← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 126

Sashe 69

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To, Allah ya ji she mu alkhairi, ya sanya albarka na gode sosai" Ammi ta ji tamkar ya yaye mata kaso mafi rinjaye na damuwarta.

Da ta koma wurin takawa, ya kalleta ya ce "Ya dai na ga kina fara'a?"
"Ina ruwanka?"
Yayi murmushi ya ce "Tuba nake".

Ta zauna ta ce "Kai ban gaya maka ba"
Ya tattara mata hankalinsa.

"Laila za ta shigo cikin sati Mai zuwa"
Ya waro ido ya ce "Yanzu muka gama magana a waya, amma ba ta gaya mini ba".

"Oho muku dai".

"To ta koma ba ma so, ba ta zo lokacin rasuwar aisha ba, ba ta zo ta ga
an ta ba, na yi aure ba ta zo ba sai yanzu?"
Ammi ta ce "Ai ka san yanayin aikinta a can, amma ta ce za ta da
e sosai idan ta zo, yaran ne za su koma da wuri, tare da babansu idan ya zo, shi sai next month in Allah ya kaimu zai zo".

"To Allah ya kawota lafiya, gashi ni zan yi tafiya. yauwwa Ammi, mai girma turaki ya kirani, ya ce mini mai martaba ya tura mu wakilcin taro, kuma da na dawo zan je course
in nan ta watanni shida, kin ga ba zan wani da
e tare da ita ba".

"To sai ta zo
in dai tukuna".

"Ammi, ina Jamil ne?

Ban
ara ganinsa ba fa, tun da ya tafi
aukko Rumaisa".

Ammi ta ce "Ni ma dai na yi mamaki, ka san da ta zo ta ce wai
in hawa motar ta yi, saboda ta san yana jin haushinta, ina ga sa
ani suka samu, ya ji haushi, mukullin motar ma, Sidi ya bawa ya kawo".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "To ai ba da ni suka yi ba, ni kaina ba na son surutun nan na ta, ita ba ta iya kara ba ko ka
an".

"Ai
uruciyar kenan, sai dai ayi ta sakata a hanya, ni maganar da ta fa
a ne a kan Jamila, nake jin tsoron kar ta koma kunnenta, bana son tashin hankali da masifarta, in da na gode wa Allah ma, ba a gaban wani ta fa
a ba"
Takawa ya ce "Ina tsoron wannan bakin na ta a cikin masarautar nan, sai dai Allah ya shirya".

Can
aki kuwa, suka gama koke-koken su, ita da Iman, kamar wata babba haka ta yi ta rarrashin iman.

Can Iman ta ce "Anty rumaisa ba zaki kira mai sunan baba ki yi masa godiya da ya ya je gida ba?".

Ta yamutsa fuska ta ce "Godiyar me kuma?"
"Dubiya da ya zo mana".

"Ba ki san halin gayen nan ba, ba lallai ya gode, kina ganin yarfani ya yi dan na ce zan raka shi, wai na je na kula da mijina, yanzun ma zai iya yarfa ni".

Iman ta ce "Ba haka bane, yakamata ki yi masa godiya, idan yana gida ma sai ki gaisa da su mama, ko yana zama yayi dare a waje?".

Rumaisa ta kalleta ta ce "To mai sunan baba da mace ne, da an shigesu, ba shi da wasu abokai fa, daga makaranta sai kasuwa, sai gida, su wani ball su wani abubuwan abokai, ko yawo duk ba ya yi, da dai yaya usy ne ko gadanga na mama yaya Aliyu, mama da kanta take fita yawon nemansu wataran"
Iman ta yi murmushi ta ce "Kowa da halinsa kenan, ga wayar ki kira shi"
"Sai dai ke kira shi"
"In kira shi in ce masa me, na gaya miki ya ce na daina kiransa".

Rumaisa ta ce "Gaskiya idan na kira shi, ya yi mini wula
anci sai na rama a kan ki".

Iman ta bata wayar ta ce "na yarda".

Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya
aga, alhalin wayar na hannunsa, yana kallonta, ya din ga fatan Allah ya sa muryar iman zai ji, ba ruma ce ta kira ta dame shi ba.

"Hello mai sunan baba"
Sak yayi da ba Muryar iman ya ji ba.

"Ya aka yi?"
"Amm dama, kiranka na yi na ji ya ka je gida, na gode sosai"
"Yayi" ya fa
a a ta
aice yana
arin kashe wayar.

Ruma ta ce "Dama Iman ce ta ce, na kira ka na tambayi ya ka je gida?"
Da sauri Iman ta ce "Kai Anty rumaisa" ta yi maganar tana kar
e wayar ta kashe.

"To me na yi kuma?".

Cikin shagwa
a iman ta ce "Meyasa zaki gaya masa haka, kar ya zaci wani abun fa".

"Wani abu kamar me?"
Iman ta ce "Bakomai" ta tashi tsaye ta ce "Ki kwana a kan gadon, ni sai na kwana a kan katifa a
asa".

Rumaisa ta kwanta ta ce "Ai ba kara zan yi miki in ce a'a zan kwana a
asa ba" Iman ta yi dariya, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shirin baccinta ta kwanta.

Har kusan
arfe biyun dare, rumaisa idonta biyu, rabon da ta ci karo da abun da zai hanata bacci, tun farkon shigarta hannun kidnappers, daga baya kuwa baccinta take yi, sai lokacin da ta ku
uta da Sabir.

A hankali ta tashi zaune, ta na jin kanta duk ya yi mata nauyi, tausayin wa ma yakamata ta ji ne?.

Ta kalli in da iman take barci, ta girgiza kai 'Allah sarki Iman, a yadda ki ka bani labari ke yanzu gaba
aya ba ki da uwa ba ki da uba, sun rasu ba zaki ta
a ganinsu ba har abada, ba a san in da za a ga dangin su ba, ba ki da wa ba kuma ki da
ani ga larura.

Ashe ni kukan da
i nake, na ban san babana sai a hoto, wannan ke ce marainiya.

Allah sarki ammi, ashe da gaske mama take da take cewa aure
an ha
uri ne, ni na zata kawai abinci ake ci ayi bacci, amma a
wace mini
a a bawa kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta.
an ta ba shi da lafiya,
ayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a
wace mata
aya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a
wace Sabir ya auri
anwar anty aisha ya bata.

Kam bala'i wallahi da sai dai kowa ya rasa'.

Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?.

Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a
asa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta,
arshe a nan
asa ta yi bacci.

Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nisha
i a
asan zuciyarsa, dan
ari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan ya
i yadda ya sallama cewar ya fa
a soyayya, haryanzu tantama yake yi.

Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka.

Ta hau kan gadon, ta
auke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba
aya.

Wajen
arfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a
akinsa, ta zo a kaita makaranta.

Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta.

Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi
akin nasa.

Ciwon kwana
aya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru.
arasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe
in jallabiya ta ce "Sannu ka warke?".

Ya kalleta ya ce "Ina kwana?" Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce "Lafiya
alau, ya jiki?"
Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce "Baki san gatse ba ko?

Ban isa ki gaisheni ba?"
Ta ce "Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na
auka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?"
Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo.

"Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka
i amsawa wai sai an yi maka irin taka".

Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta.

"Barka da wannan lokaci ranka ya da
e, na sameka lafiya?" Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa.

"Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta".

Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje.

Sai dai a harabar gidan, ta ha
u da Mahmud, yana shirin fita.

Gaisawa suka yi, ya ce "Ya mai jiki?".

"Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi"
"Anya zuwa dubiyar nan kuwa?

Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta"..

Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta bu
e motar ta shige.

Sidi ya taho da sauri, ya ce "Ranka ya da
e, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne".

Mahmud ya ce "Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare" ya ja motar suka tafi.

Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata.

Can ta ce "Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna.

Allah ya bani abun da zan shagwa
a ta, in ta sai mata abubuwa".

Ya ce "Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu'a".

"Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza.
Chapter 69 · 0% Book details