Sashe 133
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ya zo take kukan." Sai a lokacin ya kula da mutumin ma dake zaune a gun ya shafa eyarsa ya gaida shi, sannan ya shiga goge mata hawayenta yana yi mata ra a dole ta saki dariya tana sunne kanta asa. Baban Jiddah yai gyaran murya sosai ya ce, "Alhamdulillah! Ko yanzu na mutu na gode wa Allah tun da naga wanda Jiddah ke aure naga yadda yake sonta da kula da ita haka kuma naga jikokina na gun Jiddah su na cikin kyakkyawar rayuwa haka naga anen Jiddah har da aikin yi tabbas burina ya cika saura fatana ki yafe min Jiddah don Allah." Jiddah tai ajiyar zuciya tace, "Ba komai Baba ban ta a ri e a raina ba tun da na mallaki hankalin kaina nasan daman haka addarar rayuwata take don haka Allah Ya bamu ikon sauke ha in juna dake kanmu baki aya na ji da in ganin anina sosai har ma da aikinsa tabbas mun zama abin so ga danginka tun da yanzu mu ma mun zama mutane muna da aikin yi muna da ku i muna da komai. Alhamdulillah! Naji da i sosai Baba." Daga nan kai tsaye gidan Jiddah suka matsa mai suka tafi tare ya ga gidan Jiddah ya sake jin da i sosai a ransa sai ga abinci kala-kala daga gidan Maryam wai a ba Baban kafin ta zo su gaisa tun da bai je gidanta ba, ba a auki lokaci ba kuwa sai gata ita ma ta iso akai ta fira gwanin da i suka tafi tare ya je gidan Maryam ita ma yasa mata albarka ya sake yi masu nasiha sosai ya tafi cike da farin ciki. Hafsat sai da tai laushi sosai sannan Alawiyya ta sake ta dole ta koma gidansu ta natsu har ta samu mijinta tai aure Allah Ya so ba bai da mata ta rasu sai yaranta da ta bari manya ne mata da maza su ne suka zame mata koshiyoyi a cikin gidan ga shi uban na son yaran bai ganin laifinsu sam. Haka ta ha ura ta zauna bata isa da su ba haka sai abin da suke so suke yi a cikin gidan. Cikin Jiddah na shiga watan haihuwa Maryam tace ta bar ma Jiddah Mustapha har sai ta haihu ya dinga kwana gidanta saboda kar ciwo ya kama ta cikin dare ba kowa gidan. Mutane da dama sun jinjina wa Maryam kan yadda take kauda kanta daga abubuwa da dama da Mustapha ke nunawa a gabanta kan Jiddah Ita dai takan yi murmushi kawai tace "Allah kadai yasan alherin da na samu zamana da Jiddah Ni da ita ba kishi sai aminci." Ita kanta Jiddar akwai masu kai mata zugar Maryam wai ta zama sakarai tana girka kishiya tana nemar wa kishiya ku i bata da wayau." Ita ma dai takan sace masu gwiwa ne ta hanyar gaya masu bata da kishiya sai abokiyar rayuwa a gidan aurenta. Ranar Juma'a da dare ciwon na uda ya kama Jiddah Mustapha ya auke ta suka nufi asibiti yadda yaga ta galabaita sai da yai ta kuka yana addu'ar Allah Ya sauke ta lafiya. Bata haihu ba sai gab asuba akai mai albishir da samun a namiji. Har lokacin bai natsu ba sai da yaga Jiddar sannan ya samu sararin aukar yaron yana kukan farin ciki sosai ya auki waya ya dinga kiran mutane yana gaya masu Jiddah ta haihu. Maryam ma ta ji da i sosai nan da nan ta shirya abinci ita da yara suka nufi asibitin su na ta murna suka auki yaron kowa na cewa da shi ya yi kama. Mustapha ya auki yaron ya ura mai ido sosai ya fashe da kuka ya ce, "Sunanka Uncle Salim ka ci sunan Uncle in Umminka kuma an'uwan Abbanka abokin Abbanka an wajen Hajjo." Jiddah tai wuf ta watsa mai ido ita ma sai hawaye suka zuba mata, ina ma ace yana raye take wannan rayuwar cike da aminci da galihu? Tabbas da ya fi kowa farin ciki. Kasancewar jaririn da Mamansa duk lafiya suke yasa aka sallame su ko dan asibitin ta rage mutanen da ke cike duk na ganin jaririn. Mutanen Abuja sun taka rawar gani domin kaya na gani na fa a su ka yo ma Jiddah abin ba a cewa komai, sai ga Yusuf Matashi da matarsa da nasu sha tara na arzikin sun kawo Alawiyya kuwa rasa me za tai ta yi don haka ta cike takardun gidan manta dake Kaduna ta ba jaririn. Ranar suna ba a magana domin an yi suna mai sunan suna wanda ba a ta a yin irinsa ba a kaf zuri'ar Jiddah data Mustapha wanda dole suka rufe kansu a aki suka dinga rusa kukan farin ciki. Ita kanta Hajjo sai a ranar sunan ta ji sunan yaron ba karamin farin ciki tai ba sai da tai kukan tuna Autanta sosai a ranar. Ba yadda Hajjo ba tai da Mustapha ba yabar Jiddah ta koma gidanta tai wanka ba ya ce sam bai iya barin matarsa da ansa shi tai ha uri kawai. Dole ta ha ura ba don ranta ya so ba. Sai bayan suna Mamar Jiddah ta zo ta ga jariri taga gidan Jiddah tai murna sosai don a gidan Maryam ma ta kwana gwanin da i abin. Deeni kuwa ba a cewa komai don har yanzu dai jiya iya yau ba cigaban ba komai cike yake da wahalar rayuwa komai ya tsaya mai aurenma ya kasa yi abin sai wanda ya gani ya koma abin tausayi kowa maganarsa yake da labarin tsohuwar matarsa Jiddah da yadda ta koma yanzu ake. To daman haka rayuwar take ai, idan ka cutar da wani sai kaga kaima ka kasance a cikin mafiyin halin daka kasa wancan in. Kaga shi kuma ya samu bu in rayuwa ta ko'ina har yafi arfinka bayan kai ke kake ganin ka fi arfinsa a baya. Alhamdulillah! A nan na kawo arshen littafin nan mai suna HA IN ALLAH. Sai mun ha u da ku a sabon littafina mai suna KISA KO AURE... Taku a kullum Haupha. 07081095452 Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office f0f8e48cb8894e0480efb6fd7d695060