Sashe 77
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KADUNA Alawiyya ta dube su duka tace, "Lokacin da muka rabu da ke na ruga ban zame ko'ina ba sai wani shago dana gani a rufe na shige na runtse idona tsabar tsoro yasa barci ya kwashe Ni ban sani ba, sai da safe gari ya waye sannan naga wasu mutane a gabana suna min kallon mamaki, Ni kuma na bi su da kallon tsoro domin na auka wasu ya kira min su kama Ni. Sai dai a hankali na fahimci ba wancan mutumin bane domin naji suna tambayata daga ina nake? Ko buki muka zo na ace? Ina ne gidanmu? Hakan yasa na fasa kuka na kama kiran sunanki domin sai a lokacin hankalina ta komo jikina na tuna kuma baki tare da Ni, don haka na tashi da gudu ina kuka ina kiran sunanki sai wannan mutumin ya sa sauran suka ri e Ni suka ban kalaci na i ci duk da ina jin yunwar amma na kasa samun natsuwar cinsa tunani nake kada ace mutumin ya kama ki don haka na kasa samun damar cin abincin da suka ban. Ganin hakan yasa suka ce na ci abincin su kuma za su je su nemo min ke. Sai a lokacin naci abincin ina kuka duk da hakan, bayan na gama ci ne ya tambaye ni daga ina nake ? Nace mai gada gidan marayu muke Ni da ar'uwata muka gudo neman iyayenmu saboda ance mana iyayenmu na da rai sune suka kai mu ajiya gidan marayun. Intakaice maki labari sai da muka wuni muna nemanki bamu ganki ba har lokacin tashi ya yi gun aikinsu ba ki ba labarin ki don haka sai na saka a raina kema kin yi wani wajen ban ji a jikina ba cewar wani abu ya same ki ba. Da suka rufe shagon ne wanda naji suna ambata da yaron Oga ya dubeni sosai ya ce, " Ya sunanki?" Na amsa ma shi da "Alawiyya ita kuma awata Jiddah sunanta." Daga wane gidan marayu kuka fito? Sanin cewa ban san wani gidan marayu ba yasa nace mai daga Lagos muke, amma Yau kwanan mu biyar nan garin." "Kwana biyar a ina kuke kwana to?" Na ce mai a cikin masallaci muke kwana da asuba kafin Ladan ya kira sallah mu ke ficewa daga masallacin." Girgiza kanshi ya yi ya ce "Mu je na kai ki gida, amma sai dai ki sani nima in kamar ki nake domin ba nan ne iyayena suke ba, daga almajiranta na samu uban gida mai mutunci ya maida Ni yaronsa a garejin nan to yanzu bai nan ya tafi neman wani abu kuma zai jima bai dawo ba, idan kin amince zan kai ki gidansu ki zauna nima a can nake zaune kafin ya dawo asan abin yi." Ban da mafita don haka na amince muka tafi gidan tare, tun daga waje nagane gidan mutane da dama ne a ciki ganin yadda mutane ke fitowa wasu na shiga, ko da muka shiga gidan sai zatona ya zama gaskiya, domin naga ofofi kashi daban-daban a cikin gidan, ofar wani gida muka shiga, a mamakina shima ofa uku ce a cikinsa. Muna shiga cikin gidan da sallamarsa ina biye da shi a bayansa, wata mata dattijuwa na zaune ga alama abinci take rabo ta ago kai ta kalle mu ta ci gaba da abin da take. Har asa ya du a ya gaidata sannan ya yi mata bayani na ya tsince Ni ne a shagon Oga shi yasa ya kawo Ni nan kafin Oga dawo. Dattijuwar ta watsa mai harara tace, "Ban san baka da tunani ba sai Yau, kai ban da rashin tunani me zai sa ka auko yarinya haka kawai ka kawo mana ita a gida wai ka tsintso ta? To nan gidan marayu ne da zaka kawo min ajiyar yarinya? To ba dai nan gidan ba, tun kafin duhu ya ida maza ka kama gabanka ka maida ta inda ka auko ta... Wani dattijo ne ya yi sallama ya dube ta ya girgiza kai sannan ya dube ni ya ce, "Wai ni Saude yaushe za ki san Annabi ya faku ne? Yanzu ko abin da ya faru ga Autanki bai ishe ki ishara ba? Yanzu ke ba za ki zama mutunniyar kirki ba ko Allah Ya dubi halayenki ya amsa maki addu'arki ta bayyana maki inda Autanki yake ba? Haba Saude miye don kin ri e wannan yarinyar? To idan ke ba za ki ri e ta ba Ni na amshe ta zan ri e ta, don haka ta zauna da miyau na a cikin gidan nan." Ya shige wani aki yana yi ma Saude fatan shiriya. Harara ta banka mana mu duka ta girgiza kai tace, "Ka kyauta Mansur dama don kasan da cewa ya kusa shigo wa gidan shi yasa ka kawo ta, to ta zauna gata ga gidan nan indai nice ta zauna mu gani." Fuu ta shige aki ita ma aka bar mu tsugunne Ni da Mansur da sai yanzu na ji sunansa ma. Dattijon ne ya sake fitowa ya ce, "Mansur je ka abinka, Allah Ya yi maka albarka Yasa ka gama lafiya, ka barta nan zata ci gaba da zama muga abun da hali ya yi in, ai a na kowa ne." Mansur ya dube ni sosai da alamar tausayi ya ce min, "Alawiyya ki yi ha uri don Allah ki zauna lafiya da mutanen gidan nan, ka da ki yi rashin ji ko ki raina mutane ki zama kina bin kowa yadda yake so, za ki ji da in zama a gidan kin ji ko? Sannan insha Allah zan dinga taimaka maki nima da abubuwa sosai da yardar Allah za ki gane iyayenki wata rana insha Allah." Wani aki aka ce na shiga, na shige jikina sanyi alau ina tunanin yanzu kuma wace rayuwa ce zan yi a cikin gidan nan? Ko wace rayuwa kuma Jiddah ke yi yanzu haka ita ma a inda ta samu kanta? Tabbas indai Jiddah na garin nan to zan cigaba da neman ta har na ganta, ba zan yadda mu rabu da juna da Jiddah ba, dole mu rayu waje guda gida guda saboda mu in kusan addararmu guda ce. Washegari sai ga Mansur da kayan gwanjo kusan kala biyar ya kawo min, har da takalma da hijabi, sai ga maigidan shi ma ya kawo min wasu kayan. Sai dai duk abin nan matar gidan ko kallo ban ishe ta ba, abu biyu ke ha a Ni da ita harara da tsaki sune kawai abin da take bina da su. Nan da nan labari ya kacame a cikin gidan an kawo ba uwa a sashen Inna Saude ba a san inda danginta suke ba, sai ga gidan na cika da mutane sun zo ganin ba uwa. Daga nan sai gulma ta fara tashi wasu na cewa ai Mansur arya yake iyarsa ce ta yawon ta zubar kawai ya samo ya kawo ta nan ya yi arya, wasu kuwa cewa su ke Inna Sauden aka raina da aka bata ri on shegiya. Nan da nan na shiga matsananciyar rayuwa a gidan, yaro da babba kowa ya raina Ni, ban da ikon ta a abu sai a ce na aje shi tun da na iyayena bane ba. Inna Saude tafi kowa takuramin tafi kowa nuna min tsana tafi kowa nuna min tsangwama. Babu yadda magidan bai ba amma ina abin ya fi arfinsa, dole tasa nake zuwa Gareji ina wuni gun Yaya Mansur saboda idan ba can ba babu inda nake samun sau in rayuwa. Dama kin san na ware da iya aiki tun horon Iyami don haka aikin abincin gidan sam bai damu ba, nakan gama komai kafin ta ankara na gama duk wani aikin da nasan nawa ne a cikin gidan. Sai kuma ta tsiro da cewar sai na dinga bin sauran gidajen cikin gidan ina masu shara da wanke-wanke ina ebo masu ruwa kullum tunda abincin da nake ci ai daga hannun an'uwansu yake fitowa Hakan yasa aiki ya aru sosai a guna, kaf gidajen da ke cikin rukunin gidan nan babu mai tausaya min sai Inna Fattu da anta guda aya Faisal sune kawai ke matu ar nuna min tausayi suke matu ar taimaka min ta hanyar sakani karatu duk da sai da akai tashin hankali gun kai Ni makarantar boko da islamiyya amma haka suka daure na cigaba da zuwa. Sai kuma Inna Saude ta ce ita ba zata amince ba, talla zata dinga ora min ta gya a da goro tunda ba iyayen da za su sai min kayan aure gare Ni ba idan na tashi aure ko da yake waye ma zai auri shegiyar da ba a san ko da mutum guda ba a cikin iyayenta ba? Na kan yi kuka na gode wa Allah duk lokacin da Inna Saude ko wasu suka kirani da suna shegiya. A haka dai na yi shekaru biyar a gidansu Inna Saude cikin mayuwacin halin gaske, ban da gata ban da mai min gata sai su Faisal da mahaifiyarsa suma sai da Inna Saude ta shiga ta fita ta raba mu , amma ta kasa raba Ni da Faisal duk da cewar Faisal jikanta ne amma ta kasa raba Ni da shi, ko da yaushe cikin kulawa da Ni yake. Ban kuka sai idan bai nan, da ya dawo zai shigo shashenmu tunda Ni an hanani zuwa sashensu, haka Inna Saude zata dinga mai fa a amma ya yi kunnen uwar shegu da ita ya cigaba da koya min karatu ko ya tambaye ni abin da nake so. A hakan kullum dai na je nemanki, ko da yaushe sai na ba Faisal labarinki babu wanda bai san labarin Jiddah ba a wa anda nake shiri da su. A gefe guda kuma na dage da zuwa makaranta domin ban manta da al awarinmu ba na zama manyan Lauyoyi ba don kawai mu dinga hukunta iyayen dake haihuwar yara suna watsi da su ba, da mazan da ke auren mata suna wula anta su har su saka su tsallake yaransu kan dole su bar gidan su kuma ba iya ri e yaran za su yi ba. Hakan yasa ko da yaushe nake gaya ma su Yaya Mansur Ni fa Lauya zan karanta, ina son na