Sashe 94
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya dasa mata takaici yasa ta fita hayyacinta Yau kuma ita ce namiji yasa ta kwanan farin ciki yasa ta manta komai na ba in cikin a namiji ya aikata mata a baya. So kenan ba abin da bai sawa yasa ka a farin ciki wani lokacin ya saka a ba in ciki. Mustapha na kwance sai godiya yake ga Allah wanda ya nufe shi da fita daga angin rayuwar da yake ciki na rashin samun cikar burinsa na samun macen kirki ta warai wadda zata iya yi mai duk abin da yake so zata saka shi farin ciki idan yana cikin damuwa haka idan yana cikin nisha i zata ara mai da shau Kasa daurewa ya yi sai da ya kira number abokinsa Ali angote cikin daren don ya bayyana mai irin halin da yake ci na samun wadda yake mafarki wadda ko da yaushe yake yin zancen ta . Cikin magajin barci angote ya aga kiran don yasan ba lafiya ba kira haka cikin dare. Mustapha cikin muryar farin ciki yake cewa, "Dilla Malam ka kauda barci daga Idonka ka ji wani kyakkyawan labari daga bakina yanzun. Ko kasan cewa Jiddah ta amince da Ni ta ban dukkan soyayyarta har ta amince da maganar aurena?" angote abokin Mustapha ne sosai yasan yadda Mustapha ke fama da rigimimar gidansa haka yasan burin Mustapha na auren wayayyar mace wadda ta ware a soyayya haka shi in yasan yadda Mustapha ke masifar son Jiddah tun shekarun baya. Sosai ya taya abokinsa murna don yasan cewa yanzu abokinsa zai samu kwanciyar hankali tunda ya samu abin da yake bu ata . Jin Mustapha bai da niyyar barci ya kashe wayarsa ya juya ya cigaba da barcinsa duk da yana jin kamar kiran sallar asuba. Wajen arfe takwas na safe Jiddah ta gama shiryawa ta shiryawa su Afnah don haka ta kira Prince don ya kaisu tasha kamar yadda taima Baffa al awarin tafiya da safe. Suna gama karyawa ya shigo sai amshi yake, idan ba gizo idonta ke mata ba sai taga ya ara yi mata kyau har wani haske ya ara kamar ba shi ba. Hajjo ta ara yi mata nasiha tai mata fa a sosai sannan suka fice zuwa tasha. Suna zuwa suka samu mota don haka ta shiga tana kallon yadda baki aya jikinsa ya yi sanyi idanunsa suka ka a su kai jajir damuwa muraran kan fuskarsa. Ta san itama tana jin yadda yake ji amma ya zatai? Ya zama dole ta tafi ne don haka ta kauda kanta kawai don bata son ta sake karya mai zuciya har itama tata zuciyar ta ida karyewa. Motarsu na agawa ya fara zubo da hawaye daga idanunsa ya yi sauri ya bada ku in motarsu ya haye mashin insa ya ba shi wuta sosai har saida kowa ya kalle shi. Jiddah ta sadda kanta asa kawai tana jin yadda bugun zuciyarta ke aruwa tamkar wadda tai gudun gaske. Motarsu bata jima da tashi ba kiran wayarsa ya shigo mata ta auka tana agawa ta ji ya fashe da kuka yana cewa, "Princess don Allah kar ki tafi ki barni don Allah Princess." Kuka yake sosai wanda sai da taji nata hawayen sun zubo mata ita ma. Bata da bakin yi mai magana don haka sautin kukansa kawai ke dukan zuciyarta, yayin da hawayenta suka kasa tsayawa don haka ta kife kanta a cinya ta cigaba da kukan zuci dana fili marar sauti. Sun jima a yanayin kowa ya kasa daina kukan kuma kowa ya kasa magana na tsawon lokaci har sai da yaran suka fara fahimtar abin da ke faruwa sannan tai mai sallama ta kashe wayar ta kife kanta cikin cinya tana saukar da ajiyar zuciya. Har suka shiga Kaduna bata san sun isa ba, saboda tayi nisa a tunanin soyayyarta da Prince. Bata ta a tunanin cewar zata wayi gari da soyayyar wani Mustapha ba an'uwa ga Uncle Salim ba, ita bata ma tuna shi ko ta hasko ko da fuskarsa a baya amma yanzu ga shi cikin ikon Allah sun wayi gari cikin aunar juna ta gasken-gaske, ta yarda da cewar ha uwarsu ita ake kira da HA IN ALLAH wadda ba sanin wani ba shawarar wani sai wayar gari kawai da ita su kai. Komai ya tsaya ma Alawiyya saboda ta lura sosai Jiddah ke fushi da ita, tunda har ta kasa aga mata kira kuma tabar gidan. Kuka take sosai duk da bata lafiya a kwanakin nan amma haka take jurewa don kawai ta samar wa da mijinta natsuwa amma hakan ya faskara sai ma arawa kanta damuwa da jawo matsala da tai tsakaninta da Jiddah. Me yasa Faisal zai masu haka ne? Me yasa ya shiga tsakaninsu don kawai ya raba su? Ya manta yadda suka wahala kan neman juna shi ne zai saka masu da hakan bayan sun ga juna? Ya kamata ta nuna mai cewa bai yi masu daidai ba kuma akwai abin da ake bari don kunya ko da ya zama halas ne. Sai a yanzu ma take hasaso irin rainin da Faisal ya yi mata wanda har shahararsa tasa ya wanke ido ya wanke baki ya ullo da maganar son auren Jiddah. Wai ita ce Faisal ke auke ma kai, yana mata ciccin magani yana nuna mata halin ko'in kula da ita kanta da yaranta akan zai ara aure? To idan ya ara auren ya kenan zai mata kuma? Tabbas sai ta wayi gari ya juya mata baya ita da yaranta baki aya idan ma bai sake ta ba. Lallai Jiddah masoyiyarta ce wadda bata da kamarta a fa in duniya tun da har take mata fa a kan mijinta ya san ciwon kanta. Wayarta ta kalla sunan Jiddah ne da take ta kira amma bata auka ba, kiran wayar Faisal ne ya shigo wayarta kamar ta auka amma kuma sai ta ji ya kamata ta nuna mai ita ma mace ce fa tana da ancin gaske a gidan mijinta ba zata iya aukar kowane irin cin fuska daga mijinta ba. Hakan yasa ta kashe kiran kawai, tai wurgi da wayar ta kwanta tana jin yaushe ne ma tai saken da Faisal ya yi mata irin wannan rainin? Zumbur ta mi e tsaye ta shige toilet tai wanka ta fito ta auki cikin kayan Jiddah ta saka ta nufi kicin ta fara ha a girki don tai ma kanta al awarin sakin ranta ba zata sake sakama kanta damuwa ba kan hidimar Faisal ba, amma tabbas ya sake kawo mata raini sai ta ha a shi da soyayyar tai masu wankin babban bargo ta ji dalili. Nan da nan ta ha a abin da take bu ata ta fito ta zauna ta ci iyakar cinta ta jawo wani littafi ta fara karantawa kira ya shigo mata daga Lagos. Tana agawa aka fara kora mata bayani kamar haka, "Madam dama wata tsohuwa ce ke son magana da ke ta damu mutane ko da yaushe kuka take tana cewa a kira mata ke ko a waya ne tana son yin magana dake, to da dai mun share ta sai mu ka ga bata lafiya a kwanakin nan, kuma tana cikin jerin wa anda Gwamna ya yafe mawa amma ta i tafiya tace dole sai an ha a ku don ta ganki a kwanakin baya a cikin gidan nan, shi ne dai nace bari na kira mata ke ga ta nan." Cike da mamakin ko wace tsohuwa ce tace mai ya bata wayar. Cikin kuka Inyami ta ambaci sunan Alawiyya da Hausarta wadda har zuwa yanzu bata koma ta daidai ba. Ko da Alawiyya ta ji sunan ta tashi zaune sosai, domin ta gane muryar Iyami mai abinci Lagos ce uwar ri on Jiddah da ita a shekarun baya. Iyami cikin kuka tace, "Don Allah ina Jiddah take ne? Ina son ganin Jiddah don Allah ki ha a Ni da ita na nemi gafararta kan abin da nayi mata don Allah ki yi min wannan lamunin Alawiyya ke ma ki yafe min tabbas na cutar da ku sosai." Alawiyya tai ajiyar zuciya tace, "Iyami ki daina kuka natsu muyi magana da ke. Me ye ya kai ki gidan Yari ne?" Iyami na kuka na gaya mata abin da ya kaita gidan yarin har ta are ta gaya mata da ta ga Baban Jiddah ma a gidan. Alawiyya tai murmushi tace, "Bayan shi ma akwai mijinta dake nan duk nice na kai su ajiya don su gyara halayensu." Gaban Iyami ya fa i jin cewar Alawiyya ce ta kai Baban Jiddah gidan yarin to ina ga ita da ta ri e Jiddah ri on cin amana? Nan ta saki baki tai ta garza kuka tana neman tafiyar Alawiyya ta kuma ha a ta da Jiddar. Duk da cewar Iyami ta cuce su ai ta yi masu gatan ri e su, ta kuma hana wasu su cuce su, ita ka ai ta amince ta cuce su bata yadda kowa ya ci zarafin su ba, ta sha yin dambe da atti kan sun ta a su ko suna neman keta masu mutunci. Sai taji tana son sake ganin Iyami a rayuwarta don haka tace cikin muryar tausayi, "Ki yi ha uri ki daina kuka zan aiki a zo min da ke Iyami har Jiddah duk muna jiranki kar da ki ji komai mun yafe maki." Iyami tai ta godiya, da Hausarta, tana arawa duk ta cika wa Alawiyya kunnuwa da arar kukanta. Baban Jiddah na zaune a gefe ya buga tagumi yana kallon yadda Iyami ke neman gafarar su Jiddah sai kunya ta kama shi, wai ace shi ne Baban Jiddah amma bai isa ya ce ga yadda ta koma ba yanzu. Ya san ba don bai isa ya ce bai gane iyarsa ba, to ba shakka da bai gane ta. Hawaye suka zubo mai ya hasko yadda yai rayuwa da mahaifiyarta mace mai ha uri da kauda kai da tausayi amma haka ya banzatar da ita ya dinga tafiyarsa yana mantawa da ita. Haka ta haifi Jiddah cike da takaici da rashin jin da in abin da yake mata, amma shi ko a jikinsa yana sane da yadda mahaifiyarsa ke takura mata amma ba ruwansa har dai ya kaita arshe tace ya bata takardar ta.