Sashe 30
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
amma idan ba a biyani ku in kayana da aka bata ba wallahi tallahi sai dai ta mutu cikin akin can." Har ya zaburo da gaske zai kama Ni da komowa nace, "Dakata abin bai kai nan ba da farko amma tunda ya kai yanzu shege ka fasa to." Na gyara tsayuwata na dun ule hannu ina jiransa. Ban san yadda akai ba naga ya ja baya ya ce, "Don Allah ki bu e mata ofa sai mu yi maganar daga baya kar kisa ta tara min mutane a banza." Na waro idanu waje nace, "Kasan Allah ba mutane ba ko aljanu ne za su zo nan gidan Yau sai an kawo min kayana ban san ku in ma kayana nake so wallahi." Tun muna yi ka an har abu ya kai makwabta sun fara jiyo kukan yarinya da tashin muryarmu sama-sama don haka mutane suka zagayo jin abin da ke faruwa. Muna cikin hakan iyayen yarinyar suka zo sai kuma aka ci sa'a ashe yarinyar ba gidansu ta kai kayan ba gidan awarta dake da aure takai kayan domin itama an kusa bikinta nan da sati biyu don haka tana gudun ta kai su gidansu ace ina ta samo su, don haka ta kai ajiyarsu. Akai-akai da Ni kan na bu aki yarinya ta fito nace sam, ban bu ewa sai na kama kayana a cikin hannuna sannan zan bu e mata aki. Ubanta ya le a ta taga ya tambayeta ina kayan suke? Tana kuka tana gaya masu inda ta kai ajiyar kayan. Uwarta ta saka Salati tace "Kin banu kau dan Fure ta je garinsu Tani barka sai gobe zata dawo, e wallahi kin ja wa kanki tsiya Hinde." Ganin anyi juyin duniyar nan na kafe ban bu akin yasa iyayenta da Deeni suka ha a ku en dake aljihunsu suka ban suka ce na bu e ta gobe idan an kawo min kayan sai na basu ku in tunda sun fi na kayana ai ku irga naga dubu hu u ce daga Deeni sai dubi shida daga Innarta dubu takwas daga Babanta na soke a zanina nace "Na rantse da Allah idan ba a kawo min kayana ba sai na ba su mamaki." Sannan na bu e ta, tun kafin ta ida fitowa ubanta ya kai mata duka uwar ma ta kawo nata, naga suna neman sabauta yarinya cikin gidana na janye ta bayan na tabbatar da ta bugu sosai nace, "Ba dai nan gidan ba, su bari har su je can gidansu sai su yi mata koma miye." Suka kwasa suka fice yara na biye da su uuuu duk an tallar ne ba mamaki auyensu ne ma. Ko da kowa ya watse na zabura zan mi e tsaye kawai sai naga Deeni ya kwasa da gudun masifa ya bar gidan har yana yada wayarshi. To masu karatu ko ina Deeni zai je kuma? Waye Mustapha me ke damunsa? Wane irin zama Jiddah ke yi yanzu a gidanta? Shin zata kuwa bada ku in bayan an kawo mata kayan? Dama wasu abubuwan duk za ku ji su a page na gaba. Taku a kullum Haupha [8/4, 5:11 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa