← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 126

Sashe 58

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har baba uwani za ta fita ta ce "Kenan papa da gaske maye ne?"
A razane baba uwani ta waiwayo ta ce "Me ki ka ce?"
"Kin ji me na ce ai".

"Ke waye ya gaya miki?"
Rumaisa ta ce "Ke ce ki ka gaya mini yanzu"
Baba uwani ta ce "Ke, yaushe na gaya miki?

Ki ji tsoron Allah"
"Ke ki ka fa
a, wannan ne karo na biyu ki na gaya mini, zan kuma tambaye shi".

"Dan girman Allah ki rufa mini asiri, da wasa nake yi ma fa, dan Allah kar ki gaya masa"
Rumaisa ta juya ta cigaba da saka
an wakenta, baba uwani kuwa ta toshe baki ta na fatan, Allah ya sa kar garin neman gulma, ta janyo kwa
arta ta yi ruwa, domin kuwa ta lura bayan
uriciya, har da wauta ke damun rumaisa.

"Hajiya Lubabatu, ki na free gobe in Allah ya kaimu".

Mummy ta yi maganar da waya a kunneta.

"Ya aka yi ne?".

Mummy ta ce "wurin malam na gidan dutse, zaki rakani, akwai case ne".

Hajiya Lubabatu ta ce "Wane irin case kuma?".
an maje ne ya turo mini sa
o, wai ya ji mai martaba zai wakilta turaki, zuwa taron bun
asa al'adu da harsunan afrika, rainon burtaniya, wai ya
auki mutum biyu a matasan yaran nan ya tafi da su, kuma da alama za a samu cigaba, wai ya ji turaki ya ce har da Adam za ayi tafiyar".

Hajiya Lubabatu ta ce "To ba sai su yi ta yi ba"
"Ina ba fa zai yiwu ba, wai ke meyasa ki ke
aukar al'amuran nan da sau
i, komai sai dai shi, duk wannan miyagun fentin da suke tare da shi, komai sai dai a saka shi, ke me zai hana a tafi da Jabir, ga mahmud, ga Jamil nan, ina su yarima jikokin mai marataba, duk ba a
au kowa ba sai shi?

A dalilin me?".

"Kuma fa da gaskiyarki Jamila"
"Dan Allah ki shirya, na ga da yadda zai tafi ai".

"Ke dole ma, zan shigo da wuri ma yi maganar, ni Jabir ne yadda ki ka san an yi masa asiri,gaba
aya hankalinsa ba ya kan harkar sarautar nan, mussman idan abu da adam a ciki, sai ka ce ya yi masa asiri".

"Ni ma na fuskanci kamar aikin da ake yi wa Mahmud ba kamar da ba, zamu ha
u kawai".

Ko da Adam ya dawo da yamma, ya iske ruma, tana kwance a doguwar kujera, tana kallon cartoon.

Ya kalleta ya na jiran ya ji ko za ta ce wani abu, suna ha
a ido ta galla masa harara, bai dai tanka mata ba, ya wuce
akinsa.

Adam dai hatta abincin sa bai iya ci ba, yadda aka kawo su, haka ruma ta
auka ta mayar musu.
bacci sai
arawo, kwana ya yi ya na juyi, kuma yau sai ya kasa tashi ya yi sallar dare kamar yadda ya saba, tasbihi ma sai ya kasa sa
anin da, sai ajiyar zuciya da istigfari, ji yake komai ya yi masa zafi, ba ya jin da
in komai, ko abinci ya kasa ci, ya rasa ta ina zai fara.

Sai gefin asuba barcci ya
auke shi, ana kiran salla shi ma ya tashi.

Ko da ya dawo daga sallar asuba, neman wuri ya yi ya zauna, ya cigaba da Adduoi, sai da rana ta
aga, sannan ya tashi ya shiga wanka.

Har ya kammala shirinsa, bai ji motsin ruma ba, gashi yau Monday.

Gaba
aya ba shi da kuzari, balle karsashi, ya nufi
akinta.

Ta na tsaye a gaban mudubi, yau ta fara saka uniform
in ta, ta saka skirt
in ya zauna a jikinta cif, da taimakon jigidar da ke
aure a
ugun na ta.

Ta saka
ar cikin, ta
aga kai tana
arewa wuyanta kallo, ta na shafa wurin da ya yi mata rauni.

Uniform
in sun yi mata kyau sosai.
an gyaran murya ya yi ya ce "Haryanzu ba ki shirya ba, balle ki karya yau monday fa"
"Na gama shiryawa, uniform nake
arasa sakawa".

Ya juya ya tafi dining ya zauna, da niyyar ko yaya ya ci wani abu, dan ya na jin yunwa, amma ya ji bakinsa babu
ano.

Ta fito ta ajiye jakarta a kan kujera, ta nufo dining
Ta bu
e food flask
in abincin, soyayyiyar doya ce da miyar
wai.

Ta ce "Bari na yi bisimillah, na ci abincinka, yau ban yi girki ba, ko sallar asuba ba ka tashe ni ba, da safe na yi salla kuma alhaki a kan ka".

Ta kama kujera, ta haye saman dining ta zauna.

Kallon ta yake, yana jiran ta yi maganar abun da ya faru jiya, amma ya ga ba ta yi ba, ta ha
a shayi ta tura masa kofin gabansa, ta
au na ta.

Jujjuya cokali ya din ga yi, amma ya gaza kai wa bakinsa ya sha.

"Wai da zafi ne shayin?" Bai ce mata komai ba, ya cigaba da kallon shayin.

"To in
ara maka madara?" Sai a wannan karon ya girgiza mata kai alamar a'a.

"To ka sha mana, ka ci abincin"
A hankali ya kai kofin bakinsa, sai dai zu
ayan da ya yi, sai da yayi ta fama sannan ya ha
iye shi,
arshe ya tashi ya ce mata, ta same shi a mota.

Kasancewar rumaisa tana son shayi, haka ta ha
e nasa da nata ta shanye abun ta, ta
auki jakarta, ta ga tasa jakar ma ya bar ta a wurin, ta
auki jakarta da tasa, ta fita.

Ta tarar da shi, ya kifa kansa a sitiyarin motar, sai da ta bu
e motar, sannan ya
ago.

Idanunsa sun yi ja, kamar am zuba masa abu a cikin su, har sai da ta fara fargabar ko haya
in ne zai fara fitowa, amma ta ga idon ya tsaya a haka, ya fara jan motar a hankali.

"Wai zazza
i ka ke yi ne?" Bai amsa ba, sai lumshe ido da yake ya na bu
ewa.

"Yauwwa papa ka san me?

Na san ba zaka amsa ba, haka mai sunan baba yake yi, shiyasa bakomai ka ke yi mini na ji haushi ba, na san ka na ji na.

Dan Allah ka sai mini lunch box mana, in din ga zuba abinci ina tafiya da shi makaranta".

"Lunchbox na
an primary ne"ya fa
a a hankali.

"Eh, ni shi nake so,
arami mai kyau" tana cikin maganar traffic ta tsayar da su, sai ga mai alawar madara, rumaisa ta tsayar da shi ta kalli Adam ta ce "Papa
an sai mini".

Ya kawar da kansa gefe, yana kallon wajen window.

Ta saka hannu ta zuge jakarsa da ke hannunta, ta ga ku
i a ciki, ta
yale da dariya ta ce "Allah ya kama ka, ga jakarka a hannuna ai, na ranci dubu
aya, idan na gama makaranta, na samu aiki, salaryna na farko zan biyaka" sai da Adam ya kalleta jin abun da ta ce, ta bawa mai alwar madara, ta ce ya bata ta duka.

Gaba
aya ba shi da kuzarin da zai biye mata, dan haka bai ce mata uffan ba.

Ita kanta ta lura shirun nasa ya yi yawa, shi kuma mamaki yake yadda duk surutunta, da mitar tsiya amma ta yi shiru, ba ta ce masa komai ba, a kan abun da ya faru.

Suna tafe ta cika masa kunne da wa
in indiya, ga abun da yake damunsa, ga wa
arta da ta addabe shi, kuma ya san da ya kuskura ya ce ba ya so, za ta tsiri wani abun.

Sai kuma ta koma wa
e-wa
e, masu kama da habaici "Idan mutum ma bashi da lafiya, shan kunu ba magani bane ba.

Idan kuma wani abu ne yake damunsa, rashin cin abinci ba maganin matsala bane ba.

Cikin mutum ne zai gaya masa, ulcer ta kama shi na ruwan rumaisa, lalaaalallaaa, alawar madara da da
Duk ta yi ta gama ya na jin ta, ya kaita
ofar makarantarsu, ta sauka ta
au jakarta, ta shiga.

Ya na tsaye ya na saka lense
in rigarsa, sai kokowa yake ya saka, amma ya kasa sakawa saboda hankalinsa ba a kan abun da yake yi, yake ba, jin zuciyarsa yake tamkar a kan wuta, wata
ishirwar ba
ini ce ke addabar ruhinsa, abun da yake ji a jikinsa, zai iya rantsuwa da abun da zai kashe shi, tun da Allah ya sa mama ta kawo shi duniya, bai ta
a jin irin sa ba, duk yawon zuwa makaranta da yake yi, da yadda
an mata, ke kaiwa suna komowa a gabansa, bai ta
a damunsa ba, amma yau ba gaira ba dalili
ar mutane ta tsaye masa a tunaninsa.

Mussman jiya da ya ga status
in ta, ta yi video ita da sabir, ta
ora, ya kalli status
in nan, bai san adadi ba, sai da ya fara bawa kansa haushi.

Kuma ya kwanta bacci ya din ga mafarkinta, mafarkin da sai ya kai shi ga danganawa ya tsarkake jikinsa kan ya yi salla.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mayar da hankali, ya gama abun da yake yi, ya fita ya yi wa mama sallama ya tafi.

Sai dai a
asan zuciyarsa ya na jin, da zai samu dama ya ganta, wata
ila atleast, zai rage abun da yake ji a tsakanin
irjinsa zuwa zuciyarsa, amma ta yaya?.

Sanin halin rumaisa na rashin isasshen saiti, ya sanya ba ya wasa da abun da ya shafeta, duk da halin da yake ciki, da lokacin tashi ya yi, haka ya tafi
aukota.

Sai dai ya shafe mituna goma sha biyar, a tsaye, bai ganta ba bai ga alamarta ba.

Sai da ya
an tsorata, ya fara addu'a Allah ya sa ba tafiyarta ta yi gida ba, saboda abun da ya faru.

Har zai shiga mota, ya shiga cikin makarantar yana duddubawa, can ya hangota, a cikin liluka, ta ajiye
aramin hijjabinta, sai fama take yi kai ka ce wata
ar primary 2.

Sai da ta hango shi, sannan ta saukko, ta
auko jakarta da hijjabinta, ta zo ta wuce shi, ta tafi mota, ba tare da ta ce masa uffan ba.
Chapter 58 · 0% Book details