← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 133

Sashe 100

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

don haka ta sake gyara kwanciyarta cike da nisha i tace, "Ni kuma ko da yaushe addu'a nake, fata nake so nake Allah Ya ara aukaka min kai, Ya ara maka bu i Ya baka duk abin da kake nema Yasa ka gama lafiya Prince, arshe Ya azurta Ni da samun damar zama mata a gareka." Baki aya sai ya dinga jin wani barcin nisha i nason kwashe shi, Jiddah na matu ar saka shi a farin ciki da nisha i, tasan duk kalaman da yake so tasan duk abin da yake bu ata wanda zai saka shi a farin ciki. Tana ganin kiran Yusuf Matashi tun da suka fara wayar amma bata jin zata iya amsa mai ko tace ma Prince in ana kiranta zata aga kiran,sai ma ta dinga jin haushi. Alawiyya ta shigo cikin shirinta da gani tafiya zatai, ta dubi yadda Jiddah ta saki baki cike da fara'a tana waya tana ta keta dariya sai taji ba zata iya datse mata wayar ba, don da gani tana sakata cikin farin ciki ko da jin yadda take dariyar. Ta gefe guda kuma ji take inama ace ita ce ke da halayen Jiddah gun soyayya? Ina ma ace yadda Jiddah ke zuba soyayya da Prince inta haka ita ma take zubawa da Babansu Anam? Tabbas tana son gwada abubuwa da yawa da Jiddah ke yi ma Prince amma sai taji sam bata iya yadda take yi. Ganin Jiddah bata iya daina wayar ga shi tafiya za su yi sai ta dafa kafa arta tace, "Princess ta Prince za mu wuce mu domin ina da shari'ar da nake yi nan da sati guda." Jiddah tace ma Prince inta "Don Allah ka cigaba da zabga tunanina kafin nayi sallama da Sahibata za su tafi gida yanzu." Yar dariyar da i kashe Ni ya yi ya ce mata, "Ko baki ce ba, ko da yaushe cikin tunaninki nake da kewarki ga begenki dake awainiya da ni ba dare ba rana balle safiya. Ki s allame ta ina jiranki Princess baki da damuwa." Jiddah ta dubi Alawiyya ta kwashe da dariya bayan ta kashe wayar tace, "Ya naganki da shirin tafiya har komai ya daidaita kenan?" Alawiyya ta ata fuska tace, "Ban san iskanci miye na dariya kuma?" Jiddah ta kasa daina dariyarta tace, "Ni fa ba cewa nayi ba ya zo biko ya samu nasara kenan ba, cewa nayi har za ku koma anyi daidaito?" Alawiyya tsab ta fahimci Jiddah so take ta yi mata shegantaka don haka sai ta juya tai ficewarta ba tare da tace mata komai ba. Da sauri Jiddah ta diro daga kan gadon ta bi bayan ta tana bata ha uri. Har sun fice suna ta fara'a tai sauri ta bu e wa Alawiyya ofar motar tace, "Ranki ya da e Allah Ya tsare Ya kiyaye hanya, sauka lafiya mata ga Dr. Uwa ga su Afnah." Duk sun fahimci tsiya take masu, don haka sukai tsit kawai suka wuce, sai da ya tada motar ya le o ya ce mata, "Mu zamu wuce, a gaida mana da Yarima idan ya kira." Da gudu Jiddah ta koma tana dariya, suma suna dariyar suka wuce. Yusuf Matashi shi ne sunan dake kara e kunnuwanta bayan ta aga kiran, sai dai tayi mamakin jin cewar yana ofar gida yana jiranta. Kamar ba zata fita ba, sai kuma ta zari gyalenta ta fice tana jin fa uwar gaba sosai. Tun daga nesa ta hango su Afnah na wasa suna tsalle suna ihu irin abin nayi masu da in nan. auka Baba maigadi ne ke wasa da su, sai da ta fita fili sannan ta hango shi, ya biye masu sai tsere suke a harabar gidan, su ruga bayan waccan motar su koma bayan waccan motar suna ta dariya. Ta jima tsaye tana kallonsu kafin ta ida isa inda suke, suna hango ta kuwa suka rugo inda take suna dariya. Shi kuma ya yi tsaye yana kallonsu cikin farin ciki fal a kan fuskarsa. Yaran ta tura cikin gida ita kuma ta nufi inda take ganawa da ba in ta, saboda bata ta a shigar da ba on ta cikin gidan ba sai dai a harabar gidan, Prince ne kawai yake shiga cikin gidan. A hankali ta isa inda yake zaune yana kallonta, yana sakin murmushi, ji yake tamkar ya ruga ya rungume ta don ta yi bala'in birgeshi, bai tsammaci da gaske ta ta a aure ba, sai da yaran ke fa a mai ita ce Mamansu sannan ya lura da suna kwasar kama da juna. Cikin siririyar murya tai mai sallama ta ja kujera ta zauna, ta sadda kanta asa domin shi ne karon farko da ta fara ha uwa da shi. Kallonta yake yana son fahimtar wane yanayi take amma sam ta i ba shi wannan damar, ta sadda kanta asa ya kasa ganin ko idanunta sai bakinta kawai yake kallo wanda ya sha man baki da gani zai taushi. Cikin natsuwa take gaida shi wanda sai ya ji tamkar a fili muryarta tafi cikin waya da i da za Ganin tai shiru daga gaisuwa ya gyara zamansa yana kallonta ya ce, "Jiddah naga kamar ba ki yi murna da zuwana ba, don Allah kada ki sa naji a raina ban samu kar uwa ba daga gareki ba, bayan na gama bin dangi da abokaina na bayyana masu ke a matsayin abokiyar rayuwata." Ajiyar zuciya tai, shi kam fes da shi gwanin sha'awa, amma sam kalamansa basu birgeta, ita a kalaman da ake fa a indai na soyayya ne to na bakin Prince ne kawai ke birgeta sune kawai ke saka ta nisha i, amma darga ba bakinsa ba duk wanda zai gaya mata kalaman auna ranta aci yake sam bata jin ko da i suna yi mata, yanzu ta ji ta gundura da zama kusa da mutum indai ya fara yi mata maganar soyayya yanzu ta ji ta tsani magana da mutum. Don haka ta tsuke fuska tai shiru bata ce mai komai ba sai shi ka ai ke zuba kamar Kanyar da babu da A nashi angaren ma mamakin kansa yake da kansa wai Yau shi ne a gaban mace yake ta magana ko kallo ga alama bai isheta ba, ya fahimci baki aya ta takura da zamansa a gun don haka ta kasa ko furta mai kalma guda irin wadda yake furta mata. Maimakon ya ji haushi ko ya ji cewar bata kyauta mai ba, sai ya sake ji har a asan zuciyarsa cewa ya yi mata, yanzu ne aurenshi ya zo, domin yanzu ne ya samu irin macen da yake ta lalube shekara da shekaru bai samu ba. Yana son macen da tasan kanta, tasan martabar ta da ajinta mai tsare gida ko da yaushe, sannan wadda bata son abin duniya bai dame ta ba sam, tun da ya ganta yake bibiyarta don kawai ya fahimci halayenta, ya sha mamakin gaske lokacin daya tattara jawabai kanta, bai sake mamaki ba sai Yau da ya zo ya iske kyawawan yaranta suka tabbatar mai da cewa ita in mahaifiyarsu ce, ko a jikinta ba a gane cewar ta ta a aure, lallai ya yi masifar samun dacen matar aure mai matu ar tsada da wahala a wannan arnin da ake ciki. Jiddah kuwa ganin ya tasa ta gaba sai wasu surutai yake wa anda ba abin da suke saka ta sai ciwon kai ta dube shi ta an muskuta tace, "Ranka ya da e naga sa on ka na yi matu ar farin ciki, ina addu'ar Allah Ya saka maka da alheri Ya baka abin da kake nema." Murmushi ya yi, ko shakka babu ya ji da in addu'ar da tai mai, hakan ma wata alama ce ta bayyana cewar ya samu Mar'atussaliha. Yana dubanta kamar kar ta daina magana saboda yadda muryarta ke saka shi nisha i. Da yar ya samu ya ce mata, "Kar da ki samu damuwa Special komai nawa naki ne, don haka ba godiya a tsakaninmu." Jin ya ambace ta da suna Special sai da ta ja tsaki a cikin zuciyarta, sai ta ji sunan ba wani da i haka zalika bai ma bada wata ma'ana ta azo a gani ba. "Special ina so don Allah ki taimake Ni kar da ki barni, idan kika barni tabbas kin ida kashe bishiyar da ta fara bushewa daman samuwarki ce tasa ta fara yabanya." Kanta na a asa ko kallonsa bata iya yi, saboda Prince ne kawai take iya jure kallo ko da za su kwana su yini ba zata ji ta gaji ba, haka zalika ana yawan cewa idan aka cika kallon mutum ana ganin muninsa to ita dai duk lokacin da take kallon Prince ara mata kyau yake sosai ta ji yana bala'in birgeta har bata iya auke ido daga kallonsa, mafi yawan lokuta ba san lokacin da take tambayarsa ba shin yasan yana da kyau kuwa? Tabbas da gaske take yana matu ar yi mata kyau na gasken-gaske. Ganin ya jefa ta a tunani yasa ya mi e tsaye yana kallon fuskarta ya ce, "To Special Ni zan wuce ina fatan zan ji kyakkyawan labari daga zuciyarki ta hanyar bakinki ko rubutunki?" Sai taji wasai da ya tashi zai tafi har ta saki murmushin jin da in tafiyarsa, wanda shi kuma sai ya auka na abin da ya ce ne yasa ta murmushin wanda hakan na nufin zai ji abin kirki kenan. Tana kallonsa ya isa gun motarsa, da hanzari wani ya taso ya bu e mai gidan baya ya shige sai kuma ta ga mutumin ya fito da akwati biyu ya nufi inda take. Kamar ta shige cikin gidan haka taji, don ta tsani kyautar soyayya indai bata Prince inta bace ba. Kamar ya sani sai taga ya wuce ta ya nufi cikin gidan kai tsaye da kayan, don haka sai ta bishi baya kawai. Yana kallonta yana kallon yadda ta ata rai ganin an fito da kayan, sai abin ya sashi murmushi, da gani ta ware a shagwa a yarinyar. ofar akinta ta nuna mai ya aje mata, ya juya, ita ma ta shige akinta ko kallon kayan ba tai ba, wanka tai kai tsaye ta fito ta saka doguwar riga marar nauyi ta janyo wayarta don ta
Chapter 100 · 0% Book details