← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 126

Sashe 117

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba zai gaya mini ba"
Mai sunan baba ya ce "Zai gaya maka mana, zaka ci abinci ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Bari sai na gama farfa
owa, idan kuma na mutu....

"Shhhh, zaka farfa
o in sha Allah, har aurar da kai sai na yi"
Ammi bakinta ya
i rufuwa dan murna, ita ba ta san ya aka yi ma ta sa ta zo
aya da Mahmud ba, saboda Mahmud akwai taurin kai da rashin mutunci, mai sunan baba kuma akwai izza da son girma, amma yadda yake yi masa zaka gane akwai mutuntawa da girmama juna a tsakaninsu.

Ya kwantar da Mahmud, ya ce "Ka yi bacci, zan je gida
anwarka ta yi maka girki, mu zo ta duba ka"
"Kar ka wahalar da ita, ga Mummy ga Ammi ga daughter duk na wanda na samu zan ci".

"Ba wata Mummy, na ammi zai ci" Rumaisa ta fa
a tana harare-harare.

Fauziyya ta bu
e baki za ta yi magana, amma kwarjinin mai sunan baba ya cika mata ido, dan ta san
arya take, ta zagi rumaisa a gabansa ya
yale ta.

Ya kalli Adam ya ce "Ina son yin magana da kai"
Mamaki ne ya kama Adam, amma ya tashi ya bi bayan mai sunan baba suka fita.

Fauziyya ce ta
ora da rashin mutunci.

"An yi magana wani ammi ce za ta bashi abinci, sai ka ce ammin wahalar sa ta sani, uwarmu ce dai ta yi masa duk wata wahala ta rayuwa".

"Da tayi mata fashin
an?

Kallon biri ku ke masa yake yi muku na ayaba fa.

Uwar me ta tsinana wa rayuwar ta sa ban da masifa, uwar ri
on arziki ce za ta raba uwa da
an ta, ta raba jini da jininsa, ta raba shi da
an uwan sa, yanzu dai shi ma ya san gaskiya, gurbin ido ba ido ba ne, kuma wallahi ko bayan shekara dubu, tuwo sunan sa tuwo"
Ammi sai
arin hana magana take yi, amma rumaisa tayi mursisi ta din ga gasawa Mummy da Fauziyya magana, ita ka
ai su biyu ba tare da kunya ko tsoro ba.

Duk abun nan da ake yi Mahmud yana jin su, amma yayi shiru kamsr mai bacci.

Mai sunan baba ya kwashe komai ya gaya wa takawa, game da Alhaji Aminu, jikin takawa har tsuma yake yi ya ce "To yanzu Lagos
in zamu je, ko yaya za a yi?

Mu ga shi Alhaji Aminun, idan ta kama tambayarsa zamu yi, ko ma a tafi da ammi sai ayi "
Mai sunan baba ya ce "A'a ina ga gara mu mu je mu tabbatar, tun da yanzu tana cikin damuwar rashin lafiyar Mahmud, dama da shi na so mu je, to gashi ba shi da lafiya"
"Bakomai, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu, in dai ya
ara warwarewa, sai mu je kawai, ina fatan Allah ya tabbatar ya sanya
an uwan iman ne "
Mai sunan baba ya amsa da Amin, har takawa ya juya zai tafi mai sunan baba ya ce "Na ce ba" ya juyo ya tsaya yana sauraren sa.

"Akwai bu
atar duk abun da ya faru a baya ya wuce, a fuskanci gaba.

A zamana da Mahmud babu abun da yake marari da so da ya wuce ka, you have to play your role as his senior brother, babu abun da yafi
an uwa da
i.

Ba zaka gane hakan ba sai ranar da babu shi a duniya"
Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai" mai sunan baba ya jinjina masa kai ya tafi.

Samha sun je duba Mahmud a asibiti, dan tuni labari ya zaga masarautar, Mahmud ba shi da lafiya,
an dubiya sun fara kaiwa suna komowa.

Sai dai fa cacar baki ta
i tsayawa a tsakanin Fauziyya Mummy da rumaisa.

Muraran yau ruma take nuna musu asalin tantirancinta.

Samha za ta saka baki ruma ta ce "Yi mini shiru, ba dake nake ja gayyar mushirikai ma
iya Allah, ai wallahi a doron duniya ban ga bokan da zai yi asirin da zai kamani ba, sai dai ku yi wa wasu".

"Su waye mushirikan?"
"Gaku nan gaba
ayanku, ban da yawon asiri da
arin rusa rayuwar mutane me ku ka saka a gaba, azzalumai ma
iya Allah"
A rikice ammi ta fita neman Adam, suka yi kici
is a hanya, ta ce masa maza ya je ya
au rumaisa ya mayar da ita gida.

Sai dai suna shiga
akin, suka tarar Samha da Fauziyya tamkar za su rufe ruma da duka, ita ma ta tsaya ta ri
ugu tana bala'i, Nusaiba sai ba su ha
uri take.

Babu abun da ya gigita Samha sama da ganin tirtsetsen ciki a jikin rumaisa bayan ta mi
e, ta ri
ugunta.

Ruma ta ce "Mamaki ki ke yi ko Samha, kin ga ciki a jikina?

Baba uwani ba ta gaya miki na cire layar da aka saka a cikin katifar
akunan mu ba?.

Ai tunda Allah ya sa na ritsuta, duk wani lungu da sa
o, sai da ta tone komai, na zauna na warware abun da ki ka
ulla mini na tsiya, masifarku sai dai ta
are muku".

Cikin matsanancin tashin hankali Samha ta ce "Me ki ka nufi?

Nima sharrin zaki yi mini?".

"Wallahi na fi
arfin in yi miki
arya, rufa miki asiri kawai na yi, amma tarkacen layoyi da kayan tsubbun duk da ku ka binne mana a cikin gida an tone su, na kuma tara su wuri
aya saboda sheda, duk bala'inki ke da Adam sai dai ido Samha"
Ba tare da sanin Adam ya shigo ba, ta yi
arin hanka
a Rumaisa.

Amma cikin zafin nama, ya hana faruwar hakan, ya
auketa da mari.

Tsit suka yi suna kallon Adam.

"Wallahi ko da makamancin wasa, ki ka sake ki ka yi wa rumaisa wani abu, sai na taka ki, sai dai zumuncin ya watse uban kowa ya kama gabansa wallahi.

Kuma na gode da abun da ki ka yi mini, na mayar da ni mara amfani a gidana, sai dai Allah ba a azzalumin sarki bane ba, kanki ki ka yi wa samha"
Mahaifiyar Samha ta fara bala'i "Wane irin mutum ne kai?

Duk abun da yarinya ta fa
a sai ka yarda da shi, kai ba ta laifi kenan.

Saboda rashin ta ido, a gabana ka mari
a ta"
"Saura Jamil ma, wallahi sai na warware kowane munafuki, babban algungumi mara tsoron Allah"
Nurses ne suka shigo, suka ce su fa asibitinsu ba wurin hayaniya ba ne ba, dan haka a tafi a bawa mara lafiya dama
r hutawa.

Adam ya maze ya ce kowa ya tafi Shi da Ammi za su zauna, ruma kuma anjima zai mayar da ita gida.

Mummy ta ce bai isa ba.

Likita ya zo da kansa, ya ce wace mahaifiyar Mahmuda ta zauna da shi, ita da mutum
aya, ruma ta nuna Ammi ta ce "Ga mahaifiyar sa nan" Mummy na ji tana gani aka sallame su, ya rage sai ruma Ammi Nusaiba da takawa.

Mahmud ya kalli ruma ya ce "Daughter kina ganin bai yi wuri ba?"
"Bai yi ba daddy, yakamata komai ya zo
arshe, enough is enough"
Adam ya ce "Ban gane me ku ke nufi ba"
"Zaka gane very soon, amma kar ka matsa Please"
Ammi ta ce "Mahmud, a kawo abincin?

Ya ka ke ji yanzu?"
"Alhamdilillah da sau
i, Yaya zai kawo abincin"
Da azahar takawa ya tafi sallar juma'a, bayan ya dawo ne Iman suka zo tare da mai sunan baba.

A lokacin Mahmud yana zaune, har yayi salla jikin da sau
Iman ta din ga jera masa sannu, mai sunan baba ya ce "Deeja zuba mana abincin tare da shi, ko zai samu ya ci da yawa".

"Cikina dai babu da
i, kar a
ura mini abinci da yawa".

Mai sunan baba ya yi murmushi, ya ajiye abincin a kan gadon, ya ce "Ko a baki zan din ga baka ne?

Na iya
ura ka tambayi deeja ka ji"
Iman ta sunkuyar kai, saboda ammi na wurin a zaune da nusaiba.

Takawa kuwa ya cewa ruma ta tashi ya mayar da ita idan sun gama cin abincin.

Iman sai tsokanar ruma take yi, wai yau abun
oye ya fito fili, sabir zai yi
ani.

Ta din ga tura baki, tana harar su.

Ko da suka je gida gaba
aya takawa ya hau yi wa rumaisa fa
"Why are you making things complicated rumaisa?"
Cikin rashin fahimta ta ce "As how?"
"Ni da ke idan kin gaya mini abu ina yarda da ke, sauran mutanen fa? maganganu sun fara yawo, mahmud ya daki Jabir ya rufe shi ba wanda ya san dalili, mahaifiyarsa ta je an
i sakin sa an ce sai mahmud ya je.

Kin ce Samha na asiri, a dalilinki na daketa, komai ya hargitse na ma rasa ya zan yi, wambai ya ce lallai in zo da ni da ke, kun hargitsa al'amura, babu wanda ya san me ku ke ciki, kina
oye mini wasu abubuwan"
"Wait" tayi maganar tana
aga masa hannu.

"Duk cikin wannan maganganun naka, marin Samhan da ka yi ne ya fi baka haushi kenan?

To sai ka koma ka bata ha
uri ai.

Ka san dai ba zan yi mata
arya ba, tun da lokacin da na zo gidanka ba uwar abun da na sani, balle in san an yi maka wani asiri baka da lafiya, ko in yi wa Samha
arya.

Kuma ba wambai ba ko gaban waye idan na je ina da gaskiya kuma zan fa
eta.
arasa ta saka mukulli, ta bu
e wata wardrobe, ta
aukko wata Viva bag, cike da takaici ta watsa masa.

Ta ce "Ga ka
an daga binne-binnen da aka yi a hanani zama, daga ni har kai, da yake Allah ba azzalumin sarki bane, duk in da nake rayuwa in dai da sihiri, sai na sani.
Chapter 117 · 0% Book details