Sashe 93
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Prince? Allah ka fini kyau sosai prince kana da hanci gaka da fararen idanu ga fuskarka siririya daidai misali gaskiyar magana ka dinga gode wa Allah daya azurtaka da kyawu na gasken-gaske ." Yana murmushi yana kallonta wai Princess ce ke cewa yana da kyau har ya fita kyau? Tabdijam! Shi da yake lalata yini guda wajen tunanin irin kyawunta da dirinta wanda babu wanda zai kalleta bai so ta zama abar mallakarsa ba. Jiddah na da kyau na gaske wanda kallo guda ma kana iya fahimtar yadda Allah Ya azurta ta da kyawun jiki dana fuska. Kallonsa tai ta ta e baki tace, "Ka tashi ka tafi gidanka kar da a zo nemanka ba ruwana." Kallon kin cika rigima ya yi mata ya sadda kansa asa don bai san abin da zai ce mata ba kan maganar da tai mai, ya lura ita ma zatai kishi amma yana fatan tai kishi irin na an boko wanda ya halarta bana hauka ba wanda matan yanzu ke yi ba. Ganin ya kasa bata amsa yasa tai murmushi tace, "Na baka tsoro hala, na tuna maka da matanka?" Baice mata komai ba dai sai murmushi da ya yi don ya lura Princess dabance ko a jerin matan. Sai taji itama kamar ta za e da yawa don haka sai ta sauya zancen da cewa, "Allah ka je gida kai wanka ka ci abinci domin na fahimci baka ci komai ba kana tare da yunwa." Girgiza kansa ya yi alamar bai jin yunwa. Itama girgiza kanta tai alamar yana jin yunwa fa da gaske take. i ya ji sosai a ransa yadda Princess ke fahimtar abin da ke damunsa kai tsaye na nufin ta damu da shi sosai. Tabbas yunwa yake ji ya kasa cin abincin ne saboda sam bai masa ba, yana son jin abinci mai da i a bakinsa sosai yake son da i amma ya rasa yanda zai koman ya kawo mai da in ba a san yadda za a sarrafa mai shi ba ya bada abu mai ma'ana ba, don haka yafi son cin abincin kan titi da ya ci abincin gidansa. Ko da yake mutane nayi mai mummunar fahimta kan hakan har ma wasu na cewa ai yana siyen kayan abinci mai da i yana oyewa a akinsa bai iya ba matansa sai dai su ya barsu da tuwo da tsakin shinkafa ko da yaushe, shi ka ai ke cin da i a akinsa ba ruwansa da matansa da yaransa, sosai abin ke ona mai rai duk lokacin daya tuna abin ji yake ransa ya aci sosai har ya ji ya tsani aurenma baki aya. Jiddah lura da tai ya yi zurfi a tunani daga maganar wasa sai taji bata ji da in hakan ba, don haka ta dube shi fuska cike da shagwa a tace, "Prince shi ne ina maka magana za kai banza ka yale Ni ko? Gaskiya Ni ba zan yadda ba." Magana take cike da shagwa a abin da yake matu ar so kenan a rayuwarsa yaga mace na yi mai shagwa a abin na bala'in birge shi sosai, don haka sai ya samu kansa da manta halin da yake ya saki baki da hanci yana kallon yadda take mai shagwa a abin birgewa. Samun kansa ya yi da lallashinta tamkar wata aramar yarinya haka ya dinga lallashinta yana jin shau i sosai na ratsa dukkan jikinsa na aunarta. Haka suka kwashe tsawon lokaci suna kwasar soyayya inda Jiddah ta dinga zuba mai shagwa a yana biye mata abin nayi mai da i har dai Hajjo ta gaji ta le o tace basu ji an kira sallah bane ba? Kan dole suka tashi ba don ransu na so ba ta raka shi har zaure, a can ma sai suka sake bu e wata sabuwar firar suna ta dariya suna jin farin ciki tamkar karda su rabu. Mustapha ya kalli Jiddah kallo na so da auna ya ce, "Allah ji nake tamkar na sace ki kowa ma ya huta Princess. Kinga yadda ki ke da bala'in kyau kuwa wai? Allah duk wanda ya sameki ya yi dacen mata ta nunawa a cikin jama'a a baka lambar yabo." Sadda kanta asa tai tana murmushi tace, "Kai fa don baka ganin kanka ne kawai yasa kake cewa ina da kyau, amma nesa ba kusa ba ka fini kyau gaka an kyakkyawan gaske uwa uba gaka an gayu, gaskiya ina matu ara gode wa Allah da Yasa na sameka a lokacin da sam ban zata ba, lokacin da ban ta a tsammanin zan samu kamar ka ba Prince." Ajiyar zuciya ya yi yana murmushin dake ara masa kyau ya ce mata, "Wallahi Princess har mamakin kaina nake akan ki baki aya komai nawa ya sauya tun daga kan wasu daga halayena da tabi'una duk sun sauya saboda soyayyarki don darajar Allah ki amince ki ci-gaba da tafiya dani cikin rayuwarki, sannan ki dinga ban shawara kan duk abin da kika ga ban daidai ba don haka shi ne soyayyar gaskiya." Cike da fara'a tace, "Tabbas naji da in maganarka amma don Allah Prince kaima ka dinga gayamin gaskiya kan dukkan abin da ya shafe Ni zan murna da hakan sosai da sosai." Wayarsa ya kalla yaga yanda lokaci ya ja sosai don haka ya kalleta kamar zai kuka ya ce, "Princess zan tafi nayi sallah naga lokacin ma sauri yake ko dan yaga muna tare ne yasa yake sauri Yau oho." ar dariyarta ta amsa mai da cewa, "Shike nan Prince ka je kawai Allah Ya tsare min kai Yasa ka kasance cikin farin ciki da natsuwa Ya bu a maka dukkan ofofin alheri." Farin ciki fal ransa ya dinga amsa mata da "Amin Ya Allah Princess." Abin yana birgeshi daman ya ji ana mai addu'a sai ya ji yafi kowa samun dace da macen kirki. Haka suka rabu suna agawa juna hannu kowa fuska cike da annurin jin da Jiddah na komawa taga miss call na Alawiyya dana Baffa har dana Maman Alawiyya ba adadi don haka ta fara kiran Baffa don jin abin da ke faruwa. Cike da dattaku yake maganar, " iyata kina ina ne tun azun nake nemanki cikin gidan nan baki ba jikokina?" Sai a lokacin taji cewar bata kyauta ba, don kawai Alawiyya sai ta bar gidan ba sallama? Amma ya zatai hakan shi ne daidai bata san ko da wasa Alawiyya ta auka cewa tana son mijinta don haka ta bar gidanma baki aya. Cike da jin kunya tace mai, "Baffa ina Kano ai." "Kina Kano fa kika ce? Me ake yi ne a Kanon da kika tafi ba sallama Jiddah?" Hawayenta suka dawo don haka sai kawai ta fashe da kuka tace, "Baffa Alawiyya ce wai tace ... Kuka ya hanata magana don haka tai shiru tana jan majina. Baffa yai murmushi ya dubi Alawiyya dake zaune gabansa tana ta kuka ita ma ya girgiza kansa ya ce, "Saboda hakan kika bar gidanku kika tafi Jiddah? Yanzu kin kyauta min kenan da za ki yi fushi ki kwashe min jikoki kibar gida? Me nayi maki Ni to?" kukanta ya ara arfi sosai ta cigaba da ba shi ha uri tabbas tayi laifi mai girma amma ranta ne ya aci ta rasa abin da zatai don haka taga dacewar barin gidan kawai, don haka ta bar gidan tare da yaran cikin tashin hankali. Baffa ya jima yana mata nasiha ya are da cewa, "Ki kwantar da hankalinki babu wanda ya isa ya yi maki dole kan aure ko za ar mijin da za ki aura iyata sai wanda kike so ya kwanta maki a rai shi ne kawai wanda zan ba aurenki amma duk na yi maki iyaka da su baki aya harma da Mansur in babu wanda zai sake takura maki don haka gobe ki dawo gida na kammala maki komai na karatunki ranar Monday za ku fara karatu, ki yi ha uri da abin da ar'uwarki tai maki bata kyauta ba, kin san yadda mu ke mu maza ba ruwanmu da cewar waccan macen idan na aureta akwai kunya ko wani makamancin haka, ku mata kune kukasan kunya kan aure banda maza basu da kunya kan mace." Sai a lokacin ta tsaida kukanta ta gode mai tace gobe suna hanya ita da yaran insha Allah. Bayan tai sallah ta kira Maman Alawiyya ita ma dai kan tafiyarta ce tai mata fa a sosai tace maza ta koma gidansu gobe kar ta sake jin irin wannan ya faru tabar gidan Baffa. Itama ha uri tai ta bata har ta sauko suka gaisa sosai ta ara da yi mata nasiha sosai suka gaisa da Haidar ta kashe wayar ta kwanta tana jin tamkar an auke mata nauyi. Tun suna waya da Mama take ganin kiran Alawiyyar na shigowa wayarta ta share har ta gama wayar tana ta kiranta amma ta aga kiran, don har ga Allah taji haushin abin da Alawiyyar tai mata wai ta za a mata mijinta matsayin mijin da zan aura akan me to? Kenan tana nufin zan iya kishi da ita har wata rana su yi fa a abin kunya kenan ya tabbata ace sun yi fa a kan namiji kuma tasan indai zata auri Faisal wata rana sai aya ta ga laifin aya. Don haka zata nuna mata kurenta ta hanyar kulle ta kwana biyu. Cikin dare online ta hau suka ha u da Prince inta suka dinga amayar da ruwan auna kowa ya fito da ciwon da ke kwance a asan ransa kan soyayya,anyi aman kalaman auna anyi ma soyayya fata-fata kamar wasu sabbin amare ranar farko haka suka raya daren da nuna auna ga juna ta hanyar bayyana abin da ke cikin zukatansu. Wajen arfe uku na dare sukai bankwana ba dan sun gaji ba sai don gobe zatai tafiyar safe wanda shi ne zai kai su tasha su hau mota da safen. Ko bayan sun bankwana kowane kasa barci ya yi sai ajiyar zuciya da karanta sa on nin juna da sukai. Jiddah bata ankara ba sai jin kiran Sallah tai, abin ya bata mamaki warai yadda ta kwana ido biyu kan soyayya ta manta yadda namiji ya ci mata mutunci ya raba ta da farin cikinta yasa ciwon hawan jini ya kamata