Sashe 123
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fashe da dariya. Tai an ihu ta fa a jikinsa tana cewa ba zata yadda ba ita sai ta rama ko saka mai kuka. Sai kuma ya fara bubbuga mata baya yana cewa cikin siririyar murya, "Afuwan Princess ban san lokacin da marar jin hannun nan ba ya watsa maki ruwa ba amma ki hutunta bakinsa daya kasa gaya maki abin da zai faru." Ya mi a mata bakinsa nufinsa tai ma shi kiss. Manna mai kiss in tai da nufin tai mai walele amma ta makara sai ji tai yai caraf da halshenta yana tsotsa tamkar ya samu sweet. Sun jima a yanayin har ya fara sauka layi tai azamar janye jikinta, tana cewa time na urewa fa Prince yanzu ka fara jin sallamar mutane kasan Yau an Jalingo za su koma fa." Shi dai ko magana bai iyawa, don haka tai mai wanka ta tsaya jiran yai mata taga alamar wutar jikinsa ta auke baki aya sai ta nufi yin wankan da kanta, sai kuma ya amsa ya cigaba da yi mata. Suna fitowa tai mai shafa, shima ya shafa mata mai da powder ta zizara kwalli zata ora jan baki ta tuna da wani abu don haka ta aje shi zuwa anjima. Kallonshi tai ta kalli kayan daya cire jiya ta fara sinne dariya irin alamar zai maimaita kayan daya cire yana matsayin ango guda. Fahimtar abin da take nufi yasa ya nuna mata wata leda dake can gefen gadon. Tana aukowa taga wata rantsattsiyar shadda mai kyan gaske wadda tana da irinta cikin kayan daya inka mata na cin bikin, hakan yasa ta fahimci iri aya za su saka kenan Yau ma kamar kwanakin baya kala guda suke sakawa. Da kanta ta saka mai kayan ta auki turare ta fesa mai tana cewa, "Idan aka arar min da turare ba wani da in bakin da za ai min sai an biyani abina har da riba." Girgiza kansa ya yi ya ce, "Ni fa taimaka maki nake ina saka wannan aramin turaren saboda turarena yafi naki nauyi da hidimar ma baki aya." ura baki tai ta fara dire-diren ita ba zata yadda ba sai dai a fitar da turare guda kowa ya dinga amfani da shi. Dariya ya dinga yi yana cewa bai yadda ba shi ba zai dinga shafa turaren mata ba, ta kuwa ara aimin abin da take tana cewa ita fa ba ruwanta amshi guda take so shi da ita su dinga yi kawai. A haka dai ya taimaka mata ta saka tata shaddar, kawai aukar ta ya yi ya kama juyi da ita wai tayi kyau fiye da azun. Hotuna suka cigaba da yi sannan suka koma yin videos abin gwanin birgewa. Sun ata lokaci gun hotunan da videon sannan ya janyo ta jikinshi suka nufi falo suna ta murmushin nisha i. Tabbas sun cika amare masu son junansu. Kan kujera suka zube ya dubeta da dukkan kulawa ya ce, "Princess me kike son ci na fita na nemo maki naga rana tayi amarya bata karya ba, duk wazon da tai jiya gun bada darasi." Sunne kanta tai, tana dariya asa - asa sai kuma tace, "Har ka tuna min da babbar kyautar da akai min kuwa a wajen aukar darasin." ewa tsaye yake son yi don fita nema mata abin da zatai breakfast da shi, sai ta kama hannunsa ta nufi inda aka tsara don cin abinci ta zaunar da shi yana bin ta da kallo don bai fahimci komai ba. Sai da ta bu e naman ta zuba a filet ta zuba mai kunun a kofi ta zuba fanken ta tura gabanshi ta zagaya ta zauna kusa da shi tace, "Bisimillah Prince komai ya kammala kai ka ai ake jira daman." Kasa cewa komai yai sai arin tunanin lokacin datai girkin kawai yake, bai ankara ba ya ji saukar kofi a bakinsa ya bu e ta zuba mai kunun. Lumshe idonsa ya yi jin wani gar i da da i na musamman daya sauka akan halshensa, a hankali ta cigaba da ba shi a baki yana sha, ganin kamar bata sauri ga shi kunun ya yi mai da i sai ya amsa ya cigaba da sha da kansa yana ha awa da fanken. Sai da ya shanye wanda ta saka mai duka sannan ya aje kofin ya fara arin zuba mata naman a baki don itama ta gama shan nata kunun. Yana cin naman sau aya ya kalle ta da alamar tambaya sai kuma ya ce, "Princess yaushe kika fita har ki kayo cefane ban sani ba?" Dariya tai ta cire kallabinta ta saka a gefensa wai ita ala dole santi yake yi. Sai da ya sake tambayar sannan ta gaya mai sauran na jiya ne ta gyara saboda ba kayan da take bu ata na girki a gidan. Ya kalli jug in kunun ya ce, "Shi kuma wancan fa ina kika samo shi ban ta a shan irinsa ba ke ban ma san shi ba Ni sai Yau, don Allah dame ake yin shi?" Ta fashe da dariya tace, "Da zallar so da aunar Prince ina ake yinshi , ina fatan ya yi maka da Kiss ya manta mata a fuska ya ce, "Bayan da i ma har gar i da birgeni ya yi don haka na gode sosai da wannan breakfast mai inganci dana samu bayan kyakkyawan darasin dana auka." Shiru tai ta yale shi, domin bata san lokacin da Prince ya koma haka ba, shi da take hangen magana bata dame shi ba, a hangenta ma sai ta koya mai wasu abubuwan da dama ashe kar yake. Sai da ya ji cikinsa na neman fashewa sannan ya ha ura ba don ya gaji da ci ba a bakinsa ba. Falo suka dawo yana kwance cikin doguwar kujera ita kuma tana kwance jikinsa suna kallon hotunan da sukai azun tana cewa yafi ta kyau yana cewa ta fishi kyau. Suna cikin haka suka ji ana buga gidan, tashi tai ya mi e tsaye ta nuna mai kumatunta alamar yai mata kiss kafin ya fita bu ofar, ya kuwa manna mata ita ma tai ma shi ya fice yana kallonta tana aga mai hannu alamar bye-bye kamar wanda zai fice daga gidan baki aya ba ofa kawai zai bu e ba ya dawo. Yana ficewa ta ruga aki ta sake gyara fuskarta ta shafa jan bakin ta gyara aurin kallabinta ta zauna tana jiran taji su waye suka zo. Tana jin yana magana da yara sai ta fito, kayan alaci ne aka aiko daga gidan Yayarsa ta amshi kayan tana tambayar yaran ya Auntyn take, ta juye komai ta zuba masu cin cin da dubulan suka zauna suna ci ita kuma ta ja Prince suka shiga kicin in don zubama Auntyn kayan bikin nata yaran su tafi da su. Sai ya ding a ganin abin kamar a mafarkin daya saba yi na rayuwar da yake so suyi da Princess insa idan sun aure, nisha i suke su duka kowa cike yake da annashuwa har ta gama zuba komai yana cewa sun yawa tana cewa Auntynsa za a kai mawa ko tata? Dole ya ja bakinsa yai shiru don abin yafi arfinsa. Suna fitowa yaran sun gama ta basu kayan tace su gaida mata da Auntyn sosai. Suna tafiya suka koma inda suke da ta jawo wayarta ta kira lambar Alawiyya kamar jira take daman ta kama kiran tana cewa, "Kaga amarya a gidan Mustapha bada kanki a sare ki je gida kice ya fa i, tun azun nake aukar waya da zummar kiranki sai Abbansu Anam ya hanani ya ce yasan baku tashi ba, haka kawai zan matsa ma sabbin amare da kira." Dariya ta saka tace, "Ya kyauta min kuwa, domin yanzu haka juyin farko ne mukai abinmu." Alawiyya tace,"Ai fa abu ya zo ga ma'iya daman breakfast in ku ne nace ya za ai kuna iya bu e gidan yanzu a kawo maku koko sai anjima?" Tai murmushi tace, "Aunty ta jima da kawo mana breakfast Madam ke dai kice kin kira ki ji gulma kawai to Prince da Princess na lafiya." Wayarsa ce tai ara don haka ya auka bai ma duba suna ba, sai ji ya yi ance, "Sai ka zo kaba yara ku in makaranta da ku in cefane?" Murmushi ya yi don Maryam ce hatta Jiddah dake jikinshi tana waya tana jin yadda take magana cike da gatsali da fusata. "Yanzu za a kawo, bari na kira waya, amma har cefanen jiya duk ya are?" "Ban sani ba, sai ka zo ka duba da kanka , kai dai ka ji haushin kanka kuma wallahi ka ji tsoron Allah tun yanzu ka fara mugun halin naka, to indai kai ne ai gata ga ka nan muna nan zamu ga yadda zata kaya." Murmushi ya yi yana cigaba da wasa da kitson Jiddah ya ce, "Shike nan za a kawo maku komai." "E daman kace haka man, ai Allah Ni ba zan juri wula anci ba don ta amar kayi wani auren banza can." Kashe wayarsa ya yi kawai don yasan idan ba katinta ya are ba, ba zata tsiyaya mai masifa ba, shi kam ko zaginsa za tai ba zai ji komai ba yanda yake tare da Princess insa matsayin matar aure . Duk abin da tace mai tsab Jiddah ta ji sai tai kamar bata ji ba, suka cigaba da waya da Alawiyya. Sallamar an Jalingo ce tasa ta tashi daga jikinsa su kai sallama da Alawiyya ta fita waje ta tarbe su, shi kuma ya koma aki. Sun gaggaisa suna ta zare ido sunga gidan Jiddah kamar ba Nigeria ba, gida mai kyan gaske ya ji kayan alatun rayuwa komai akwai a gidan wani abun ma basu san ko miye ba. Jiddah ta tarbesu da martaba ta kawo masu kayan abincin da Aunty ta aiko masu da shi, suna ci suna sunne kai domin baki ayansu ba wadda ta ta a taka afarta gidan auren Jiddah da Deeni. Suna gamawa ta kwashe kayan ta kai kicin ta le akin tace mai ya fito ya gaisa da mutan Jalingo suyi bankwana za su koma gida Yau. Tare suka jera suka fito yana ri e da hannunta suka gaisa suna ta yi mai Allah sa