Sashe 69
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kama kukan yana jin kansa a mugu azzalumi wanda ya so kansa fiye da tunanin kowa. A yanzu ji yake Jiddah ita ce kawai jin da in rayuwarsa, ita ce kawai wadda ke iya rufa masa asiri a rayuwar nan. Amma tana ina ? Yaushe zata dawo? Shin Hajjo zata amince ya maida Jiddah ma? Bai jin mahaifiyar Jiddah domin mace ce mai sanyin hali mai kauda kai da ha uri da sanin yakamata ba shakka a gunta Jiddah ta kwaso kyawawan halayenta. Ganin an buge wata guda ba Jiddah ba labarinta yasa Deeni fara cuku-cukun ha a ku in motar da za su kai shi Kano gun Jiddah. A yanzu ji yake idan bai ganta ba a lokacin nan ba tabbas ciwon zuciya zai iya kama shi. Hakan yasa ya dage da neman ku i ta hanyar yin aikin wahala irinsu gini da sauransu don kawai ya tara ku in ya tafi Kano gun Jiddah. Ganin tamkar ba zai iya tara ku in ba a gunsa yasa ya shiga adashe gun wata Hajiya nan bayan gidansa, duk sati yake zuba Naira dubu uku, da yar yake samun ku in da yake kaiwa a sati wani lokacin ma sai ya i ci ya i sha ya ha a ku in da yar ya kai mata, burinsa shi ne ya ha a ku in mota dana sadakin da zai bata shike nan ya wuce gun. Sai da ranar kwasa ta zo tun da safe ya shirya tsab ya auki an kayansa ya isa gidan Hajiya mai adashe, ya zabga sallama yana ta washe baki don ji yake tamkar an biya mai Makka tunda zai ga Jiddah Yau a gabansa. Ko da yake bai san unguwar da take ba, amma daga nan yana amsar ku in gidan mahaifiyarta zai je ya amshi adireshin gidan Hajjo ya wuce yasan ba zata hana shi ba. Sai da ya yi sallama sau uku sannan Hajiyar adashen ta fito fuska ba yabo ba fassala ta dube shi tace, "Yauwa har ka iso ashe? Daman jiranka nake ai ka zo." Fuska kamar gonar auduga haka Deeni ya washe baki yana ta murmushi tsabar farin ciki ma ya kasa ko da amsa mata tambayarta. Ta wage baki ta walawa yarinyarta Hanifa kira, sai kuwa ga wata budurwa ta fito daga cikin gidan. Hajiyar adashe ta dubi Deeni ta fito da ku i Naira dubu talatin ta irga cif tana kallonsa tace, "Kaga ku i nan Naira dubu talatin ko?" Deeni ya aga kanshi yana murmushi tace, "To ba naka bane, nawa ne, domin sune adadin ku in da na kashe wajen zubar mata da cikin shegen daka irka mata a shekarun baya." Ta saka ku in cikin jakarta ta shige gida yarinyar na zabga mai harara domin bata manta tsinannen dukan da akai ta mata ba jeri-jeri sanadin cikin da ya yi mata ba a gidansu. Jagwab! Deeni ya zauna ba shiri zufa ta wanke mai jiki nan take ya ji wani irin zazza i ya rufe shi don haka ya ja jiki ya kama hanyar gidansa idonsa na zubar hawaye. Wai me yasa yanzu komai ke kwance mai ne? Me yasa baki aya lissafinsa ke kwancewa ne ba sadda ya so ba? Har ya isa gidansa hawaye ke kwaranya idonsa tamkar an bu e fanfo. Nan da nan hadari ya taso aka fara ruwa tamkar da bakin warya, ya yi nisa a tunanin abin da ba zai ce ga shi ba ya ji wata irin ara har ya zabura ashe bangon gidansa ne suka zube baki aya sai akin kawai a tsaye tsakar gidan, daga inda yake yana hango hatta toilet in ya afka lokaci guda da katangun. Komawa ya yi ya zauna ya kasa ko da furta kalma guda ko raya kalma guda a ransa. Jinsa yake tamkar ba mutum ba, ji yake yafi kowa matsala a duniyar, ji yake yafi kowa damuwa a duniyar. Yanzu ya zai yi kenan? Waye gare shi da zai taimaka mai ya gyara gidansa? Ta ina zai samu ganin Jiddah yanzu? Sai a lokacin hawaye suka zubo mai tuna Jiddah da ya yi, lokacin da take gidan bai damuwa da duk abin da ke samun gidan domin ita ce ke shiga ta fita ta gyara, hatta wutar gidan ita ce ta jawo ta, take biyan ku in wutar duk lokacin da ake biya bai san ma nawa ake biya ba shi sam. Abu guda ya sani idan aka yanke wutar bata biya ba ya dinga mata masifa kenan yana fa an don me zata bari a yanke wutar. Sai ga shi yanzu tunda ta tafi ba wuta gidan domin bai iya biya, haka ya ha ura ba don bai son hasken ba sai don bai da halin biyan. A bayan rabuwarsa da Jiddah ya fahimci cewar ita ce rufin asirinsa ita ce mai biya mai bu atu bai sani ba yana ta hauka, hatta kayan sawarshi yanzu duk sun tsufa sun lalace babu na kirki dama ita ce idan ta yi sarin kaya Kano take ware mai wasu ta ba shi tun daga takalma yadi shadda hadda ananan kaya yanzu duk sun lalace kuma bai da halin siyen wasu. Tsananin tashin hankali yasa zazza i ya rufe shi nan inda ya ke yana ji mutane na sallama don jajanta mai abin da ya faru na zubewar katangun gidansa amma ya kasa amsawa, har suka gaji suja juya ba tare da sun le o ba sunga halin da yake ciki ba a cikin akin. Wasa-wasa har dare yana kwance cikin azabar ciwo ga ishirwa yana ji ga shi bai iya tashi ya ebo ruwa ya sha. Hakan yasa ya tuna lokacin da Jiddah ke kwance cikin ciwo ga uban ciki amma ya kasa yi mata alfarmar ebo mata ruwa idan ta ro a, haka zatai amai ya dinga mata masifa yana fa a ba tausayi haka zai tada ta ya ce dole sai ta kwashe shi ko mutuwa za tai sai ta kwashe aman bai damu ba. Bai manta akwai ranar da take wani irin ciwon kai tana kwance a falo sai nishi take shi kuma jin haushin nishin yake don haka ya fito ya tsaya a gabanta ya ja tsaki ya ce, "Malama kin dame ni da nishi har kin hanani barci cikin salama ya kike so nayi ne ina jin barci kuma Ni?" Cikin azabar ciwon ta bu e idonta ta yar tace, "Kai ha uri, kaina ne kamar zai tsage biyu don ciwo ga zazza in dake damuna." Tsaki ya ja ya fice daga gidan yana masifar ta tabbatar tayi barci kafin ya dawo a ranar. Yau ga shi kwance cikin jinya yana jin ishirwa ba mai ba shi ruwa babu mai yi mai sannu shi ma. Duk yadda yake mata idan bata lafiya bata nuna mai komai haka idan ciwo ya kama shi zata siyo mai magani idan ma ya cika kwanciya ta ba shi ku i tace ya je asibiti yaga Likita, abin da bai ta a yi mata ba kenan bata ku in magani, to shi da ke auke maganin ma ya saida idan ta siyo ko Mamarta ta sai mata? Hawaye suka cigaba da zubo mai yana jin nadama da takaicin abin da ya faru a baya tsakaninsa da Jiddah. Sai bayan sallar ishsha'i ya samu da yar ya mi e ya sha ruwan kuma sai amai, sosai ya dinga aman dan da nan ya galabaita ya kasa ko da kakarin aman, ya kwanta asa yana jan numfashi. Mijin Binta ne ya ganshi kwance da alamar ba lafiya, ya shiga cikin gidan yana kiran sunan Deenin. Kasancewar Deeni daman irin raggwayen nan ne a gun ciwo yasa yake kwance yana ta kuka kamar aramin yaro. Cikin hanzari ya kama shi ya kai shi aki yana mai sannu da jiki ya ara da yi mai jajen abin da ya faru na zubewar katangun gidansa. Shi dai ba baka sai kunne sai kuwa kukan da yake wanda har ga Allah ba kukan komai bane illa na nadamar abin da ya yi ma Jiddah. Ji yake yana matu ar son ganinta, sosai yake son ora idonsa kanta. Soyayyarta ke yawo a sassan jikinsa ko da yaushe ita ce a cikin ransa, yana yawan tuna abubuwan da ya yi mata na takurawa da gadara duk ta shanye ta ha ura bata ta a nuna mai acin ranta ba, sai ranar da ya zage ta ranar ne kawai ta nuna mai acin ranta har ta kwantar da shi jinyar kwanaki. Lallai ya yadda da mutane da suke cewa Jiddah matar arzi i ce, tabbas yanzu ya amince domin ita ce arzi insa ya fahimta yanzu. Bata da son kai haka bata aukar muguwar shawara akansa komai za a ce mata ya yi bata tankawa haka shima bata ta a tsare shi ba kamar yadda ya sha ganin matan abokansa na turke su idan suka yi nisan kiwo basu koma gidan ba. Yana jin yadda abokansa ke yawan orafi kan matansu idan suka haihu suna tada masu hankali kan sai sun yi masu kaza da kaza abin da bai ta a faruwa ba tsakaninsa da Jiddah. Shi idan ta haihu ma shike cinye duk abin da ta samu kuma bata nuna ko a fuska ta damu. Yaushe zai sake samun mata kamar Jiddah ne? Yaushe zai samu dama irinta baya ne ta sake auren Jiddah? Tabbas auren Jiddah shi ne kawai abin da zai sa shi a cikin hasken rayuwa a wannan ba ar rayuwar da yake yi amma ta yaya hakan zai faru ne? Mijin Binta ya mi e tsaye yana cewa, "Deeni ka rage tunani bai da amfani ka auki ha uri Allah da Ya baka ikon gina gidan nan shi ne zai sake baka wata damar insha Allah." Ya fice yana jin tausan Deenin a ranshi yadda lokaci guda komai ya sauya mai. Cikin arfin hali ya samu ya fice waje yana addu'ar Allah Ya ba shi ikon ha uwa da wanda zai sai ma shi ko da ruwan shayi ne ya sha domin yunwa yake ji sosai kuma bai da ko sisi. Haka ya dinga gararanba amma bai dace da wanda ya ba shi ko da Naira ari ba, har ya yanke tsammani ya nufi hanyar