← Book details Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 126

Sashe 107

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam bai ga rumaisa ba sai bayan sallar magariba, ya fa
akin unexpectedly ya tarar da ita a zaune tamkar zata fashe, gashin nan ya sha gyara, ya kwanta sai
yallin mai yake yi.

Gashi ta wani
ara fresh, dan gyaran jiki suke sha tare, an yi mata lalle kamar ita ce amaryar,
akin kansa sai
amshin turare yake yi.

Cikin sanyin jiki ya
arasa, ya ce "Mimi dan Allah ki saurareni, i will explain to you"
"To hell with your explanations, bana son ji" ta yin
ura za ta tashi, ya sha gabanta.

"Rumaisa kin fi kowa sanin ni ba mutumin banza bane ba, wallahi bani na gayyato Samha gidan nan ba, kawai ganinta nayi unexpected".

"Dama na ce kai ka gayyato ta, idan ma gayyato tan kayi ina ruwana?

Dan Allah ka rabu da ni, bana son jin duk wani bayani naka"
"Kiyi ha
uri dan Allah"
"Ai ni baka yi mini komai ba,
arewa saura tayi tsirara ka kalleta, shi ma duk cikin kuskure ne" Duk yadda ya so ta tsaya ta fahimta ta
i, tayi mursisi ta din ga yi masa rashin mutunci.

Tun da ake fa
ar fitsararta, bata ta
a gwada masa tijara muraran ba kamar yau, sam tayi burus ta
i fahimtar sa.
arewa ma, yana fita ta kulle
ofarta.

Gaba
aya Adam ya rikice, ya rasa abun da yake yi masa da
i, rarrashin duniyar nan, ruma tayi burus da shi, da sassafe ta fita ta tafi gidan ammi, aka cigaba da shirin biki, tamkar babu abun da ya faru.

Rashin ganinta a gidan bayan ya tashi, ba
aramin
aga masa hankali yayi ba, ya fara zuwa gidansu, amma ya tarar da ita tamkar ba abun da ya faru, tana ta hidimominta,
an uwan su ammi na gombe, duk sun hallara.

Daga nan gida tayi tafiyarta gidansu, nan ma gida ya cika mutanen katsina duk sun hallara.

Ana ta shirin biki, da daddare su habiba suka zo ita da mamanta, idan da aikin da za a kamawa su mama, ga su Hauwwaliya, ai tuni ruma ta manta da damuwarta, ta shiga cikinsu suka cigaba da ta
ararsu.

Aliyu tun da yaga Habiba yake shiga yana fita.

Ruma ta ce "Habiba baki da mutunci fa, ki ke soyayya da yaya Aliyu ba labari, kuma ko gaisheni ba kya zuwa yi"
Habiba ta ce "Sannu mama" suka tuntsire da dariya.

Habiba ta ce "Kamar in janyo lokacin candy rumaisa, ina
aunar Yaya Aliyu kamar me, Ruma aure da da
i dan Allah?"
Hauwwaliya ta ce "Eh
an gaya mana"
Ruma ta ce "Eh to, ba nace babu ba, bana ce akwai ba, idan kun je kwa gani, idan ku ka yi sa'a ku ka auri irin mijina, to kun dace, ni da mijina bani da matsala, sai danginsa 'yan bala'i.

Ku san kowa da kalar jarrabwarsa a gidan aure".

Hauwwaliya ta ce "To, Allah ya sassauta mana"
Suka amsa da Amin.

Da Adam ya koma gida, aka ce masa ruma ta tafi gidansu, dan haka ya tafi yana fatan Allah ya sa ba ta fa
i wani abun ba.

Wayar mama ya kira, suka gaisa ya ce mata rumaisa ta zo, zasu tafi.

Ba ta son tayi musu ko wani abu da zai sanya, a gane sa
ani suka samu, dan laila ta garga
eta sosai a kan haka, ta ce mata duk wata matsala, in dai za su iya warwarewa a tsakanin su, kar ta bari wani ya ji, balle ya shiga.

Galibin aure yana samun matsa a dalilin sako mutum na uku a cikin matsalolin auren.

Bayan motar ta bu
e ta shiga, ko kallonsa ba ta yi ba.

Har suka je gida ba ta kula shi ba, shi ma kuma bai iya ce mata komai ba, duk da
asan zuciyarta har ta fara jin tausayinsa, dan a ki
ime yake sosai da sosai.

Da suka je gida ma, a bu
e ta bar masa motarsa ta yi shigewarta cikin gida.

Ko tayi niyyar daina fushin, da ta tuna yadda ta ga Samha a tsaye a gaban sa, ta turo
irji sai wani irin ba
in ciki ya turnu
eta.

Wanka tayi, ta je kitchen ta damo kununta, ta koma
aki tana sha.

Ita kanta missing
in sa take yi sosai da sosai, saboda sun yi wani irin sabo sosai da sosai.

Kamar mara gaskiya haka yayi sallama a
akin, ta amsa masa
asa-
asa.
arasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Rumaisa".

"Na'am" ta amsa a da
ile.

"Yanzu kina tunanin zan iya aikata abun da bai kamata ba kenan?

Yakamata ki fahimce ni, ya ci ace kin san halina, wallahi rumaisa babu wani abu da ya faru, abun da ki ka gani ma is not intentionally ban san me ma zan ce miki ki yarda da ni ba.

Amma dan Allah kar ki kawo komai a ranki".

"Amma fa tsayawa ka yi kana kallonta, fisabilillahi".

"Rumaisa a rayuwata bana tunanin akwai wanda na ta
a bi ina bawa ha
uri, kamar yadda nake binki a yanzu, dan Allah ki yi ha
uri, ko sai na dur
usa
in a kan gwiwoyina?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki dube ni mana, kiyi ha
uri Please" yayi maganar yana ri
e hannunta cikin nasa.

"Na ha
ura amma dan Allah kar ka sake kulata, wallahi ji na yi kamar na je kitchen na samo ta
arya na zo na rotse mata kai.

Kawai ta wani tsaya ta gantsare a gabanka, wallahi na ji haushi"
Ya ce "Subhanallah, duk ba ta kai ga haka ba, nima ban ji da
i ba amma ki yadda da ni, ai ni namu sun isheni, me zan kalla a na wata"
"Abun da bai fi murfin jarkar faron ba?"
Yayi murmushi ya ce "Har laifukana na baya za'a tayar kenan?".

"Eh
in, ka je ka kalli naka ko na Samha"
Yayi murmushi ya ce "Allah dai ya bada ha
uri"
Ta amsa da "Amin"
Ya rungumeta ya ce "I so much miss you, smile please"
Ta lashe cokalin hannunta ta ce "ba zan iya ba yanzu, idan na ce zan yi murmushi yanzu, ya
e kawai zan yi.

Ka ci abinci kuwa?"
"A ina zan ci, tun da baki bani ba?"
Ta ce "To mu je na sama maka abun da zaka ci"
"Yauwwa my dear, ana so na ana kaiwa kasuwa, an damu da ni amma ana ta wahalar da ni"
Ta kalleshi ta ce "Ka ke dai so na"
Ya ce "Na yadda".

Ta ce "To amma sai dai ka goya ni, ka kai ni kitchen
Ya dur
usa ya ce "Zo ki hau"
Aikuwa ta mi
e ta hau bayansa tana dariya, ya goyata a bayansa, har kitchen.

A ranar dai suka shirya, rumaisa tayi iyakar
arin ta wurin bin shawarar da anty laila ta bata, na cewa idan har namji zai iya yi miki laifi ya baki ha
uri, to ba
aramin kimarki yake gani ba, ba kowann namiji ne zai yi ba dai-dai ba ya nemi afuwarki, sai ma yayi
arin nemo wani laifin ya jingina miki, duk dan kar ya nemi afuwarki.

Sosai aka shiga hidimar biki, ka'in da na'in, mai sunan baba kai ya
au caji sosai da sosai, abunka da wanda bai saba da hayaniya ba, nan da nan sai ciwon kai.

Gidan marigayi galadima Sharif ma, ya cika ya tumbatsa, mutane sai kaiwa suke suna komowa.

Mummy kuwa ba gaira ba dalili take tsinewa auren, tare da mummunan baki a kan haka.

Rumaisa kuwa ba ta a nan bata a can, takawa sai mita yake a kan ta nemi wuri ta din ga hutawa, kar sai an kammala biki, ta zo tana ciwon jiki.

Ranar da aka yi dinner rumaisa tayi kyau, haka amarya Iman da mai sunan baba, shi gaba
aya ma kunya yake ji, ko
aga kai baya son yi ya kalli taron jama'ar nan.

Yazo wurin nan ne kawai saboda iman ta matsa.

Kamar da bikin rumaisa a wannan karon ma, kaiwa da komowa zaratan samarin gidan maman suka din ga yi, sanye da kaya iri
aya a jikinsu gwanin sha'awa ango ba shi da wasu abokai, sai classmates sai
annensa.
awayen ammi sun yi mata kara sosai da sosai, suka din ga li
i suna kaiwa da komowa, duk wanda ya ga couples
in sai ya ce masha Allah, saboda kyau ne ya ha
u da kyau, duk da bai kai iman haske ba, amma kallo
aya zaka yi masa ka ce kyakkyawa ne.

Bayan an kammala dinner suka taso, Mahmud ne ya
aukko su a motarsa, Iman sai hamma take yi, saboda ta gaji.

"Kin gaji ne?" Ya tambaye ta lokacin da ta kashingi
a da seat
in motar.

"Eh yaya umar, ko ina ciwo yake mini"
Yayi murmushi ya ce "To sannu, idan kin je gida ki kwanta ki huta sosai"
Ta ce "To ango"
Yayi murmushi, suka fara kaita gida, sannan suka wuce Mahmud ya kai mai sunan baba gida.

Washegari aka
aura aure, turaki ne yayi wa Iman waliycci.

Aka
aura auren Umar Mahmud da Khadija Muhammad Galadima.

Ayshercool
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR
DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO.

SHIN
URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION?

KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE
I KINA HASKAWA?
Chapter 107 · 0% Book details