Sashe 22
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *INNALILLAHI WA INNA'ILAIHIRRAJI'UN!!!* Allah Ya yiwa magajin mahaifiyata (Yayan Mamata) rasuwa a yau Alhamis, ina neman addu'arku Allah Ya ji ansa Ya gafarta masa Yasa ya huta. Mahaifiyata ma bata lafiya ina neman addu'arku Allah Ya bata lafiya Yasa kaffarane tare da sauran marassa lafiya na gida dana asibiti. Haupha Page 18 Haka nake tsugunne har asuba sannan na dawo daidai, na tashi da yar na auke Haidar dake kwance asa, na sashi ya yi fitsari na kwantar da shi, jin ana kiran sallah yasa nayi alwala na kabbara sallah, na gama na fara lazumi naji barci mai nauyi ya kamani, don haka na rungume Haidar barci ya auke Ni. Can cikin barci naji kukan Haidar, na bu e idona da yar, naga gari ya waye tangaram, don haka na tashi don nasan kukan yunwa yake, sauran abincin jiya na duba bai yi komai ba, don haka na hura wuta na umama shi, na zuba ma Haidar, na shiga wanka na fito na ci nawa, shi ma nayi mai wanka. Sai naji a raina ya kamata na je gidansu Abban Haidar na gano shi, ba wai don ina jin ban kyauta ba na dukan da nai mai ba, sai dan da da i yana mijina ya kwana wani waje na je naga yadda ya kwana. Na shirya tsab zan fice kenan wata abokiyar wasana ta iso ofar gidan, don haka na fasa rufewa muka shiga cikin gidan. Bayan ta zauna ta fara tsokana ta, "Sai ina kuma iyayen yawo? Ke dai kullum kamar kin ci afar Kare ba a iske ki gidanki, ko dai mijin ke korarki?" Ni dai murmushi kawai nake, don ban iya wasan da ake kira na tsakanin an mace da an namiji ba. Can ta nisa tace min, "Jiddah ina tason na ganki mu yi magana amma Allah bai sa mun ha u ba, kuma nayi al awarin idan ba ke na gani ra'ayil ainu ba, cikin gidan nan ni da gidanki har abada. Na dube ta da fuskar mamaki, harma da tambaya. Tai ajiyar zuciya tace, "Jiddah kwanakin baya can na zo zan wuce ta unguwar nan, sai na hango gidanki sai nace a raina bari na shigo Mu gaisa, tun da ke baki iya zuwa gidan mutane, gidan Inna (Mamana)kawai kike zuwa ko kin je wajajen mu. Ina shigowa gidan nan da sallamata na iske maigidan, ya le o daga aki yace, "Ki shigo man kin tsaya tsakar gida?" Ni kuma ina dariya nace, "Ina auyen matarka ta fito ta kawo gaisuwa na zo." Yana ar dariya yace, "Shigo ki zauna man sai ta baki amsa ai tana da bakinta." Nace nima ina dariyar "Kai haba yaushe tai bakin ban da labari? Ai ura ce matarka tsoron mutane take balle ta iya maida masu magana." Ina maganar na shiga akin na zauna. Ya dube ni yace, "Yanzu ta an fita nan makwabta yanzu kin ganta ta dawo ina ga ko magi taje siye." Da yace hakan sai na zauna ina jiranki, tunda yace kina kusa. Jiddah ina zaune kan kujerar can mai zaman mutum biyu ban san ya akai ba kawai naga Deeni zaune gab da Ni, yana ta murmushi yace, "Wallahi ina ta son dama na je gunki mu yi wata magana ban samu damar zuwa ba...yana magana yana neman ora hannunsa kan irjina. Na yi Wuf na mi e tsaye ina zare idanuwa gabana na fa uwa. Sai yace mun "Ke wasa nake maki bata ma kusa tana gidanmu kawai ki saki jikinki... Ban bari ya ida ba na nufi ofa amma dai ya yi sauri ya isa gun ofar ya rufe ta. Mu kaita yawo cikin falon nan dole sai ya ta a min irji Ni kuma na i, muna ta yawon nan Allah Ya gwadamin rediyo na kuwa auka ciccin arfina na maka mai ita, ya du e ta fa i kafin ya ankara na fice da gudun tsiya ina zaginsa ta Uwa ta Uba. Ke Jiddah ranar naga ikon Allah! Kamar bai san Ni ar'uwarki bace ba? Kuma nasan dai ai yasan sai na gaya maki, tunda ke in jinina ce." Ajiyar zuciya nayi, bakina ya yi min nauyi, tabbas Abban Haidar do yake ta kowane angare sai ya zubar min da mutunci, wane irin abu ne wannan ka nemi ar'uwar matar da fasi anci? Cike da jin kunyar abun na dube ta nace, "Don Allah ki yi ha uri, ban san kuma ki gayama kowa, don Allah maganar ta tsaya iyakar Ni da ke, don Allah." Tai min kallon tausayi tace, "Jiddah daman kin san halinsa haka ye? Daman kin san an iska ne Deeni? Gaskiyar magana kin ban mamaki ko ni da ban aure ba wallahi babu an iskan mijin da zai dinga kawo min mata cikin gida kuma ina sane na yale shi. Idan gani kike wani abin kirki ne to wallahi ba komai bane illa sakarci da mai da kai baya, sannan idan ma don yace kina da kirki ko babu ruwanki ko ya kira ki da macen kirki kin makaro, wallahi yanzu wasu mazan ba ai masu haka, sai kin tashi tsaye kan shi kina nuna mai kin san ciwon kanki, sannan za ki iya aukar kowane mataki kan shi idan bai bar halayensa ba. Yo Allah na tuba Jiddah wannan zamanin wace sakaryar mace ce zata amince da wannan iskancin na mijinki? Shike nan ke baki da wani anci balle martaba ko kimar da zasu sa Deeni dinga kiyaye acin ranki?" Tun da ta fara magana hawaye suke zubowa daga idona, ban san me zan ce mata, har ma da sauran mutanen da ke min kallon Sakarya ba, shin ya zan da halin Deeni ni? Duka nawa nake? Me nasani ma kan rayuwar auren na jin da i? Ban da yadda zan Deeni, shi in halinsa ko da yaushe ara gaba yake madadin baya, da farko na auka idan na haihu yana ganin abin da na haifa zai natsu ya daina abin da yake, ko dan kar watarana ai ma shi gori ko yaron yaga abin da bai kamata ba daga gare shi, ko jin mummunan labari akan rayuwarsa... "Au wai kuka na saki daga gaya maki gaskiya? Anya kuwa Jiddah kin san ciwon kanki yadda ya kamata kuwa? Kai ban zaton kin san wacece mace kawai sunan macen gareki baki da halayenta kam gaskiya. Ta mi e tsaye"To ni kinga tafiya ta, ruwanki ne ki gyara haka ruwanki ne ki bari yana maki cin kashi kina kuka, shi kuma abin murna ya same shi tunda ya ga hawayenki." Har ta fice daga gidan ban tanka mata ba, don babu abin da zan iya ce mata Ni kam. Bayan ta tafi na mi e na auko rediyon tabbas batai arya ba, don ga rediyon nan ta fashe, haka zalika idan zan fa i gaskiya ya jima bai kunna ta sai da naga ya kwance ta yana gyara,ashe abin da ya faru kenan? To Allah Ya shirya shi Yasa ya gane gaskiya-gaskiya ce. Ganin rana ta kawo kai nasan ba lallai bane na je a ban abinci ko a ba Yarona ba yadda mutanen gidan ke fusace dani kan abin da Ni a ganina ban laifi ba, yasa na tashi na nemi abin da zan ci Ni da Yarona, duk da wata zuciyar na raya min na dafa abincin da yawa na kai mai gidansu, amma ina gudun ya auka ina ma da ku i ko abincin da yawa ya i ban, ga shi abincin ba shi ne da Ni ba, kawai an dabaru ne nake ina dafa mana abin da ya sawwa a muna ci. Hakan yasa sai yamma na fice na nufi gidansu, jama'ar unguwa nata min ya mai jiki, duk da nasan gulma ce tasa suke tambayata haka na share nake amsawa, marassa kunyar ciki har tambaya ta suke ko can zan je nema gunsa? Wasu kuwa tambaya ta suke amma yana asibiti ko? Duk ban da amsar basu irin su, sai dai na wuce kawai ban tanka masu. Ina zuwa na iske jama'ar gidan kowa nata hidimarsa, ban damu da yadda sukai tsit da maganar da suke ba,wadda tun a zaure na gama fahimtar shawara suke ba shi kan zamana da shi, kar ya kuskura ya sake ha a jiki da Ni wai zan iya sabauta shi fiye da hakan, ko ma na kashe shi, duk iskancin da zan ma shi ya je gun uwata tunda nafi jin maganarta ya gaya mata, ta auki mataki, amma kar da ya kuskura na sake bugunshi irin haka a banza. Tun a zauren na ta e bakina don wannan su ta shafa, tsorona guda ya je ya ja min sharri gun Mama, ban san abin da ranta zai aci sam a kaina. A hankali na dinga gaishe su, suna amsawa tamkar basu so. Na samu waje na zauna Ni da Yarona, muka bi sahun an jinya tun da na lura jinyar ake ka'in da ka'in ba kama hannun yaro, har da su lemu da ayaba a gabansa. Yau ma bai tanka min ba, haka bai tankawa Haidar ba, duk da naji ba da i amma na cije don ba yadda zan yi. Ganin ina ta zaman banza, na tashi na tattara kayan wanke-wanke nayi na gama na yi shara, ina gamawa ana kiran sallar magrib, na yi sallah na zauna nan ina ta lazumi har ishsha'i nayi ta, lokacin, Haidar ya gaji da kukan yunwa ya yi barci kusa dani. Yau ma kamar wadda aka ri e sai da kowa ya yi barci sannan na goya Haidar na nufi gida. Yana tsaye da fitilarsa mai haskeb gaske mutumin jiya, Yau ma kamar jiya ban ga kansa ba, ya yi gaba ina bayansa yana haska fitilar hannunsa. Haka muka tafi har ofar gidana na bu e yana tsaye na shige na maido ofar na rufe, na je na bu akin na shige. Yau ma kamar jiya ina shiga akin tsoro ya kama Ni sosai, da yar na kwance Haidar dake bayana na udundune waje guda. Sai asuba na samu natsuwa nayi