← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 126

Sashe 5

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rumaisa na
yin sallama ta tsaya a tsakar gida ta ce "Me nake ji haka kamar warin daddawa?"
Huzaifa ya ce "Mama ce ta ce tuwo take sha'awa, shi za ayi yau".
mama ba ta da lafiya amma ta rasa mai za ta ci sai tuwo?"
Abdallah ya fito daga kitchen ya ce "Uban me ya hana ki cin abincin rana?"
"Abinci ba kifi ba nama, ba salak kawai tsuransa ni ba na ci"
"Iyeee ashe da gaske Huzaifa yake,
azu mai sunan baba ya tambayi abincin waye Huzaifa ya ce naki ne kin ce ba zaki ci ba ba kifi ba nama, ya ce zai gamu da ke idan ya dawo"
"Ku dai kullum burinku ku ga mai sunan baba yana tagayyara ni, ai shikenan"
Ta shiga
akin mama da sallama, "Mama ya jikin?"
"Da sau
i, shi ne ki ka
i cin abinci ko ruma, ke idan baki samu abun da ki ke so ba ba zaki ci ba ko?"
Rumaisa ta girgiza kai ta fara cire kayanta.

Sallama aka yi mama ta amsa, rumaisa ta shiga uwar
akin mama da gudu, dan ta tu
e daga ita sai phant za ta canza kaya.

Ammi ce ita da iman da Nusaiba, iman na rungume da Sabir.

A gurguje rumaisa ta canza kayan ta fito tana tsalle.

"Oyoyo yau ammi ta zo gidanmu"
Murmushi ammi ta yi tana fa
in "
ar gidan ammi, maman sabir"
Ta dur
usa ta gaida ammi, ta amsa mata cikin sakin fuska.

Mama ta ce "Bisimillah ku zauna"
Suka zauna su Nusaiba suka gaida mama, mama ta amsa musu cikin sakin fuska.

Ruma ta ce "Ammi ya aka yi ki ka san gidan nan?"
"Baban sabir ne ya saka yaronsa ya kawo mu, na ce bari mu zo duba mara lafiya"
Ruma ta fita da sauri, ta samu plate ta zubo musu ruwa, ta kawo musu tana ta murna.

Mama ta bi ta da kallo, ta tuna iskancin da ta yi da adam ya zo gidan.

Ammi ta ce "Ke maman sabir ya ki ka bar
an maza da aikin gida?"
Ruma ta ce "Idan na yi gwaleni za su yi su ce bai fita ba, shiyasa nake bar musu aikin su.

Ammi wannan wacece?" Ta yi maganar tana nuna iman.
anwar takawa ce, ita ce
ar autana"
"Tubarkallah mai kyau da ita" iman ta yi murmushi ta ce wa ruma "Ina wuni?"
Ruma ta zaro ido ta ce "Kai ki ka gaishe ni, ni fa yarinya ce, kin ma fini tsawo".

Dariya suka yi mata ammi ta ce "Ki daina gaya musu kar su raina ki, ai kin girma tun da ke maman sabir ce" ruma ta yi dariya ta ce "Eh kuma haka ne, ai kunya na ji da ta gaishe ni".

Ammi ta ce "Yau ba zaki
au sabir
in ba?"
"Hmm, ai da ni na yi zuciya na ce ba zan sake
aukar sabir ba, baki san me babansa ya yi mini ba ne"
Ammi ta ce "Subhanallah, me ya yi miki?"
yaleshi kawai ammi, ai ba zan iya zuciya da sabir ba, a bani masoyina na ganshi" ta
auke shi a hannun iman, ya cika hannu, suma ba
irin ta cika masa kai.

Suna cikin magana mai sunan baba ya yi sallama.

Wata irin razana iman ta yi da ya shigo
akin, wanda ita kanta ba ta san dalilin razanar ba.

Ya risuna ya gaida ammi, sannan ya tunkari rumaisa, ya dur
usa ya ri
e mata kunne ya ce "Abinci ba kifi ba nama ba zaki ci ba ko?" Ya ajiye mata leda a gabanta ya ce "Ki kai musu su dafa miki wani abun, dan yanzu ma sai ki ce yayi sanyi ba zaki ci ba, tuwo ma ki ce ba zaki ci ba, ki yi ta wahalar da mutane babu dalili".

Ta sunkuyar da kai ta
i magana.

Ya dungurar mata da ledar ya sanya hannu ya
au sabir a kan cinyarta ya yi waje.

Ammi ta din ga murmushi, gaba
aya rayuwar rumaisa burge ammi take yi.

Kifi ne manya ya kai na dubu, mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, ta tashi cikin murna ta tafi kai wa su yasir su yi mata wani girkin bisa umarnin mai sunan baba.

Ammi ta dubi mama ta ce "Amma dai kamar akwai wani abu da yake damunki, bayan rashin lafiya ma"
Mama ta ce "A'a, jinina ne ya hau"
"A tunanina zuwa yanzu mun zama
aya, dukkanninmu iyayene, masu fuskantar matsalar iyali kala-kala, dan Allah idan wani abu ne ke faruwa kar ki
oye mini ko ba zan yi wani abu a kai na yi addu'a"
Mama ta nisa ta ce "Babar
awar rumaisa ce ta zo, take gaya mini ma
wabtana na ta ya
a jita-jita, wai rumaisa ciki ta yi, na kaita garinmu ta
haihu, muka ce wai saceta aka yi, wai Allah ne ka
ai ya san yadda muka yi da
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ma
wabta kuma?"
"Wallahi kuwa shi ne abun ya dameni, wai abun ya cika unguwa, sun
ata mini sunan
a, na san rumaisa ba ta ji, amma ko kusa komai zaki yi wa rumaisa ba ta san hanyar lalacewa ba, balle ta yi ciki".

Ammi ta ce "Wallahi ba sai kin fa
a ba, duk wanda ya ji maganar nan ya san son rai ce, ki yi ha
uri basu isa su
ata mata suna ba, duk wanda yake son ta da gaske jita-jita ba zata hana shi aurenta ba, ki kwantar da hankalinki kuma kar ki bari ta sani, tun da da bakinta ta ce mini duk wanda yayi mata abu sai ta rama" shigowar rumaisa
akin ce ya sanya ammi sauya maganar.

Suka mi
e zasu tafi, rumaisa ta ce "Ammi, an
ora mana abinci fa, ku tsaya a gama"
Ammi ta ce "Tuba muke, muna sauri ne, ayi ha
uri" rumaisa dai ba haka ta so ba.

Suka fito zasu tafi, mama ta ce ina ga mai sunan baba yana waje da sabir.

Suka fito aikuwa yana wajen, ammi ta ce "Iman kar
o sabir"
Jikinta har rawa yake yi, saboda gaba
aya mai sunan baba tsoro yake bata.

Kamar munafuka sai sunkuyar da kai take, ta mi
a hannu za ta kar
e shi, amma shiru bai bata shi ba.

Sai da ta
aga kai suka yi ido hu
u, gabanta ya sake fa
uwa, har numfashinta ya tsaya na wucin gadi.

Ganin yadda ta tsorata ta rikice, sai da ya bawa mai sunan baba haushi, shi ba dodo ba meye na wani tsorata.

Ammi ta saka sidi ya bu
e booth, ya
ebo cartons na lemo da kayan marmari, na dubiyar mama.

Ammi ba ta tsaya ba, dan ta san mama cewa za ta yi yayi yawa, suka shiga mota suna
aga musu hannu.

Tun da suka tafi ammi take sa
awa da warwarewa a zuciyarta, dole mama ta shiga damuwa, babu uwar da za ta ji da
in a
ata sunan
a a cikin unguwa dan wannan kawai sai ya hanata auruwa.

Suna tafe Nusaiba da iman na ta yi wa rumaisa dariya, yadda take gudanar da al'amuranta da yadda yayyenta ke kula da ita.

Tun a hanya ammi ta kira adam a waya, ta ce idan an yi sallar magariba tana son ganinsa.

Kamar yadda ta bu
ata ya je ya sameta, ta idar da salla tana lazumi, bayan ta kammala ta dube shi ta ce "Mai ka yi wa rumaisa ne?

Take cewa da tana da zuciya ba zata sake
aukar sabir ba?"
Ya kalli ammi ya ce "Wani abun ta ce na yi mata ne?"
"Ba ta ce ba, amma abun da ta fa
a ya tabattar mini da wani abun ka yi mata"
"Ba wani abu bane ammi, na mata garga
i a kan zuwa gidan nan ne?

Idan aka fuskanci wacece, za'a iya
arin citar da ita ko cutar da sabir ta hanyar ta".

"Na ji, yanzu ba wannan ba ma, wata shawara na yanke a matsayina na uwa na kira ka na sanar da kai, ba dan kana da hakki a kan abun ba ma sai dai ka ji na zartar".

"Wane hukunci kenan?"
"Ina son ka auri rumaisa!!!"
Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR
DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO.

SHIN
URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION?

KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE
I KINA HASKAWA?
Chapter 5 · 0% Book details