Sashe 99
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abokanki kyautuka ba amma ke ko da wasa ban ta a ko saka maki katin wayar daya kai darajar ari biyar ba. Don kar ki gane komai yasa na gaya maki ban da waya amma sai kika ban taki wayar, haka zalika na dinga yi maki arya don kawai baki ganina saboda a lokacin ina cikin hidimar bikina ne da A'isha. Bayan anyi auren ne na zo gareki da zummar na cigaba da yaudararki har na gama karatuna na tsere daga rayuwarki ashe kin gane nayi aure ki kai min magana kuma kika nuna min acin ranki har ki ka ce min duk wanda ya cuci wani Allah Ya saka mai. Naso warai mu shirya kika i baki aya kika tsane Ni kika fita sabgar kowane namiji amma ban ji komai ba sai naga ma a lokacin ai ke kika sani kawai don haka na cigaba da kula da matata na bar ko tuna mai sunanki, idan an kira ma sai nayi dogon nazari nake gane inda na ta a sanin mai irin sunan. Lafiya lau muke rayuwa da matata, har ta samu ciki wanda nayi murna kamar me, duk da cewar ina azabtuwa da abubuwa da dama daga matar tawa, irinsu raini bata ganin girma na sam ban isa idan zata fita ba ta tambayeni ba, idan nayi mata magana sai tace tana da ku in mota don haka tsayawa tambayar me zatai min? Daga arshe ma ta koyi mota duk inda zata motata take auka kawai ta fice ban isa nace mata don me ba? A haka ta samu ciki na sha ba ar wahala domin daina komai tai na gidan tace ita cikinta ba zai wahala ba, don haka nike komai na gidan wanki, girki, da wanke-wanke duk nike mata su. Bayan suna da kwana biyu sai ga wata yarinya an kawo mata daga gidansu wai ita ce zata dinga mata reno da sauran aikin gida ita kam bata iyawa. Abin ya ata min rai sosai domin na lura duk bayan lokaci sai A'isha ta fito da sabon salon iskanci wanda ban isa nace ga nawa ra'ayina ba kan nata. Komai na gidan Aminatu ke yinsa kasancewar yarinyar na da natsuwa da hankali sosai take da tsabta yasa naji da i wani wajen na zuwanta gidan. Babu ruwan A'isha haka take barin yarinyar da yaron ta fice sabgarta don yanzu ita ma ta zama ar siyasa don haka bata zama gida ko da yaushe tana waje idan ta dawo gidanma tare da jama'arta take dawowa maza da mata. A takaice dai bata da lokacina ko na Yarona sai na hidimar siyasar da take yanzu nayi mata magana tai min rashin mutunci ta tafi gidansu na auka idan naje iyayenta zasu yi mata fa a bayan na gama karanta masu zaman da nake da ita sai naga sun goyi bayanta har suna i rarin jin zafi nake mata so nake na ga tana zaune kamar yadda nake zaune ina jiran wasu an canji daga gwamnati wanda ba abin da za su yi mata ga iyali ta fara tarawa. Haka dai naita basu ha uri amma duk da haka sai da ta shafe sati uku bata dawo ba sai dai nike zarya kullum ina ara bata ha uri da iyayenta. Sai da yar na samu ta dawo, amma fa da sabon salo ta dawo na raini da wula anci, gadara da nuna min isa ko shan waye haka zata ci min mutunci ba ruwanta da mijinta ne Ni. Yawo kuwa sai tai sati bata nan kuma yarinyar nan take barma yaronta haka bata gayamin zata yi tafiya sai dai idan ban ganta ba na kira wayarta sai ta gayamin ai bata gari ne lafiya nake nemanta? Abin na matu ar damuna ko da yaushe na dawo daga aiki Aminatu mai aiki nake iskewa ta ha a min abinci tai ma yaro wanka komai na gidan a hannunta yake. Sannu a hankali sai na fara jin cewa gwara na auri yarinyar tunda ta saba da kula min da gida haka ta iya rainon Yarona tamkar ita ce ta haife shi. Ban oye mata ba, amma sai Aminatu tace min a'a tana tsoron Hajiya A'isha nayi ha uri, Ni kuma sai na kasa ha uri domin a lokacin sai A'isha tai wata bata ma asar tana wata asar hidimar ta. Kin san namiji da naci kan abin da yake ganin zai ba shi mafita don haka na dage gun cusa ma Aminatu soyayyata har kuwa nai nasarar saka mata soyayyata a cikin zuciyarta ta amince zata aureni amma ba gidan zata zauna ba zan ware mata gida daban. Na amince domin gaskiya na gaji da ba ar wahalar da nake da sunan ina da aure kuma, kai tsaye naje gun iyayen Aminatu da farko basu amince ba sai daga baya sannan suka amince aka tsaida maganar aure wata hu u, matsalar da aka samu ita ce, sai na dawo da Aminatu gidana ta ci gaba da zama, ban san wa ya gayama A'isha maganar aurena da Aminatu ba sai gata a fujajan ta dawo ta kama yarinya da duka da yar na wace ta, na tabbatar mata da cewar aurena da Aminatu babu fashi sai dai duk abin da zata yi ta je tayi na gaji da iskancin da take min. Mun yi sati guda ana wannan bala'i kwatsam! Rannan sai jin ihun Aminatu nayi ina zuwa na iske A'isha ta caka mata wu a a ciki , tsabar ru ewa tasa na fisge wu ar daga cikin Aminatu sai kawai jin an sanda nayi a baya na suna cewa "Kar ka matsa daga inda kake ." A kotu ne naji daga bakin Lauyar A'isha wai ta shigar da Ni ara na nayi wa mai aikinta ciki kuma na kashe ta. Nasha ba ar wahala gun shari'ar domin ta auki babbar lauya wadda kowa yasan ta haka sauran Lauyoyi ke shayin buga shari'a da ita watau Barista Alawiyya Bello Gareji, sai da komai nawa ya are amma har yanzu ba a gama shari'ar ba, don Allah ki taimake Ni Jiddah domin naga hotonku ke da Barista Alawiyya ki yi min ari ki fahimtar da ita cewar alhakin ki ke ya kama Ni ban kashe kowa ba." Tun da ya fara bata labarin kanta ke asa har ya gama. Lallai yana cikin matsala ko bai fa a ba jikinsa ya bayyana, kuma insha Allah zatai arin watar mai ha insa. Ta kalle shi tai murmushi tace, "Kar ka damu a wane gari kuke shari'ar ne? Yaushe za ku koma kotun ne?" Cike da farin ciki ya sanar da ita a Kano suke shari'ar Yau saura sati guda su koma Kotun. Tai mai al awarin zata taimaka mai, ko waya bai da ita sai ta zare sim card inta ta ba shi aya daga wayoyinta tace ya ri e zata aiko mai da sabon sim card yanzu idan ta shiga gida don su dinga waya tana jin abubuwan dake faruwa kafin zuwan ranar . Nan ta bar shi yana kallonta irin kallon nadama da mamakin yadda ta koma kamar ba ita ba. Bata jima ba sai ga wata ar aiki ta kawo mai sa on cikin ba ar leda ba aramin mamaki ya bayyana a kan fuskar Abubakar ba ganin iyayen ku i a cikin ledar tare da sim card in sai wata ar takarda da ta rubuta. "Ka je ka samu kaya masu kyau, kuma ka kula da kanka kafin na shigo Kano in." Tana komawa ta iske miss call in Prince dana Yusuf Matashi sai ta fara bin kiran Prince domin yana cikin ranta daman, tana son ta dawo ta kira shi ta ji ko ya tafi inda ya ce mata an tura shi aiki. Kiran farko ya aga kiran har da ajiyar zuciya. "Haba Princess anya kuwa kina jin yadda nake ji kuwa?" ar dariya tai tace, "Ai Prince na fi ka ma jin abin da kake nufi kana ji indai ana so da aunarka ne." "Haba Princess ban ga alama ba, don ko da yaushe Ni ke cikin tararrabin kar ki ku uce min." "La,la,la, Prince haka ma zaka ce yanzu? Duk yadda sonka ya yi min kamun kazar Kuku kace min wai ban kai ka ba? Ni fa na auka ma son da nake maka ya ninninka wanda kake min domin Ni duk abin da nake kana cikin raina." "To ai Princess ban ce baki sona ba, kawai dai na ce nawa yafi naki yawa son." Tasan ko za su shekara ba zai amince da cewar tafi shi son ba don haka ta aje maganar ta je wata. "Yawwa Prince, zan shigo Kano nan da kwana shida insha Allah kan wata shari'a da zan yi." Tana jiyo saukar numfashinsa, ya ce cikin farin ciki, "Ban mu kashe Princess, har kin sakani cikin nisha i da jin da i, duk da ban gari amma zan koma kafin ranar dama na tsara daga nan gun ki nayo kawai na kwashi auna, na ganki naga kyakkyawar fuskarki nai tozali da kwalliyarki mai imauta Ni." Itama cikin farin cikin tace mai, "Ai baka kaini farin ciki ba kan hakan, domin ina son naga na tasa ka a gaba ina ta kallonka ina kallon dogon hancinka, ina kallon fararen idanunka, kana halakar da Ni da murmushinka mai ara jefa min aunarka a sassan jikina." Duk lokacin da Jiddah ke bu e baki tana gaya mai irin kalaman nan sai ya dinga jin tamkar ya bu e ido ya ganshi a bayyanar jama'a ana mai Allah sa alheri an aura masu aure. Yana son soyayya, Jiddah ta iya soyayya, yana son kulawa Jiddah ta iya ba shi kulawa, yana son shagwa a Jiddah ta ware da iya shagwa a don haka duk bayan sakan yake mutuwa yana dawowa kan soyayyarta. "Prince shi ne za kai banza da Ni ka yale Ni ina ta yi maka magana?" Cike da shagwa a take maganar, abin dake ara zuzutar da shi kenan idan yana jinta. Shima cikin nashi salon shagwa ar ya ce mata, "Afuwan Princess ina can ina tunaninki ne shi yasa kin san ko da muna tare a waya indai ba gani ga ki ba sam ban daina tunaninki." Farin ciki ya sake mamaye zuciyarta