← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 133

Sashe 95

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iyami ta dubi Baban Jiddah tana kukan farin ciki tace, "Na gode wa Allah sun yafe min yanzu haka za su aiko a tai da Ni, na ji da i da ban mutu ba na nemi tafiyarsu. Ina maka nuni da kaima ka je ka nemi yafiyar Jiddah idan kana son samun kwanciyar hankali idan ba haka ba kuwa ba zaka sake farin ciki ba a rayuwarka." Ta jima tana mai nasiha irin tasu wadda suka ga hau a rayuwa. Ranar da Jiddah ta dawo Kaduna ta iske Alawiyya bata tafi ba sai kawai ta sauya aki ta bar mata wancan sai dai idan wani abu ya kawo ta auka dole sai ta zo ta auka bata magana. Jiddah na shigo wa akin ta ga Alawiyya zaune tana waya, ko kallo bata ishe ta ba, kawai kayan da take bu ata ta auka ta koma akin data sauya, sai dai Yau wayar da Alawiyya tai ta sata kuka ta tuna mata wata rayuwa wata mata wani bigire wani yanayi na baya daya wuce. Har asan ranta ta agara gobe tayi taga zuwan matar don har zuwa yanzu tana cin moriyar abubuwa da dama da matar ta koya mata na fannin girki ba wanda bata iya ba. Washegari sai ga Iyami an kawo tayi ba i ta rame duk tsufa ya yi mata sallama. Da gudu Jiddah ta ruga ta rungume ta tana kukan farin cikin ganinta, duk da cewar Iyami ta cutar da ita ai tafi mahaifinta gunta tun da shi kasa ri e ta ya yi don haka ya kaita uwa duniya don a ri e ta, ita kuma ba dangin Iya bana Baba asalima ba addini aya ba haka ba yare aya ba amma ta amshe ta tun tana miririyarta ai kuwa bai kamata ta yada Iyami ba. Sun jima suna kukan ha uwa Iyami na neman tafiyarsu suka yafe mata, aka baya aki guda a cikin gidan ta zauna. Wani abin farin ciki ta samu Jiddah ta gaya mata cewar tana so ta musuluntar da ita, ba aramin da i abin ya yi masu ba, shi kanshi Baffa ya yi murna sosai da jin zata musulunta. A ranar aka musuluntar da ita ta amsa sunan Hawwa'u (Jiddah) Allah ke nan Yau ga Iyami ta musulunta bayan a baya ita taso saka Jiddah nata Addinin. Ko da yaushe Iyami na son yi wa Jiddah maganar Babanta amma tana jin tsoro saboda Jiddah ta bata labarin yadda rayuwarta ta kaya bayan sun rabu duka. Amma Yau dai ta kasa ha uri tai mata maganar wanda Jiddah tai mirsisi tace ita bata da wani uba da yafi Baffa don haka ta daina mata maganar wani. arshe dai sai da Baffa ya shiga maganar sannan Jiddah ta amince da cewar ta yafe mai kuma a sake shi amma kar wanda ya gaya mai inda take. Iyami tace, "Ai yasan inda kike tun ina can na gaya mai, kuma a ranar da nayi waya da Alawiyya yana tare da Ni ko ranar. Tabbas ya yi nadama kamar yadda nayi haka ma uban yaranki ya yi nadama yadda ya kamata ki gode wa Allah Jiddah domin duk wanda ya cuce ki tun a duniya yake fara ganin sakayyarki. Duk lokacin da Baffa ya dawo yaran suna murna suke rugawa akinsa. Sosai yake murna da zuwansu akinsa, yana son yaran jinsu yake tamkar da gaske jikokinsa ne daya haifi mahaifiyarsu ko mahaifinsu. Wani angaren kuma ladabi da biyayyar Jiddah na ara sawa yana jin ta a ranshi sosai, yarinyar ke burge shi don haka yake jin tausayinta yake da burin yaga ya tallafi rayuwarta ta tsaya da afafunta ko bayan ransa ba zata sake kukan rashin gata ba. Kamar wasa Jiddah ta fice sabgar Alawiyya kuma ta i komawa Kano baki aya ta fice daga sabgar Faisal itama abin kamar wasa kuma Baffa ya kawo ido ya saka mata bai ce mata komai ba, haka ita ma can Mama ta saka mata ido saboda Maman Faisal in ta kira ta tace kada wanda ya shiga sabgar Alawiyya da Faisal in a barsu su ara ta can su suka sani. Ita kam tayi haka ne don ta watarwa da Alawiyya ancin ta gun Faisal ya gane kurensa yadda ko ance gana ya yi mata irin haka ba zai sake ba. Shi kuma tun yana ganin zata dawo ne ko zata daina fushin da take tun da bai mata komai ba, kawai rainin hankali ne ta zo da shi da zata wani tafi Kaduna ta zauna ko kiranta ya yi bata aukar kiran. Gefe guda kuma Jiddah tayi blocking na number shi bai ganinta a online haka ko ya kira bata shiga da ya matsa mata ma sai ta samu lokaci ta turo mai kashedi na musamman har ta kira shi da mai raba zumunci mai yanke abota. Tun daga lokacin ya tabbatar da cewa Jiddah bata ta a amincewa da aurensa don haka ya koma kan Alawiyyar yanzu. Sai dai tai mirsisi ta yale shi kuma abin takaici ba wanda ya saka baki kan ta dawo Kano Jiddah ta dubi Alawiyya ta ara ha e fuska tace, "Malama ya za ki zo ki takura min bayan kin san cewa na bar maki wancan akin don gudun takurawarki?" Alawiyya ta langa ar da kanta gefe guda alamar neman afuwa tace, "Don Allah ar'uwata abar alfahari na mai tausayi na ko da yaushe ki yafe min ki manta ba in halin da na nuna maki, ki yi min aikin gafara ko na samu sukuni a zuciyata. Tabbas na manta cewa Ni dake tamkar uwa aya Uba aya muke auren miji guda ya haramta garemu. Sai dai idan ba ran guda a doron duniya ne ayar zata iya auren mijin don cigaba da ri e yaranmu da shi kanshi mijin." Jiddah ta kalleta fuska ba walwala tace, "Ban ta a tunanin za ki yi min abin da kikai min ba Alawiyya. Ko kin san da cewar duk lokacin da nake cikin uncin rayuwa addu'a nake Allah Yasa ke baki cikin uncin. Haka zalika duk lokacin dana tunaki fatana gareki ki zama cikin aminci amma sai ga shi kin watsa min asa a ido kece mai neman kai Ni ga tashin hankali da damuwa. Ban ta a zaton ke ce za ki iya raba zumuncinmu da amincinmu ba sai ga shi na gani na shaida da karin kaina. Ke a tunaninki idan auren miji guda ya gitta a tsakaninmu za mu dawwama ne yadda muke ? Ke a naki hangen auren mijinki wata mafita ce mai orewa a garemu? Uhmm! Kin wauta kamar yadda ya so kansa Alawiyya ban za ci cewar baki son mijinki ba sai yanzu, tabbas ya kamata ki natsu ki gane me kike ki fahimci waye mijinki don samun kwanciyar hankalinsa da naki baki aya. Kin ban kunya kin sa naji ba da i da har kika iya barin arakar da mijinki zai iya saka wata a cikinta. Akan me za ki yi hakan Alawiyya? Ke fa babba ce a fannin aikinki shin ba za ki zama babba ba a cikin zuciyar mijinki ba? Don Allah ki gyara halayenki domin ban gamsu da kulawar da kike ba Faisal ba sam Alawiyya. Idan barci kike ya kamata ki farka haka nan kafin ya haddasa maki wata matsala barcin." Sosai Alawiyya ke fahimtar maganar Jiddah tabbas daman can tasan Jiddah mace ce mai son kula da kulawa haka zalika bata sake da duk abin da take so, ba aramin asara bace ga namiji ba ya rasa mace kamar Jiddah ba. Tabbas ta taya Prince murna domin ta lura da cewar shi ne zakaran gwajin dafin da ya ci gasar sace zuciyar Jiddah a cikin jerin mazan dake karakaina kan neman amincewar ta kan aunarsu. Cikin mintuna alilan suka ha a kansu,sai ga su suna ta dariya kamar ba su ba. Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Yau fa muna da babbar ba uwa a gidan nan nasa an auko ta nasan suna gab da isowa nan ba da jimawa ba." Jiddah tai murmushi tace, "Kina nufin Iyami wai?" Da kallon mamaki Alawiyya ta kalli Jiddah don ita dai tasan bata gayama kowa zuwan Iyami ba, haka zalika bata gayama Jiddah da bakin ta ba. Jiddah tai murmushi tace, "Kina manta aikinki kina manta aikina ban san me yasa ba." Alawiyya tai dariya tace, "Ba fa za ki kwantar da Ni ba, nasan dole akwai yadda akai kika san da zuwan Iyami, kawai ki gayamin." Jiddah tai dariya tace, "Madam kin manta da cewa akina kike zaune? To a cikin akin akwai wayar da na aje wadda duk wanda ya yi magana tana na ewa tana turawa a wayar hannuna, don haka duk maganar da ki kai akwaita a cikin wayata ba wadda ban sani ba." Alawiyya tai murmushi tace, "Na jinjina wa babbar Lauya mai inbim basira da kaifin walwa Barista Jiddah." Jiddah ta kwashe da dariya tace, "Har kin tuna min da shari'ar da zan yi gobe ta wata yarinya da anin mahaifinta ya lalata mata rayuwa saboda abin duniya. Kuma abin takaici shi ne mahaifin yarinyar shi ne ya ri a shi har girmansa ya saida komai nashi don ya inganta mai rayuwa amma shi ne ya yi mai sakayyar lalata mai yarinya arama yar shekara takwas wai bokansa ya ce mai zai arzi i idan ya biya bu atarsa da ita, kuma zai samu kujerar da yake nema ta siyasa." Nan da nan Alawiyya ta ha e rai tace, "Dole ne ma na raka ki gobe kotun domin naga yadda zata kaya, bai kamata ki bari a ja lokaci ba gun shari'ar tun da ga alama akwai shaggun a gun mugun." Jiddah tai murmushi tace, "Ba shi ne damuwata ba sai wani tsinannen miji da ya saki matarsa saki uku bayan ya gama amshe mata komai na dukiyarta kuma ya raba ta da danginta sannan ya kwashe mata yara mata wai zai kai su Makkah aikatau. Shi ne kawai na je kotu rannan ake gayamin wata mata na nemana kamar ba zan bi takan ta ba sai kuma nace a bata lambata ta ace nace ta kira Ni. Shi ne fa ta kira Ni take gayamin zai tura mata yara Makkah aikatau har ya amshi
Chapter 95 · 0% Book details