← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 133

Sashe 4

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 4 *Wannan shafin na sadaukar da shi ga Prince ina, ina ma shi addu'ar Allah Ya ci-gaba da bu e ma shi dukkan wasu ofofin nasara Ya ara ma shi basira da aukaka tare da kare shi daga dukkan ma iya na gida dana waje Ya azurta shi da dukkan cikar burinsa.* Sai da mahaifina ya shafe wata takwas bai dawo ba abin da ya fusata iyayen mahaifiyata kenan, arshe har ta haifi abin da ke cikin bai dawo ba, wanda ta samu namiji aka saka ma shi suna Muhammadu sai bayan ta yi arba'in ne mahaifina ya dawo da iyayen magungunan gargajiya kala-kala. Bayan ya huta ne Kakata ke gaya mai abin da ke faruwa, ya ce "Wallahi ina son matata don haka bari na je na dawo da ita." Ko kallonshi bata sake yi ba, domin tasan iyayenta da ita kanta matar ba wanda zai amince da bu atarsa. Yamma nayi ya yi wanka ya kwashi yaransa suka nufi gidan surukansa, sai dai tun kafin ya shiga mahaifinta yace "Yawwa fatan takardar ce ka kawo min ? Ai ba sai ka shiga ba, ni kaina idan ka bani ya wadatas yaronka kuma idan ka so ka bar mata idan ka so ka auka ka ha a da ar'uwarsa duk ya rage naka." Da gaske yake yana son matarsa bai shirya rabuwa da ita ba, don haka ya yi ta bada ha uri amma kamar yana ara zuga tsohon dole ya tafi ba tare da yaga ko da kalar yaron da aka haifa ma shi ba balle fuskar matarsa. Abu kamar wasa aramar magana ta zama babba, ba irin magiya da mutanen da bai tura ba amma ita da iyayenta suka kafe kan bata komawa sam, daga arshe sai tace ma shi ita fa ban da yawon da yake hatta tabar da yake sha ona mata zuciya take don haka kawai su rabu ta gaji da halayensa ita. Daga arshe dai yana ji yana gani ya rubuta mata takardar sakinta ya bata. A lokacin yarinyarsu nada shekara uku da rabi don haka bai shawara da kowa ba ya auke ta ya kaita Lagos gun wata Inyamura Iyami mai saida abinci yace ta rike ma shi yarinyarsa ya bata amana domin duk sadda ya kalli fuskar yarinyar sai yaga ta mahaifiyarta, har zuwa yanzu bai daina jin son matarsa a ransa ba, duk ya takura kansa ya daina zuwa daji ya daina shan taba amma ta yi mirsisi tace bata dawowa don haka ne ma bai san ganin fuskar yarinyar na tuna mai da mahaifiyarta. Kun san dai yadda yare suke da son banza ko da Iyami taga yadda yake matu ar kula da yarinyar ko da yaushe cikin kashe manyan ku e yake sai tai na'am da yarinyar ta dinga nuna mata soyayyar arya a gabansa, ko da wasa bata barin yarinyar tai kuka, duk abin da take hankalinta na kan yarinyar, abin da ya ara mata kima da yarda ga Baban yarinyar, ya kimtsa ya aje mata manyan ku e yace zai tafi sai bayan shekara zai dawo amma zai dinga yi masu aike na duk abin da suke bu ata. Haka Babana ya tsallake ni ya barni gun wadda bai da ha in komai da ita, asalima ba musulma bace ba. Tunda ta tabbatar da Babana ya bar garin shike nan sai ta auki tsanar duniya ta ora min, sam bata tausayin aranta ta, wahal da ni take tamkar wata yarinyar budurwa, duka da zagi kuwa da suna kanta da sun yi min a jiki. Duk wanda ya sai abinci nice ke kai ma shi duk kuwa inda yake, tun ban iya wanke-wanke ba har dai na iya da duka da zagi, duk da cewar abinci take saidawa amma bata bani wanda zan ci in oshi, sai dai ta ban wanda zan lasa, hakan yasa nake ta tsawo ba iba, duk na fice hayyacina a shekaruna bai kamata ace ina wasu ayyukan ba amma duk na jima da warewa da iya su, hatta wankin kayanta don mugunta nice ke yi mata su, kayana kuwa ta tattara ta oye su kala biyu kawai taban nake sawa sai kaya sun sati biyu jikina take cewa na cire na wanke na saka gudan kayan. Akwai yaran Babana da dama dake gun suna ganin halin da nake ciki amma basu isa su tanka ba, domin muguwar masifaffa ce Iyami sam bata da mutunci ga shi tari ga ta yaudare shi ta nuna ma yarinyar auna a gabansa ta arshe don haka ba abin da za a gaya mai kanta ya amince. Shekaru na ta tafiya har na kai shekara shida a gun Iyami, zuwa yanzu ita kanta wahala idan ta ganni sara mun zatai, domin yanzu hatta girkin da take yawanci duk nice jigonsa tana daga zaune take sakani komai iyakarta ta kame kan kujera tana bani umarni ina bi. Duk da arancin shekaruna hakan bai hanani gane irin wautar da mahaifina su kai ba na kawoni gun wadda ba musulma ba, gani kara zube babu arabi babu boko aiki kawai nake kamar inji, bata ta a ce min nayi sallah ba, to idan tace min ma ban san yadda ake yinta ba ai balle inyi don haka ni da ita babu bambanci sai na suna da shigar kayan jikin mu kawai. Sule yaron Babana ne shi ne kawai ke jin tausayin halin da nake ciki yana matu ar tausaya min sosai kan abubuwan da Iyami ke min, ya sha siyen abinci idan na kai ma shi yace na zauna na cinye ya ban ku in na kai mata, shi ne yake yawan ce min na dinga sallah na dinga yi ma iyayena addu'a duk sanda nayi sallah. Duk lokacin da yake gaya min hakan kallon shi kawai nake domin ban san yadda ake sallar bama sam da ya fahimci hakan naga alamar tashin hankali muraran kan fuskarsa, an fi sati ya zo shagonmu ya ba Iyami ku i masu dama yace "Oga ya aiko da su yace na kawo maki ki saka yarinyar can makarantar boko da arabi to amma ni a shawara ta me zai hana ki dam e ku en ki samu wasu makarantun na ya ku bayi ki cilla ta duk wata ki dinga amshe ku in da zai turo kina ara jari tunda ku in makarantar ku i ne ya bada ki saka ta?" Murmushin jin da i tai tace, "Shegiya Sule ashe kanki na kawo wuta." A nan take ta ba shi aikin nemo min makarantun talakawa. Idan ba haka ya yi mata ba, ba zata ta a amincewa yarinyar tai karatu ba, shi kuma yasan hakan shi ne kawai abin da zai ma Ogansa ya rama rabin abin da ya yi ma shi a rayuwa, domin shi ne ya kawo shi Lagos ya sai mai mashin yake haya kuma bai ta a amsar ko da Naira dubu ba daga hannunsa kyauta ya sai ma shi mashin in, don haka ya ga dacewar yin hakan ga iyar Ogan. Cikin kwana biyu na fara zuwa makaranta sai aikin wahala ya rage min, sai dai tana yawan hana ni abinci tace, "Can makarantar ba a baka ba ne don ubanka?". Idan da sabo na saba da yunwa da wahalar rayuwa don haka sam ban damuwa da abin da Iyami ke mun tunda na riga na gane ba ita bace ta haifeni ba sai abin ya yi min da i domin yanzu na fahimci illar rashin addini. Alawiyya Malam ita ce kawai awata, wadda muka sha u muke tattauna magana kowace iri a tsakaninmu, babu nisa tsakanin gidansu Alawiyya da gidanmu don haka duk sanda zan je makaranta ina fara biya mata sai mu wuce, Kakar Alawiyya Inna Kande tana da matu ar kirki da tausayi ko da yaushe ita ce ke wanke kayan Alawiyya ita ce ke girka abincin da Alawiyya ke ci ita Alawiyya goro kawai take saidawa, daga shi babu aikin da take ma Inna Kande hakan yasa Alawiyya ta fini kumari ta fini walwala da natsuwa ko da yaushe ni cikin tunani nake ko ya sunan iyayena oho, ko ya kalarsu take oho, naji dai su Sale na kiran mahaifina da Oga Dawa ko hakan ne sunanshi oho, ko a makaranta ni ka ai ake kira da Jiddah Iyami kowa da sunan Babansa sai nice kawai ban da sunan mahaifi a jikin sunana. Tunda mahaifina ya tafi bai sake waiwayar halin da arsa take ciki ba sai zafin aike da tambayar ya Jiddah take aikin kenan bai ta a cewa bari ya zo yaga ya halin da nake ciki ba ko yace ya kamata yaga ya na koma ba. Rayuwarsa kawai yake bai damu da duk halin da zan kasance ba, shi dai tunda ya ba da ni kuma yana turo ma Iyami da ku e shike nan a ganinsa ya gama mai wahalar. Muna zaune ni da Alawiyya take gayamin Inna Kande tace zata je garinsu don haka zata zo gun Iyami ta nemi alfarmar ta ri e mata Alawiyya har ta dawo daga ganin gida. Ba aramin da i naji ba na maganar domin har ga Allah ina matu ar jin da in zama da Alawiyya domin tana tayani ayyuka da dama, kuma tana yawan kawo min abinci a oye, haka duk inda zan kai abinci tare muke zuwa da tallar goronta bisa kanta. Haka kuwa akai Inna Kande ta zo gun Iyami ta gaya mata zata je gida can Arewa gun danginta amma ba zata je da Alawiyya ba saboda wani babban dalili mai arfi amma don Allah ga ajiyar ta nan zata bar mata kafin ta dawo. Da farko Iyami kamar ba zata amsa ba, sai da Inna Kande ta fito da ku e ta mi a mata tace, "Ga wa annan ko da zata bu aci wani abun kafin in dawo Iyami." Nan take Iyami ta washe baki ta amshe ku in har tana tambayar "Halan zaka jima ne can?" Kowa yasan mugun son ku in Iyami don haka duk wanda zai mata tarko da
Chapter 4 · 0% Book details