← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 126

Sashe 4

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ja'ira ki na ji na ba zaki yi magana ba"
Rumaisa ta ce "Ina kwana"
"Lafiya
alau, ya ki ke ya
arfin jiki?"
"Na ji sau
i ai, har na koma makaranta ma"
"Ahh to Alhamdilillah, ya firgitar da ki ke yi fa cikin dare kin daina?"
"A'a ina yi wataran"
Gwaggo ta ce "Subhanallah, ki din ga addu'a sosai da sosai, dama zama a cikin wannan dajin ai dole ki yi gamo, wata
ila ma kin kwaso makarai.

Zan saka a ha
o miki magunguna, a ha
o miki da kayanki a kawo miki".

Da sauri rumaisa ta tari numfashin Gwaggo ta ce "A'a gwaggo, kar a kawo mini kayan nan yanzu, ki
aure mini su, ki
oye su sosai, kar ki bari wani abu ya same su, zan gaya miki lokacin da za'a kawo mini"
"To shikenan babu damuwa in sha Allah, zuwa sati mai zuwa zan aiko miki da magunguna"
"Ni fa lafiyata
alau, ba wasu aljanu da na kwaso"
"Idan ma kin kwaso ai ke ba zaki sani ba, kuma idan aka kawo magani ki ka
i yi, da kaina zan zo har kanon na zane miki jikinki"
Rumaisa ta yi shiru, gwaggo ta gama maganganunta, ta mi
awa mama wayarta ta
au jakarta ta fice zuwa makaranta.

Ringing
in da wayarsa take yi ne ya sanya shi farkawa daga baccin da yake yi, a hankali ya yi mi
a ya bu
e idonsa,
an guntun tsaki ya ja, dan ya ji haushin katse masa barcin da aka yi.

Ya mi
a hannu ya
au wayar, ya
aga ya saka a kunnensa.

"Assalamu alaikum warahmatullah, barka da safiya"
"Yauwa barka" ya amsa murya can
asa.

"Ya gida ya
ari"
Cikin
osawa ya amsa da "Alhamdilillah, waye?".

"Khalifa Usman wakili ne, na kiraka ne domin yi maka ta'aziyya tare da jajanta maka abun da ya faru da kai".

"To ka sa
a lamba, ba wanda yakamata ka kira
in ka kira ba"
Khalifa ya ce "Na sani, ba Mahmud Sharif Galadima ba ne?"
"Eh, Adam sharif galadima yakamata ka kira"
"Ba laifi bane idan kai ma an yi maka ta'aziyya ai, abun da ya shafi adam ya shafeka"
"Kai ka ga, abun da ya shafe shi shi ya shafa, ku je can ku yi abun ku, don't ever involves me, ba na son fuska biyu, wata
ila da har zuciyarka da gaske ka ke ka kirani ka yi mini ta'aziyya sai in amsa maka, amma kowa ya san abun da yake tsakaninsa da mahaifinkaa da kai kanka, jiya mahaifinka yayi masa ta'aziyya a kafafen watsa labarai, kai kuma yau ka kirani wai kana yi mini ta'aziyya bana son munafuncinku na
an siyasa, kar ka sake kirana" ya yi tsaki ya kashe wayar ya ajiye.

Ya tashi zaune yana mamakin tsabar rashin kunya na wasu
an siyasar, ya san da biyu ya kira shi, ba dan Allah ba.

Ya mi
e ya shiga ban
aki domin ya yi wanka.

Ya gama abun da yake yi, ya fito ya shirya, ya fita falo domin karya, a falon ya tarar da Samha da Fauziyya ga ruky da Mummy sai hira suke yi, kuma da alama hirar ta su na da ala
a da takawa.

"Wai ku ba ku da wata magana sai ta mutum
aya?

Look for something else mana, kowa adam adam ku bar shi ya ji da abubuwan da suka dame shi".

Gaban Mummy ne ya fa
i, yaushe Mahmud ya fara damuwa da lamarin adam?.

Fauziyya ta ce "Kawai muna
an yin hira ne a kan yadda abubuwa ke ta faruwa da shi, social media ma sai zancen ake yi".

"Ni ma yanzu wannan yaron ya kirani,
an gidan wakili wai yana yi mini ta'aziyya, na ce kar ya sake kirana bana son munafunci da fuska biyu".

Waro ido Samha ta yi ta ce "Khalifa wakili kuma?".

"Shi fa, kar ma ya kuskura ya sakani a shirmensu ni bu
e masa aiki zan yi, rukky kawon breakfast zan karya"
'Mai wakili yake nufi da kiran Mahmud a waya wai zai yi masa ta'aziyya?' Samha ta tambayi kanta.

Tashi ta yi da sauri ta ce ta na zuwa, ta fice ta bar sashin zuwa harabar gidan, ta kira Khalifa a waya.

Sai da ta kira shi sau biyu sannan ya
aga.

"Wai me kake aikatawa ne da ka ke
oyewa?"
"Kamar me fa?" Ya tambaye ta cikin ko in kula.

"Kai ka ke sponsoring ake
atawa adam suna a gidajen jaridu ko?"
"Meye shaidarki na ni nake hakan?"
Cikin fushi Samha ta ce "Waye idan ba kai ba?"
"A tunaninki ni ka
ai ne ma
iyin adam?

Ai ba mahaifina ka
ai yake da burin tozartawa ba, dan haka bani da lokacin sponsoring
in wasu gidajen jaridu su
ata masa suna".

"To me kake nufi da kiran
aninsa wai kana yi masa ta'aziyya, shi ma janyo shi zaka yi cikin tsiyar ta ka?"
"Wow, kuna tare kenan few hours da kiransa har kin samu labari"
"Ka ga, kashedi zan yi maka, kar ka kuskura ka sanya Mahmud cikin shirmenka, na san ba zai wuce an ce maka baya shiri da shi da adam ba, amma ka sani har abada jini ya fi ruwa kauri, adam jininsa ne kuma ko ba jininsa bane ba, Mahmud ba irin wanda zaka yi wasa da su ba ne ka cimma burinka".

Khalifa ya yi dariya ya ce "Jini ya fi ruwa kauri, wane irin jini ne tsakanin ki adam da har ke ake wasan da ke?

Ko daa yake wata kusan ta fi wata ai, and ba ke zaki gaya mini abun da yakamata na yi ba da wands ba zan yi ba, ina da abun yi yanzu, see you later" ya kashe wayar sa.

Ajiyar zuciya Samha ta yi ajiyar zuciya cike da takaicin biye wa Khalifa tun a farko.

Rumaisa ce zaune da wandon uniform
in islamiyya a jikinta, sai vest tana suyar wainar fulawa ita da Abdallah.

Ta ce "Yaya Abdallah ka san me nake sha'awa?".

"A'a sai kin fa
a" yayi maganar yana zuba
ullin wainar a kasko.

"Ina so in ji na ce basir ne da ni, ya tayar mini"
Tsaki ya ja ya ce "Mahaukaciya ba zaki yi hankali ba, kin san meye basir ciwo ne fa".

"Eh, kawai dai burgeni yake yi, idan na ji an ce ina da basir"
"Sai ki yi ta yi ai, ba ki san masifar da ke cikin sa ba, ki
je ki ji da yawon gudawarki da ki ka saba ba yau ba gobe, ya fiye miki alkhairi a kan ace basir ne da ke"
Tura baki ta yi, ta saka hannu ta gutsuri gefen wainar fulawa ta saka a baki, Abdallah ya ce "Kin ci a taki"
ar wannan
in?"
"Eh, uban wa ya ce ki ci ba a raba ba?"
Ta mi
a hannu ta ce"To bari na cinye guda
ayan na ci a tawa" ya buge mata hannu ya ce "Baki isa ba uwar son zuciya"
Sallama suka ji, suka amsa gaba
aya, maman habiba ce, rumaisa ta gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska, tare da tambayarta ina mama.

Rumaisa ta ce "Mama tana cikin
aki ki shiga"
Bayan ta shige, Abdallah ya kalli rumaisa ya ce "Ina fatan ba wani laifin ki ka aikata ba?"
"Ni ba abun da na yi".

"Wallahi idan
ararki ta kawo sai kin daku?"
Shiru ta yi masa ta hau lasar yaji.

Maman su habiba ta
an da
e, sannan ta fito, mama ta rakota sai dai fuskar mama babu walwala, ruma sai da ta
an tsorata ta yi zaton ko
arar ta ta maman su habiba ta kawo, amma bayan tafiyarta ta ji shiru mama ba ta yi mata fa
a ba.

Amma gaba
aya maman ta sauya, damuwa sosai ta bayyana a kan fuskarta.

Rumaisa ta ce "Mama
arata a ka kawo miki ne?

Wallahi ban yi wa kowa komai ba"
Mama ta ce "A'a ba
ararki aka kawo ba"
"To menene, na ga ba kya son yin magana"
"Bakomai".

Gaba
aya suka lura da yadda mama ba ta walwala, duk wanda ya tambayeta menene sai ta ce bakomai, mai sunan baba kawai ta iya gayawa abun da yake damunta.

Washegari da safe, bayan tafiyar rumaisa makaranta, jikin mama ya tashi, sai da aka kai ta asibiti likita ya dubata, sannan suka dawo gida.

Kusan kwanaki biyu kenan mama babu lafiya, babu walwala har rumaisa ta fara koke-koke.

Cikin
arfin hali mama ta ce "Ba zaki yi mini Addu'a ba sai ki sakani a gaba kina kuka?"
"To ba kin
i gaya mini abun da ya same ki ba?"
Mama ta ce "Ai na ce miki bakomai, amma shikenan tun da ba zaki yi mini Addu'a ba".

Rumaisa ta cigaba da kukanta, yayin da mama ta samu bacci.

Wayar mama ce ta fara ringing rumaisa ta
aga sai ta ji muryar ammi.

Suka gaisa ammi ta ce "Rumaisa ina maman taki?"
"Bacci take ba ta da lafiya"
"Subhanallah, meya sameta?"
i gaya mini" Rumaisa ta yi maganar tana fashewa da kuka.

"Ya salam, yi ha
uri ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta ji sau
i, ki daina kuka kin ji ko?"
Rumaisa ta amsa da "To".

Lokacin islamiyya ya yi aka gama girki, rumaisa ta ga abincin ba nama ba kifi, ba salak, ta
i ci, ta je ta shanye youghurt
in da aka sai wa mama ta kasa sha.

Ta saka uniform ta tafi islamiyya.

Da yamma ta yi suka dawo daga islamiyya, mai wanke-wanke ya kama, mai
ora girki ya
ora.
Chapter 4 · 0% Book details