← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 126

Sashe 48

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai sunan baba kuwa, missed calls
in nan a ransa ya wani, zuciyarsa na ta raya masa ya bi kiran nan, ko ya manta ya cigaba da sabgoginsa, sai ya tuna, yayi iya
arinsa ya manta, amma ya kasa, yana ta tunanin menene haka mai muhimmanci da ya sanya ta yi masa missed calls har uku.

Babban abun da ya
atawa iman rai, bai wuce yadda ta koma gida ta tarar da Jabir ba, ya kasa ya tsare a falo, suna hira da Ammi, yana ganinta ya hau rawa jiki, ya fara yi mata hira.

Iya
arin ta take yi, kar ammi ta fuskanci wani abu, dan haka ta ke amsa masa hirar.

Ammi ta tashi ta bar musu falon, ta tafi
akinta, iman na shirin tashi ita ma, wayarta ta fara ringing, ba ta duba ba ta
aga ta saka a kunnenta, tare da yin sallama.

Shiru yayi bai amsa ba, sai wani numfashi da yake saukewa a hankali, yana jin yadda murayar ta ta, ta daki zuciyarsa.

"Hello, ba a jina ne, Assalamu alaikum" ta yi maganar cikin
abi'arta ta iyayi.

"Missed calls na gani" yayi maganar cikin dakakkiyar muryarsa da take razanata.

Sai da ta
an ru
e, amma ta yi iya yin ta, ta ha
a nutsuwar ta wuri guda ta ce "Yaya Umar ina wuni?".

"Lafiya
alau".

"Dama Anty Rumaisa ce ta kar
i aron wayata ta kiraka, kuma ba ka
aga ba, ba intentionally na kira ka ba, ai ka gaya mini na daina kiran wayar ba tata ba ce, ka yi ha
uri dan Allah" ta
arasa maganar kamar za ta saka masa kuka.

Ji yayi jikinsa har wani rawa yake yi, dan shi a rayuwarsa, idan ba mama da rumaisa ba, babu wata
a da yake ke
ewa yayi wata doguwar magana da ita, ko ita rumaisan ba shiga shirgin ta yake yi ba, amma ya tsinci kansa da jin da
in sauran muryarta.

Amma da yake namiji namiji ne, cikin basarwa ya ce "Ina rumaisan take?".
azu ne na je gidanta, ba ta jin da
i shi ne ta kar
i wayata, ta kira ka, amma ta ji sau
"Shikenan" ya katse wayar.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, duk da muryarsa na razanata, amma ta tsinci kanta da jin da
in kasancewa da shi ta waya.

Wani guntun murmushi ta yi, tana
aga kai ta ga Jabir da Nusaiba duk ita suke kallo.

"Iman da wa ki ke waya?" Jabir yayi maganar a hasale.

"Kamar yaya?

Yayan Anty rumaisa ne".

"To meye ala
arki da shi" ya sake yin maganar yana tsareta da ido.

Tashi ta yi tsaye ta ce "Yayan matar wa na ce, kuma ni babu wani abu tsakani na da shi, ta ari wayata ta kira shi ne kawai".

"Ina fa lura da yadda ya din ga bin ki da kallo lokacin bikin nan, idan ya ganni tare da ke ya din ga hararata".

Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya kai ne ka ga haka, amma ba hakan bane" ta wuce ta nufi
akinta.

Jabir zai kuma magana, Nusaiba ta ce "Uncle J, ka bi ta a hankali, fushi da tashin hankali ba naka bane ba, ba abun da yake tsakaninta da mutumin nan, na riga na baka shawara, ka je wurin ammi kawai, ko ka gaya wa turaki, na san komai zai zo da sau
i" sauke numfashi ya yi, ya tashi ya fice.

Tun da Adam ya fara hawo wa step
in bene, yake jin
auri, yana hawa falon saman, ya tarar da ya turnu
e da haya
i, kuma haya
in daga kitchen yake fitowa.

A sukwane ya nufi kitchen
in, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda
aurin manja.

"Ke meye haka?

Me ki ke yi?"
Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi"
Da sauri ya
arasa yana
arin kashe gas
in, dan tuni suka ha
a baki da iman, direbanta ya
uro mata.

Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya"
"Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" Bu
e masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi sa
a mai kyau, sai
amshin attaruhu take.
aramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki".

Ta ce "Eh na yadda" ya gya
a kai ya fice.

Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya le
a falo, ya hangota tana ta su
ar baki tana cin yaji.

Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai.

Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving
in su.

Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili.

Tashi ya yi ya kunna fitilar
akinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta
ata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke.

Bai ce mata uffan ba, ya
auki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta.

A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a
an kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da
arin tsafta.

Tea yake son ha
awa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi.

Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha.

Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka
auko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare".

Ta taka kujera, ta bu
e wata drower, ta
auko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba.

Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta
auki
aramin flask ta juye masa, ta ha
a masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu.

Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi".

Kamar soko haka yake kallonta, ta
auki wani
an bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice.

Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira
aya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne.

Ta kar
a ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su
yaleta su cigaba da kaiwa.
akinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana ban
aki yana wanka, ta karka
e masa gadon, ta gyara ta kalli gadon bai gyaru sosai yadda yakamata ba, ta ce "Oho, ni a gidanmu babu gado sai katifa, hakan ma na yi
ari ai".

Idonta ne ya sauka a kan side bed, in da ya sha shayin, nan ya bar kwanukan, "Kam bala'i, Wa ya bar wa kwanukan nan a nan?" Ja ta yi ta tsaya tana jiran fitowarsa.

Rigar wanka ce a jikinsa, sai dai gaban rigar a bu
e yake, gashin
irjinsa ya kwanta saboda ruwa, da sauri ta kawar da kanta gefe.

"Ya aka yi?".

Ba ta kalleshi ba ta ce "Eh kwanukan da na ce idan ka gama shan shayin ka wanke na gani a nan".

Ya ce "Eh, idan kin gama ki fita da su ki wanke"
"Ni na sha maka da zan fita da su in wanke?"
Ya kalleta ya ce "Me ki ka ce?" Ta girgiza kai ta ce 'Bakomai".

"Oya kwashe su ki fita da su, ki je ki wanke, sannan kan na gama karyawa, ki shirya, zamu je gidan turaki".

Ta ji da
i za su fita, amma babban abun da ya bata haushi, bai wuce sakata fita da kwanukan da shi ya mora ba ita ba.

Wata turkey abaya ta saka, blueblack fuskar nan fayau babu ko kwalli, ta yi ta shafa turare, dan akwaisu available a kan mudubinta, dan ko a gida ta saba, dan Abdallah har
arauniyar turare yake ce mata.

Suna tafe a hanya, tana kallon titi, tana son gane hanya, dan so take wataran ta
alle ta tafi gida.

A gidan turaki suka tarar da Jabir, da shi da Jamil ga kuma Zainab da Mummy, Samha ce ba ta nan.

Rumaisa ta gaishe su, sai dai ba wanda ya amsa mata da mutunci sai Zainab.

Adam ya ce "Zainab nema mana iso wurin mai girma turaki" ba musu Zainab ta tashi.

Rumaisa da sun ha
a ido da Jabir take galla masa harara, haka Jamil da yake ta kallonta a wula
ance.

Aka yi musu izinin shiga wurin turaki, turaki yana ganin rumaisa ya fara murmushi.

Ita ma Murmushin ta yi ta ce "Barka da wannan lokaci ranka ya da
"Barkanmu dai
ar albarka, ya gidan ya
ari?"
Ta amsa da "Alhamdilillah"
Adam har le
a fuskarta yake, ya ga ko ita ce ta nutsu haka.

Shi ma suka gaisa da Adam, Adam ya ce masa sun zo su yi godiya ne, tare da yi musu bangajiya na hidima da aka yi.

Turaki ya yi musu nasiha sosai, mussaman ma Adam, a nasihar rumisa ba komai take fahimta ba, mussaman da ta ga da Adam ake.

Bayan turaki ya gama, yayi musu addu'a sosai, Adam yayi ta godiya, ya ce masa za su je wani wurin daga nan.

Rumaisa ta ce "Babana, yaushe zaka zo gidanmu, na iya abinci in dafa maka duk abun da ka ke so?" Yayi murmushi ya ce "Za a zo ne in sha Allah".
Chapter 48 · 0% Book details