← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 126

Sashe 40

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iman ita ka
ai a
akinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya fa
i, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata.
angaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba.

Ta
e baki yayi ya cigaba da sabgoginsa.

Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja.

Ta wuni a uwar
akan mama, tun
arfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a
arfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya.
wabta na ta mamakin wani hamsha
in ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa.

A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta
i tsayawa.

Mai kwalliyar
awar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki.

Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira.
arshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir.

Ya je ya tarar duk an yi wa
awayenta kwalliyar ban da ita.

Ya kalleta ya ce "Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?".

"Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa" ta yi maganar cikin kuka.

Bashir ya ce "Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi".

Adam dai ya
ule
arshe, Bashir ne yayi ta bata ha
uri, sannan ta tsaya aka yi.

Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri
aya da na Adam.

Hauwwaliya har da tsalle, tana ko
a rumaisa.

Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala.

A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun ha
e cikin shadda iri
aya, hatta huluna da agogo iri
aya suka saka, motar na tsayawa, ta bu
e ta fice ta nufi wurin su Usman.

Abdallah ya din ga
aukar rumaisa a hoto.

Usman ya ce "Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da
an hasken da ba zai ishemu ba"
Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce "Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki"
Bisa ga al'ada,
awayen amarya da
an uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta
ar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar
a da uba.

Abun ba
aramin
ayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren
ar mitsitsiyar yarinya.

Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maro
a da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari.

Rumaisa ta kalli yadda hall
in ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba
aya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na
ibarta.

Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya ri
e hannunta, sai da ta
an waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai
arin
aukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana
arin
wace hannunta daga na Adam amma ya ri
eta sosai.

Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin
anwar zaratan maza har bakwai.

Iman ce ta fito stage, ta kar
i mic, tare da gabatar da addu'a, da fatan alkhairi ga amarya da ango.

Jabir ba
aramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?.

Me Adam zai yi da wannan yarinyar
ar talakawa mara kunya.

Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da
awayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi.

Dangin su Adam sun so su farfa
i maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya ri
e gulmarsa.

Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta
au ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin
an mata.

'To sai me ina ruwanki?' wata zuciyar ta tambayeta.

Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya
awar amarya an sha
auri,
ar ba
a kyakykyawa.

Iman ta
arasa ta cewa Usman "Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku
aya, koda yake na san yaya Aliyu"
Usman ya ce "Usman nake, ma'abocin haske,
ar balarabiya ya aka yi ne?".

Ta yi murmushi ta ce "Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa".

Usman ya ce "Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri
aya, dama zan zo mu zauna in baku amanar
amwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi ha
uri da ita, idan aka ta
ata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza "
Iman ta yi dariya ta ce "Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka" tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta ta
a ha
ata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa.

Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su.

Jabir ya
araso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce "Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da
arasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane".

"Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan
azu, ya san yadda aka tsara komai fa" ta yi maganar cikin muryarta ta shagwa
"Yes na ji, zo mu je dai, ko na
agaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a
aura auren da namu"
Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir.

Suna yin gaba ya hau ta da fa
an, dan me za ta je wurin maza ta tsaya.

Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta
aga kai suka yi ido hu
u, da sauri ta koma cikin wurin dinner.
e fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya
an sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?".

"Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan" ta
arasa maganar bilha
i za ta yi kuka.

"Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?"
Tura baki ta yi ta ce "Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka
i fasawa, wayyo mama ni na gaji"
A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun fa
Mc kuwa ko
asu kawai yake yi, saboda shagwa
a rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga ya
e, dan kar a fahimci wani abu.

Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka.

Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce "Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?"
"Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare"
"Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya" ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara.

Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya
ebi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba.

Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa.

An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta
aga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto.

Hatta ammi ta je wurin, an yi mata li
i sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi li
Yayyen rumaisa ma da abokansu, haka suka din ga yi mata li
i, wannan ya ja ta nan ayi mata hoto, sai ka rasa waye angon ma a cikinsu.
Chapter 40 · 0% Book details