura masa an ce ya tura iyayensa.

Mai martaba da fari ransa ya
aci, mai babban
aki ta taushe shi, ta ce dama ai so ake yayi auren, a fara aura masa bintun, sai ayi aurensa da Jamila, tun da dama shekara aka saka.

Matan mai martaba suka din ga
anan maganganu, suna cewa ya na biye wa yaro, kimar sa na zubewa.

Ya tashi tawaga daga Kano, aje a yi masa bincike a kan Bintu, idan ba su da wani aibu, a nema wa Sharif aurenta.

Mai martaba ya ji da
in bayanin da ya samu, a kan Bintu da iyayen ta.

Da yawa sun yi mamaki, yadda kamar
an sarki daga kano, zai auri
ar talaka.

Aka yi shagali sosai, aka yi auren.

Daga Bintu har Sharif, yarintar su kawai suke zubawa, dan a lokacin ba ta wuce shekara sha uku ba.

Mai martaba ya tura mutane, da ban ha
uri a kan abun da ya faru, tare da tabattar wa waziri, idan lokaci yayi ba fashi, za ayi auren Sharif da Jamila.

Jamila da yayarta, da mahaifiyarsu, ba
aramin tashin hankali suka shiga ba, dan haka suka din ga bin malamai, Allah ya tabattar da auren Jamila da Sharif.

Jin akwai wadda ake so Sharif ya aura, Bintu ta din ga murna, za a kawo mata
awa.

Wasa
sai da Sharif ya shekara biyu, kan ya auri Jamila, yau ya bayar da wannan uzurin, gobe ya bayar da wancan.

Ana haka Galadiman wannan lokacin ya rasu, bayan shafe zaman makoki, mai martaba ya sanar da na
in Sharif a matsayin Galadima.
an mai martaba da matansa, suka
aga hankalinsu, saboda gani suke rashin adalci ne, a bawa wannan yaron da ba shi da cikakken kai wannan babbar sarauta, bayan ga yayyensa.

Mai martaba ya yi burus, kuma bayan na
in sarauta, aka
aura masa aure da Jamila.

Maimakon Bintu ta damu kanta, ita murna take yi, shi uban gayyar ne yake ta takaici, dan har ga Allah ba ya son jamila, ga wannan sarautar da aka bashi, ya na da shekaru ashirin da biyar.

Jamila ta
udiri aniyar,
aukar fansar abun da aka yi mata a kan Bintu.

Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban
aki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa.

Hakan ya ja mata ba
in jini a cikin facalolinta.

Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce "
a ta bintu".

Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko.

Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan.

Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta.

Sa
anin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance
an wannan
aki da wancan.

Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara ha
a Sharif da Bintu fa
a, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka.

Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al'ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita.

A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata.

Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban
aki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar.

Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta ta
a ko
ari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da
an uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta.

Ana haka mai babban
aki ta rasu, wanda hakan ba
aramin tayarwa al'ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu.

Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu
autawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu.

Saboda tsabar
uruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna.

Aikuwa ta
wafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa.

Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu
iyayya.

Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan.

Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi
ari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba.

Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur'ani.

Sai a karo na hu
u, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan
arshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake
ular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin
auke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko.

Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi
a namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi.

Aka
auki soyayyar duniya aka
orata a kan yaron nan.

Watanninsa shida, yayi zazza
in wuni
aya ya rasu.

Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da
yar aka shawo kansa.

Still sai da Bintu ta sake
ari, sannan ta samu ciki ya zauna.

Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif.

Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a fa
ar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima.

Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam.

Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya
ulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi.

A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata
ar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai.

Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun
aruwa, amma yana jin tausayin Bintu.
annen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta fa
a da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da ha
uri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata fa
an ta rage fa
Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji.

Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu.

Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matu
ar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu
aya da galadima.

Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama,
tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu.

A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar
alubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba
aya ya canza mata.

Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama bi
i ba ta al'ada sai dai ta ga ciki.

Ayshercool.
08081012143
Paid book ne,
500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu
atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book
in.
Chapter 64 · 0% Book details